chapter eleven

16 10 1
                                    

Kwana biyu kenan da zuwansu ray gidan. Lili ce tashigo dakin tana fadin.
Khay zain yamin six missed calls.
Meyasa baki daga ba?.
In daga?. Sai damuna take in aika Masa da pics dina. And finally yace Yana sona. Nace masa Ina da wani yace I'm lying. Wai yayi tracking number na ya gano Nima Ina Zaria city Yar Abhi. Wai zaizo unexpected.
Kuma wai daddynsa yasan Abhi. Khay nashiga uku.

Keya saka acikin Rai ya anbataaah...
Yayi halacci bazaya barki ba ba ba...
Status dinki dayagani yasa yake kwadayinki...
Baiji kunya dayace Yana sonki....
Ke yake jira ki dauki hoto ki aika Masa...
Baya moruwa ako'ina inbabu ke adamana....
Ya dauke hoto Yaturo maki ki dinga kallonsa....
So kauna shi ya ambata....
Yyi halacci bazaya barkiba ba ba...

Khay tana wakan tana tsalle tana hadawa da shoki.
wAllahi khay sai na.....Lili tace tareda binta sukayi falo da gudu.

Cak khay taja full stop ta tsaya. Lili na zuwa tana fadin. Thank God kintsaya da kanki you know....
Bata idasa ba itama taja birki ta tsaya.
Kallon juna sukayi sannan suka maida kallonsu ga Abdoul dake falon shi da milli suna masu confuse look.
Dasauri suka fara komawa dakinsu da gudu.

😂😂see dis gals fa...

                 ********************

Suna zaune a dinning suna cin abinci. Abhi ma nazaune dashi ake dinner.
Aje cokalin hannunta tayi ta dubi abhi sannan tace.
Abhi uhm Daman Ina son namaku magana akan makaranta. Ina son nayi degree course.
Oh ba kinyi diploma ba da HND?.
Eh Abhi Amman Ina son nayi degree.
Gyada Kai Abhi yayi sannan yace that's good Amman kinsan you're married now?.
Zaiyi kyau idan kin Kara tambayar mijinki don haqqinsane. Da amincewarsa, sai a fara shirya neman maki admission.
Tunanin tane yayi nisa Anya bros zai yarda kuwa?.

Tohm Daman ba'a Kai masa dinner ba.ki tashi kikai Masa saiki tambayesa daganan. Good luck bestie. Khay tace tare da kanne mata ido daya.

Hararan khay tayi sannan ta Kai mata duka a kafada.
Ban gama cin abinci ba. Ban koshi ba khay kaimasa zan tambayesa after dinner.
SubhanAllah irin zaman da kukeyi kenan?.
Saikin koshi sannan Zaki bawa mijin ki abinci?. No no no this is never okay.
Kallon Abhi Lili tayi sannan tace nooo Abhi ba haka bane.
Toh yane?. Amun bayani?.
Anya Zaki school kuwa?. Gaskiya tattarawa zakuyi kubarmin gida ku tafi naku gida.
Shagwabe fuska tayi tace Abhi plsss no. Zamu zauna anan zaman cikin family yafi. Allah ma zai bamu ladan haka. Tafadi hakan tana daukan tray din abincin milli tanufa hanyar dakinsa tareda fadin ni naje kaiwa mijina abinci. Cikin dagin murya.
Kinjimin mara kunya Kai. Ummy tace sannan sukayi dariya.

Sallama tayi Amma tsit babu amsa.  Kara yin sallama tayi still bai amsa ba.sai tashiga knocking da karfi.

Bude kofar yayi da wayarsa manne da kunnensa daji waya yake fuska ahade ya harareta up to down sannan ya koma ciki ya haye bed dinsa.
Shiga dakin tayi sannan ta ajiye tray din akasa sannan ta samu wuri ta zauna ta kafe shi da ido.

Dagaji da mace take waya. Yadda yake murmushi Yana fara'a murya can kasa yake magana.

Mtww jibe shi anjima sai yace shi baya harkan mata.yanzu dawa yake waya?.
Sai murmushi yakeyi idan nice sai ya koma monster. Mtww mugu.
Tace aranta.

