Ending

266 19 3
                                    

🐏🐏🐏
       *SANADIN*
               *RAGON  LAYYA*
           🐏🐏🐏
              🐏🐏
                    🐏

                  _By_
         *Ameera Adam*
    *AmeeraAdam60*
      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

               46-50

   🔚🔚🔚

Wani police ne ya karaso bakin cell din da suke ya buga Musu uwar tsawa cikin masifa ya Fara magana, " ku wad'anna irin mahaukata ne da girmanku kuke irin wannan shirmen jibeku yanxu idan yaranku sukaga Kuna irin Haka kallan me zasuyi muku Amma wlh kun bani mamaki, ko Kuma ay ba abin mamaki bane idan akayi duba da irin laifin da kuka aykata shashan banza da wofi, dubesu kamar masu hankali Amma Kan ashe na tinkiyoyi ne dasu"
    Hanne ce ta Fara sauke ajiyar zuciya da kyar tace, " yallab'ai ka taimaka ka cireni daga cell d'in Nan wallahi zata iya lahantani ji irin dukan da tamun yanxu haka bana gani sosai jiri ne yake d'ibana"
     " Anki acireki din ay kawarki ce laifinku d'aya Kuma tare aka kawoku, idan kuka cika mun kunnene zan d'auki mataki akanku" cewar police din.
    Gaba daya tsit sukayi kowa da abinda yake sak'awa zuciyarsa, hajara abun duniya ne duk yabi ya addabeta tsoron had'uwarsu da mlm takeyi.

    Masu raguna basu suka iso police station din ba sai kusan karfe goma Sha biyu na Rana, su hanne haka suka dinga rokonsu suna magiya, zuwan masu raguna keda wuya sai ga mlm kabiru ya shigo, gaisawa sukayi ya gabatar Musu da kansa sannan ya nemi asanta akashe maganar tun ba'aje ko inaba, da kyar da sid'in goshi mlm kabiru yashawo Kansu suka amince, kudin asarar da akayi Musu suka buk'ata atake mlm kabiru ya biya Wanda akaci tarar hajara, alokacin kuma aka fito da ita hanne sai rok'onsa take ko ta kanta baibi ba, su hajara sunje fita suka had'u da furaira taxo Kan maganar mahaifiyarta, tambayar hajara furaira takeyi Amma ko kallan arziki hajara batayi Mata ba tunaninta Daya yanda zasu kwashe da mlm kabiru.
     Suna fita mlm kabiru ya kalli hajara cikin tsuke fuska yace, " bayan wannan wane Abu Kika aikata Wanda bansani ba?" Sunne Kai k'asa hajara tayi tace, " kudin lubabatu Mai adashi ne ya rage" tambayar ta yayi nawa ne ta Gaya Masa zaro kudi yayi ya irgasu ya ware na lubabatu yasashi a aljihu daban, ita dai hajara da ido take bin mlm kabiru har suka karasa titi, me napep ya Tara Kai tsaye Tasha yace ya kaisu, suna xuwa ya wuce wajen lodin motocin karaye umarni ya bawa hajara ta shiga, jikinta ne yayi sanyi har ta budi baki zatayi magana mlm kabiru ya dakatar da ita.

Mlm Kabiru zama yayi shida ita bame cewa wani uffan hajara nasan yin magana tana tsoron jin ta bakin mlm kabiru, bayan sunje karaye Kai tsaye gidan kakannin hajara suka wuce duk kakannin nata sun rasu saidai irin y'an uwan Nan na dangin,  sai wani tsohon ne kawai ya rage me suna mlm Alto shima wani Dan uwan kakanta ne da suke abokan wasa, mutanen kauyen na ganinsu suka Fara murna ana ga hajara ta zo, sai dai ta bisu da yak'e Wanda yafi kuka ciwo, gurin mlm Alto sukaje suka gaisheshi mlm Alto murna yake inakasaka inaka aje, har ya bada kudi asiyo Musu abinci  mlm kabiru ya dakatar dashi, sannan ya Fara yi masa bayani, " baba Ina San kamun alkawarin duk hukuncin da zan yanke bazaka tambayeni dalili ba " rassss gaban hajara ya Fadi jikinta har karkarwa yakeyi ta gama saddak'ar wa zamanta da mlm kabiru ya k'are, mlm Alto yace, " kabiru inajinka nasan halinka Sarai bazakayi wani Abu ba tare da wata hujja ba me yake tafe dakai Fad'i kanka tsaye"
     " Yauwa, dama inasan hajara ta zauna agarin Nan na D'an wani lokaci idan lokacin yayi ni zan dawo da kaina na d'auketa" sai alokacin hajara ta D'an ji dama-dama, mlm Alto na Shirin tmbyr mlm kabiru sai ya tuno da alkwarinsu Amma ba makawa yasan ruwa baya tsami banza, D'an kudi mlm kabiru ya deb'o ya bawa mlm Alto sannan yayi Mai sallama ya fito, hajara ce biye dashi idanunta sun ciko tana rok'on sa Amma kamar baimasan tanayi ba, ganin mutane sun Fara kallansu yasa hajara komawa cikin gida tayi turus tama rasa makamar dafawa sai hawaye da yake bin fuskarta.
    Mlm kabiru badan yaso ba ya yankewa hajara wannan hukuncin saidai yasan wannan shine yafi dacewa da ita, acewarsa bazai iya rabuwa da hajara ba, ko tayi hankali ta gane muhimmancin sa yana hanya ta kirashi yafi a irga kamar bazai d'auka ba yasa hannu ta d'auka yace, "lafiya Kika isheni da Kira?" Dan Allah mlm kayi hkr........ Katseta yayi da, " dakata hajara tuni nagama magana, Ina komawa Kano zan nemi auren kawarki hanne, Kuma idan Kika sake Kika baro garin Nan ba tare da ninazo na taho dake ba wallahi kinji na rantse abakin auranki" Yana gama maganar k'it ya kashe wayar.
     Hajara batasan lokacin da ta rushe da matsanancin kuka ba,matan gidan ne suka rugo da gudu suna tambayar ta me yake faruwa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 10, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SANADIN RAGON LAYYA CMPLTWhere stories live. Discover now