🐏🐏🐏
*SANADIN*
*RAGON LAYYA*
🐏🐏🐏
🐏🐏
🐏_By_
*Ameera Adam*
*AmeeraAdam60*
@: _Wattpad_*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._*_SADAUKARWA GA DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*
_بسم الله الرحمن الرحيم_
31-35
Hanne ce ta tsaidashi cikin lallashi tace, " haba d'a na daga magana kuma sai ka tafi, to ba wani abu mun amince amma fa bamu fito da kudin ba, sai dai ko kazo ka karba " bai juya ba ya bata amsa da, " karki damu zan turo k'ugiya yazo ya karba gidanki ne na karshen layi ko akwai wata yar hannu agidan " hanne shiru tayi cikin tsawa gogarma yace, " ba tambayarki nake ba, nace gidan akwai wata yar hannu aciki ko " da sauri hanne ta amsa da, "eh nan ne "
" Kuna komawa ku aje kudin zan turo akarba, ku sa aranku kamar ansato muku rago angama " cewar gogarma.
Su hanne tafiya sukayi hajara tana yan sak'e-sak'e azuciyarta, hanne ce ta katse hajara tace, " hajara ni sai yanxu nake ganin wawtarmu wallahi " da mamaki hajara tace " wawtar me mukayi " yooo da mukace rago daya zai sato mana mukasani ko ya sato mana dan karami wanda befi dubu goma sha biyu ba " cewar hanne.
" ehh, kuma fa zancen ki na hanya hanne, yanxu meye abunyi " inji hajara.
Hanne tace, " ko dai cewa zamuyi ya sato biyu " to hanne ina naga kudin da zan bashi nace miki dubu biyar kadai ta rage mun, ke cikon kudin ma fa saidai ki aramun " cewar hajara.
" Karkiji komai na ara miki dan dai na lokaci bari muje Allah sa furaira ta dawo sai intambayeta ko zan samu yar dubu goma ko sama da haka rance " inji hanne.
Suna tafe suna hira har suka karasa gidan hajara, hajara kudi ta dauko dubu biyar ta irgasu suka karasa gidan hanne shigarsu keda wuya sai ga k'ugiya ya danna kai ko sallama babu.
Daki hanne ta shiga ta dauko cikon kudin, saida suka irga kudin dubu goma cif sannan suka mik'a masa sukace ya irga, ba musu ya irga sannan hanne ta kora masa bayani akan sun sake shawara suna san asato musu raguna biyu, hanne har kara jadadda masa take akan su samo musu kato me tsoka, kamar wacce ta bada kudinta. 🤣
Cikin dakusashshiyar murya ya bata amsa, " karku damu kunsan me gida bashi da wasa, kudai ku tanadi tirke da Abinci "
Bayan fitar k'ugiya hajara ta cewa hanne, " to bari na karasa gida kinsan Allah yau ba abinda nayi, dama yaran nan mlm ya tafi dasu tun safe ke shimfidar dana tashi ma ban gyara ta ba, saboda tashin hankalin da rashin nutsuwa "
" banda abinki hajara komai aysai da kwanciyar hankali, yanxu kije kiyi aikin da zakiyi ki dawo kafin nan kinga sun dawo sai su sameki anan koba haka ba " cewar hanne.
Sallama sukayi hajara ta tafi gida zuciyarta fess cikin jin dadi, hanne ce tabi bayanta da harara cikin dariyar keta da mugunta tace, " waiwaiwai yaro man kaza hajara kenan amma ke kam anyi wawuya wawuyar ma ta karshe, hajara kin zamemun jari ko ince kadara, ay tunda mlm kabiru yaki amincewa ya aure ni na dinga doraki aturken keken b'era, kin dauka zan zuba muku ido yana nannan dake yana baki kulawa hmmm yanxu kika fara gani tunda ke baki da hankali " hanne ta karasa maganar tana kara kecewa da dariyar mugunta.
Hajara na fita kai tsaye gida ta wuce, wannan karan yanayinta ba yabo ba fallasa sai dai har zuwa lokacin bata gama sakin jikinta ba, cikin zuciyarta take fargabar mlm kabiru idan ya tambaye wannan ragon kuma tace masa me, fargaba ce ta cika zuciyarta tana ta fatan kamalla abinda zatayi ta koma gidan hanne kafin mlm kabiru ya dawo inyaso ko wata karyar ta shirya masa.

YOU ARE READING
SANADIN RAGON LAYYA CMPLT
Short StoryBil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wa...