Yakai minti biyar Yana waya itakam tana zaune tana jin abubuwan dayake Fadi. Sai dai kalma daya bataje da kalaman soyayya ba.
Hakan yasa tadan ji sanyi.

🤔But why???.

Miqewa tayi zata bar falon taji yace malama bance ki tafi ba.
Dan yamutsa fuska tayi sannan ta dawo ta zauna.
Kasa tayi dakai tana kallon nails din aranta tana yabansu da kyan data ga sun Kara mata alokacin.

Shiko shuru yayi Yana kallonta Yana nazarinta sai kuma ya watsar.

Wa kika ajiye dazai min serving?. Yace a normal voice dinsa mai sanyi Amman fuskan Nan adaure.

Tashi tayi tafara zuba Masa a plate.
Tana cikin zubawa be taji yace.
Me ya faru?. Do you need anything?.
Dago dakanta tayi tace urh.
Kafeta yayi da idanu hakan yasa ta sadda Kai kasa tana juya serving spoon.

Dan murmushi yayi. See this gal wai sometime she's funny,wani lokacin kuma mara kunya, most times baby...
And all. She seems to amaze me with new things. Yace aransa.

Nasan you want to say something say it.
Dagowa tayi ta kallai as in tana mamaki. Yanzu kam kamar bashi yayi maganar ba.
Maida hankalinsa ga abincinsa yayi yanaci yayin da take kallonsa ba kyafta ido. Sai tayi murmushi ta kauda Kai.
Duk abunda take yana kallonta da gefen ido.shima murmushin yayi.

Fada Mana karki batamin lokaci Ina da program dazan kalla.
Uhm Daman bros Ina son........
Bata karasa ba taga ya kafeta da idanu ya daga gira daya Yana sauraranta.

Shagwabe fuska tayi ta matsa kusa dashi sannan tace.
Bros please please please idan na tambayeka you won't say no?.
Yamutsa fuska yayi alaman bai gane ba.
Please bros milhan zaka yarda?.
Kallonta tayi sosai sannan ya maida dubansa ga hannunsa data riqe.
Hannunta so soft and warm.sai yaji Kamar ya kamo hannayenta ya binne su anasa.
Itama din dai bata lura da abunda tayi ba.
Lumshe idanunsa yayi.
Yayin data kafesa da manyan idanunta Yana jin nata faman fadin please please please da baby voice dinta.

Menene kike so?tell me.
Calm voice dinshi ya fada.
Abun dadi ya mata don haryanzu mamakinsa take.
Sometimes he's cool.wani lokacin kuma strict.
Idan Yana cool yafi birgeta sai ya Kara mata kyau har Yana birgeta so hakama yanzu birgeta yake.
Promise zaka yadda.
Dan murmushi yayi yace taya zan yadda bansan me zakice ba. Kawai inje in amince ki kashe ni. Yayi maganar a tsigar wasa.
Common bros ka amince Mana.
See you fa. Idan kin shirya ki fadamin.idan kuma you're not ready?....bye bye.

Okay bros please Ina son...na...fara...zuwa... school. Don Allah kasama mun admission pleasssse.

Ware idanunsa yayi Yana kare mata kallo Kamar ya sace ta, Kamar ya hadiyeta. At this point so yake ya rungume ta.
Idanunta arintse tana jiran amsar dazai Bata.
Dayaga haka?,sai ya harde hannu a kirji ya murmusa sannan yace.
No bazaki ba. Ya daure fuska yacigaba da cin abincin sa.
Huh br...bro...bros?. Ta iya cewa.
Yeah kinjini nace ban yadda ba. Tashi ki barmin dakina now.
Wani irin faduwar gaba taji.
Yadda take ji Kamar ta fashe da ihu.
Duk jikin yayi weak tama kasa motsi.

Baki ji bane?...leave my room. School kuma bazaki ba.

@@@@

As e dey hot....
Toh ya kenan???
Lili bye bye to ABU ZARIA....

Me kuke gani???
Meyasa milli ke switching side ne haka???..

Mu hadu a next page....👇😜😜

Queen Nimnal thanks fa...
Lav yah alot babe..

Pls keep voting, comments,and share .

Lav yah ol Lili and milli's fan..
Or khay and Lolo's fan...
😜😜😜😜

LILI TAWACEHWhere stories live. Discover now