BABI NA BIYAR

31 0 0
                                    


                         BABI NA BIYAR
Dare ya tsala sosai, za'a iya kiran lokacin ƙarfe biyu da rabi zuwa uku. A dai dai wannan lokacin duniyar tayi tsit tamkar babu wata halitta mai fidda sauti a cikinta, dukkan wani ɗan Adam a wannan lokacin ya jefa haƙarƙarinsa makwanci dan huce gajiyar kujiba-kujibar wunin ranar,  ƙalilan ne waɗanda larura ko wani ƙaƙƙarfan dalili  kan iya hana musu yin bacci a lokacin. Haj. Ikilima ce ta fito daga ɗakinta a wani firgitaccen yanayi, sanye take da doguwar baƙar riga kanta babu ɗan kwali gashin kanta duk a barbaje tamkar na sabuwar kamun mahaukaciya. Ƙaton filo ne hannunta ta nufi ɗakin Faruƙ cikin tafiyar sanɗa tanayi tana waiwaye tamkar wacce ke zargin wani na binta a baya. A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, ƙofar ta buɗe a hankali ba tare da tayi ƙara ba, tayi saɗaf-saɗaf ta shige ɗakin. Yana kwance akan lallausan gadonsa rabin jikinsa a lulluɓe da tattausan bargo, ta lalubi makunnar fitilar ɗakin ta kashe dim light ɗin ɗakin,  duhu ya mamaye ɗakin yadda mutum ko tafin hannunsa bazai iya gani ba. Ta lallaɓa a hankali ta isa gaban gadon, ta ɗaga filon dake hannunta ta saita inda take tunanin kansa ne ta jefa filon ta bishi ta danne iya ƙarfinta. mutsu-mutsu da fizge-fizge ya dinga yi, tun yanayi da ƙarfinsa har ƙarfin nashi ya fara ƙarewa jikinsa ya fara daina motsi har zuwa lokacin da komai nasa ya tsaya cak! Dai dai  lokacin aka jefota ɗakin, fitilar ɗakin kuma ta  kunna kanta da kanta haske ya gauraye ɗakin, karaf idanunta suka hasko mata abinda ke faruwa, ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara tare da yanke jiki ta  faɗi tana "Wayyo Faruƙ ɗina…"
Dai dai nan ta farka a gigice cikin ƙwalla ƙarar a zahiri tana cigaba da kiran "wayyo Faruƙ ɗina…" Ta dafe ƙirjinta dake tsananin bugu fat fat tamkar ƙirjin zai fashe zuciyarta dake hanƙoro ta fito, gaba ɗaya ta gama jiƙewa da gumi. Da  ƙyar ta samu nutsuwar da ta fara ambaton innalillahi… lokacin da nutsuwa tazo mata sai taji babu abinda take so  a lokacin face ta kira Alhajin taji lafiyar Faruƙ ɗin. ba tare da tunanin komai ba ta jawo wayarta ta kunna, bayan wayar ta daidaita ta lalubi number Alhajin a karon farko da ta taɓa gwafa kiranshi tunda ta saka number a wayarta.
Taci sa'a kuwa wayar tashi a kunne take sai dai tana ta  ringing ba'a ɗauka ba har kiran ya katse, ta sake kira a karo na biyu cikin matuƙar ƙaguwar son ya ɗaga kiran dan a yadda take ji  a ranta tamkar a wannan lokacin Haj ikilima ta tafi aiwatar da abinda ta gani a mafarki zuwa a zahiri.
A wannan karon an ɗaga wayar, Alhajin ne da kansa ya ɗaga da muryarsa ta wanda yayi nisa a bacci yayi sallama, a gaggauce ta amsa sallamar tare da ɗorawa da abinda ke ranta.
"Alhaji ina Faruƙ? Yana nan lafiya kuwa? Dan Allah ka tashi kaje tabbatar da lafiyarsa"
A kishingiɗe yake amsa wayar cikin jin matsanancin bacci amma jin furucinta yasa ya  girgije jin baccin ya watsar ya tashi ya zauna kan gadon.
"Meke faruwa ne?"
"Nayi mummunan mafarki ne a game da Faruƙ, dan Allah Alhaji kaje ka duba lafiyarshi dan Allah."
"Shikenan ki kwantar da hankalinki zanje in dubashi yanzu, zan kiraki."
"Yauwa Alhaji ka hanzarta dan Allah." Duk ta ruɗe.
Ya kashe wayarsa ya ajiye a bed side ya yunƙura ya  sauka daga kan gadon, Haj. Ikilima dake kwanci tana sauraren komai tayi zaraf ta miƙe. "Ina zaka je Alhaji da wannan tsohon daren, wacece ta kiraka?" Ta jefa masa tagwayen tambayoyi.
