MABUƊI
“Allahzi wahidun jama’a! Na Annabi Allahzi wahidun!!!” Muryar wata tsohowa mabaraciya kenan data karaɗe illahirin wajen cikin bararta ta neman taimakon na-Annabi ga masu shige da fice a kan hanyar.
A zaune suke gefen titi ita da ƴar jagorarta, wata matshiyar yarinya da ba zata wuce shekaru sha uku ba. Wajen ya kasance wajen zamansu kullum tun daga safe har zuwa faɗuwar rana, sai dai in rana ta cimmusu su tashi su bi inuwa.
Dai dai lokacin lafiyayyiya kuma rantsattsiyar motar ta faka can gaba dasu kaɗan, jim kaɗan akayi ƙasa da baƙin gilashin motar mai kama da duhun magariba, wanda bazai bari na waje ya hango na ciki ba.
Ya ziro da kanshi waje, kyakkyawar fuskarsa ma’abociyar kwarjini ta bayyana, fuska mai cike da kyau da zati, a kallo ɗaya mutum bazai iya yanke masa hukuncin gaggawa na aiyana shekarunsa ba, sai dai ayi hasashen cewa zai iya hawa shekaru arba’in da biyu zuwa da biyar haka, dumin kuwa har farfatsin furfura gareshi jifa-jifa a cikin gemunsa, sai dai da gani furfurar hutu da jin daɗi ce.
“Ke ƴan mata zo ki karɓi sadaka.” Yarinyar ta miƙe da sauri tare da duban tsohuwar tace, “Kaka! Ga wannan mutumin da yake bamu sadaka kullum yazo, bari naje na karɓo mana yana kirana.” Bata jira cewar Kakar tata ba ta miƙe da sauri ta nufi gurin mutumin duk da cewa Kakar tata ta magantu da cewa, “Yi maza ki karɓo mana ƴar nan, dan yau kasuwar tamu da sauƙi.”
Yarinyar ta isa gaban motar mutumin ta rusuna ta gaida shi kamar yadda ta saba. Ya tsura mata idanu cikin ƙare mata kallon tsawon wasu ƴan daƙiƙu, har sai da yarinyar ta ɗago daga sunkuyon da tayi jin shiru bai miƙo mata kuɗin ba kamar yadda ya saba. Yayi firgigit kamar matsorancin da aka watsawa ruwan sanyi lokacin hunturu, sai ya shiga gyara zaman hularshi cikin wayencewa. Ya karkace ya zaro kuɗi daga aljihunsa ba tare da ƙirgawa ba ya miƙo mata. Ga dukkan alamu kuɗin yau sunfi na kullum yawa, wata ƙila hakan ne ya zama dalilin da yasa yarinyar ta kasa miƙa hannu ta karɓi kuɗin har sai da Alhajin ya ɗan kaurara murya yace, “Karɓi mana a’ah! Me kike kallo ne…”
A ɗarare ta miƙa hannu ta karɓi kuɗin, tabbas kuɗin yau sunfi na kullum, tudun kuɗin da taji a hannunta ne ya tabbatar mata da haka.
“An gode, Allah ya biya Allah ya jiƙan mahaifa.” Cikin sauri ya amsa da ameen. Har ta juya zata koma yayi saurin katsar hanzarinta da cewa.
“Ni baki taɓa faɗa min sunanki ba yarinya, ai ya kamata ace na san sunanki ko, yadda in nazo kawai sunanki zan kira.”
A taƙaice yarinyar tace “FATSIN”
“Fatsin?” ya maimata cikin sigar tambaya fuskarsa na nuna mamakin jin sunan haka kamar ba na hausawa ba. “Wane irin suna ne haka kuma wai Fatsin?”
“Ni dai haka ake kira na, ko kace FATSIME”
“Oh! Naso na fahimci sunan, kamar FATIMA ko? Sunan yayi kama da Fatima, ina ji Fatiman ne aka ɓata miki suna ake ce min wani Fatsin.”
“Ni dai haka Kakata take ce min, kuma na san kakata bazata ɓata min suna ba.” Ta faɗi haka tana ƙoƙarin tafiya.
“To ni baki tambayi nawa sunan ba, ko ba kya so ki sani?” Ya sake katseta a karo na biyu. Wannan karon waigowa kawai tayi tana jiran taji abinda zai ce. Da ya fuskanci ba zatayi magana ba sai yace. “Sunana SA’EED”
“Ko dai ace Alhaji SA’EED?” Ta faɗi hakan cikin nuna zallar ƙuruciyarta. Yanayin da tayi maganar ya bashi dariya, saboda haka ya murmusa yace, “In kin kirani hakan ma ba laifi.”
“To shikenan Alhaji Sa’eed mun gode… bari in koma wajen Kaka kar taga na daɗe.”