"Zahra ce" ya amsa tambayarta ta ƙarshe a gajarce yana ƙoƙarin sanya doguwar rigar baccinsa ya fice daga ɗakin. Mamaki ya kusa kasheta a zaune, sunan ZAHRA kawai take ta maimaitawa a fili cikin kiɗima da razana, lamarin yarinyar har ya kai haka? Kira da tsakiyar dare? Duk lokutan da suke kasancewa tare da rana basu ishe ta ba sai ta bi dare ta kira ta hana musu bacci? Anya bata sakarwa yarinyar nan da yawa ba kuwa? Kar fa maganar Haj. Azima ta tabbata fa! Lallai ya zama dole ta ɗauki matakin gaggawa akan yarinyar nan tun kafin wankin hula  ya kaita dare. Miƙewa tayi tabi bayan Alhajin dan taga inda zashi, ga mamakinta ɗakin Faruƙ taga ya  nufa. Kusan tare suka isa  ɗakin saboda tafiyar sassarfa da tayi har ta cimmasa. Ya kunna fitilar ɗakin haske ya gauraye ko  ina, Faruƙ na tsakiyar faffaɗan gadonshi a takure tamkar wanda aka saka tsakiyar kogi lokacin hunturu. A jiƙe yake sharkaf da gumi jikinsa sai faman kakkarwa yake, a guje Alhajin ya ƙarasa garesa ya yaye masa bargon dake kansa ya janyoshi jikinsa.
"My son lafiyarka kuwa meke faruwa?"
"Mafarki nayi Daddy, mafarki nayi mai ban tsoro an biyo ni za'a kasheni"
"Ya salam! Kayi addu'a kuwa kafin ka kwanta Faruƙ?"
"Nayi Daddy, ina yin addu'a kullum in zan kwanta."
"To ka cigaba da yi, babu abinda zai sameka da izinin Allah"
Ya sa hannunsa yana shafa bayansa "Ka kwantar da hankalinka kaji, mafarki ba  gaskiya bane." Tsaki Haj. Ikilima tayi ƙasa ƙasa ta juya tayi ficewarta.
Faruƙ yayi luf akan mahaifin nasa har bacci ya sake yin awon gaba dashi, ya zamar dashi ya kwantar ya saita masa A.C ɗakin sannan ya miƙe ya fuskanci ko wacce kusurwa ta ɗakin ya tofe ta  da qulhuwallahu da falaƙi da nasi ƙafa uku uku. Ya kashe fitilar ɗakin ya juya ya fita ya ja masa ƙofar ɗakin.
A falo ya iske Haj. Ikilima ta kifa kanta cikin hannayenta, ita kaɗai ta san abinda ke damunta. "ni na wuce ɗaki, idan kin gama tunanin kya zo  ki kwanta" yayi wucewarsa ɗakinsa, tasowa tayi ta biyo shi ta same shi da wayarsa a hannunsa yana jinjina missed calls ɗin da ya tarar guda goma sha uku duk daga Zahra. Ya bi  kiran nata ya lallameta da ta kwantar da hankalinta Faruƙ na nan lafiya yana ta  sharar baccinsa. Sai a yanzu hankalinta  ya ɗan kwanta, sai dai ta yanke wata shawara a zuciyarta wacce tasa a gobe zata aiwatar da ita.
A nasu ɓangaren kuwa Haj. Ikilima ce ta turke Alhaji da tuhumar me yasa yarinyar take kiransa a wannan tsohon daren, ran Alhajin ya ɓaci, a fusace ya dubeta, "Me  yasa kike haka ne ke ikilima? Ina laifin wanda ya damu da damuwar naka? Yarinyar nan fa mummunan mafarki tayi akan  Faruƙ taji  ba zata iya jurewa ba ba tare da ta kira taji a wani hali yake ciki ba, kina kallo kuma haka naje na tarar da Faruƙ shima a firgice yayi mafarki mara kyau, kinga Allah kaɗai ya san ƘARFIN ALAƘAR DA KE TSAKANINSU."
"Ni fa Alhaji yarda ce banyi da yarinyar nan ba, ina zargin akwai wata ɓoyayyiyar manufa a ranta, tun tuni nake baka shawarar ka daina wannan kwashe kwashen dan kar wata rana ka kwaso mana kara da kiyashi. Jikina yana bani akwai wani abu a  ƙasan zuciyar yarinyar nan wallahi, wallahi gwara ASIYAH sau dubu da wannnan ZARAR."
Tsaki kawai Alhajin yayi yaja bargo ya kwanta ya barta nan ta ƙaraci mitarta da a ƙarshe itama ta haƙura ta nemi guri ta kwanta.
Asuba ta gari ALHAJI DA HAJIYA!!!

FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)Where stories live. Discover now