Yana murmushi yace, “Shikenan, Fatima, ki gaishe min da kakar taki, kuma ki sanar mata wata rana zan zo na gaisheta.”
Ta juya tayi gaba, yayinda shi kuma yabi bayanta da kallo, yana aiyana wani abu cikin ransa, fuskarsa ta ɗan faɗaɗa da murmushi, wanda hakan ke nuna kamar ya hau hanyar cikar burinsa. Bai bar gurin ba har ta koma gun kakar ta zauna, ta juyo suka haɗa ido, ya ɗaga mata hannu alamun bye, sannan yaja motar ya bar gurin.
Kakar ta tambayeta, “Fatsin, ya akayi yau kika daɗe gurin karɓo sadakar, ko wani gurin kika biya na sanki da shegen kalle-kalle kamar wacce ta warke daga cutar makanta.”
“Hmmm! To kaka sarkin ɗorawa mutum laifi, babu inda naje, Alhaji Sa’eed ne ya tsaidani.” Cikin sauri kaka ta tareta, “Wanen shi haka?” “Mai bamu sadaka kullum ɗin nan, mai zuwa a mota.”
“Oh toh! Me yace miki ne?” “Sunana kawai ya tambaya, nace mishi fatsin, wai shine yace ba haka sunan yake ba, wai ɓata min suna kuke yi, wai sunana FATIMA…”
“Eh fa, haka sunanki yake, sunan ɗiyar ma’aiki (S.A.W), wannan tasa muke sakaye sunan saboda halin mutanenmu, sai a ambaci sunan a luƙa ashiriya, an manta ainahin darajar sunan, wannan tasa muke ce miki Fatsin.” Jawabin Kaka.
**
Alhaji Sa’eed ya dubi likitan fuskarshi cike da damuwa, kamar wanda aka aiyana masa faruwar wani abu mara daɗi. “Doctor, yarinyar ƙarama ce sosai, bana tunanin zata haura twelve to thirteen, ina tsoron samun matsala.”
Murmushi likitan yayi mai cike da nuna ƙarfafawa da ƙwarin gwiwa, “Ai alhaji wannan bazai zama wata matsala da zata zama shamaki ga wannan aikin ba, dan tana shekara goma sha biyu ko sha uku ba yana nufin bata girma ba, kasan akwai banbanci tsakanin girman mace da namiji, wata macen tun tana da shekara tara girma yake fara zuwar mata, wata kuma ta haura haka…” Ya ɗan numfasa, sannan ya cigaba yana mai gyara zaman farin gilashin dake sagale a saman siririn hancinsa mai kama da biro, “Matuƙar alamun girma sun fara bayyana a jikinta, to hakan na nufi zata iya fara al’ada ko ma ta fara, kaga kuwa in dai har zata iya fara al’ada to tabbas zamu samu abinda muke so, kuma aiki zai fi zama safe musamman da naji kace almajira ce, bara suke da Kakarta makauniya.”
Alhaji yaja dogon numfashi ya sauke, har yanzu fuskarsa bata sassautu daga yanayin damuwar data ke ciki ba, “Naga alamun girma a tattare da ita likita, sai dai ba wani can ba gaskiya, saboda daga ganin yarinyar irin masu tsattsaman jikin nan ce, babu alamun shekaru a fuskarta.”
“Ai babu damuwa Alhaji, ka saka a ranka buƙatarka ta kusa biya da izinin Allah.” Cewar likitan a lokacin da ya miƙe, bai jira cewar Alhajin ba ya ɗora da cewa, “Yanzu dai aiki ya rage gare ka Alhaji, sai ka gaggauta kawo ta ayi abinda za’ayi cikin lokaci.”
“Ok, shikenan Doctor, zanyi ƙoƙarin hakan, Allah yasa a dace”
***********
Al’amura cukurkuɗaɗɗu ne suka biyo bayan hakan, Alhaji Sa’eed ya samu biyan buƙatarsa a wani yanayi na rufewar ido da son biyan buƙata kota wani hali, ba tare da dogon tsinkaye ko lissafa ɗaya a tara da biyu da tunanin cewa lallai uku zata samu ba, ya fuskanci tarnaƙi tare da tarin ƙalubalai kafin kaiwa gaci, ƙarshe dai yayi nasara fatsarsa ta maƙalo masa gandararen kifi, sai dai kash! Kifin ba jela!!!
Cikin abubuwan da suka faru harda mutuwar Kaka makauniya, wato kakar jarumar labarin tamu Fatsin, ko yaya labarinta zai kasance?
Ku biyo ni.
YOU ARE READING
FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)
General FictionLabari a kan wani mai kuɗi (Alh. Sa'eed) wanda Allah ya wadata shi da komai na jin dadin rayuwa, sai dai abu ɗaya ne ya gagareshi wanda a kan fafutukar neman abun idanunsa suka rufe ya aikata wani al'amari wanda shi ya zama silar ginuwar labarin. A...