BABI NA TAKWAS
WASU SHEKARU CAN BAYA DA SUKA GABATA
Fuskokinsu cike da damuwa suke kallon likitan da ya gama yi musu bayanin sakamakon gwaje-gwaje da aka yi musu. Alhaji Sa’eed da matarsa Haj. Salma.
Har yanzu lamarin bai sauya ba, dukkan magungunan da aka ɗora Haj. Salma a kai basuyi mata tasiri ba, sakamakon gwajin dai duk abu ɗaya yake bayarwa kamar sauran gwaje-gwajen da aka yi a baya. Likitan ya dubi Alhaji Sa’eed yana mai goge saman karan hancinsa da ɗan yatsansa manuniya. “Idan babu damuwa ina son muyi wata magana dakai Alhaji.”
Kallon matarsa Haj. Salma yayi yace, “Salma ɗan bamu guri, kije mota ki jirani.” Hajiya Salma ta miƙe tare da ɗaukar jakarta dake ajiye a kan ƙaton teburin da ya raba tsakaninsu da likitan, “Ki ɗebi takardun ki tafi dasu mana.” Ya bata umarni. Ta tattara takardun ta zuba a jakar ta miƙa hannu ya bata mukullin motar ta fice daga ofishin likitan. Bayan fitarta suka sauke ajiyar zuciya kusan tare, likitan na ɗan juyawa kaɗan-kaɗan a kan kujerarsa mai juyawa yayinda shi kuma Alhaji Sa’eed ya tattara dukkan nutsuwarsa ga likitan. “ina saurarenka Doctor, wace irin magana ce kake so muyi.”
“Yauwa, Alhaji a kan matsalarku ko ince matsalar matarka, kaga dukkan magungunan da aka ɗorata a kai basu yi tasiri a gareta ba, zuwa yanzu ya kamata ace a hakura da maganar magani dan kar ma su jawo mata wata illar. Dukkan magungunan da aka ɗorata a kai tasirinsu yana da ƙarfi, idan basu yi aiki ba kawai mafutar itace a haƙura, dama aikin magungunan shine suyi stimulating ɗin sinadaran da suke sawa mahaifarta ta samar da ƙwayayen haihuwa kamar yadda matsalarta ta Anovulation take jaza mata rashin samar da isassun ƙwayayen haihuwarta da zasu haɗu da naka su ƙyanƙyashi kansu (fertilization) har su samar da ɗa. kamar yadda ka sani matarka tana cikin jerin masu ɗauke da larurar polycystic ovarian snydrom (PCOS) wacce ita ce maƙasudin anovulation ɗinta, wato mahaifarta ta kasa ko kuma ta samar da rashin wadatattun ƙwan haihuwar ƴa mace wato ovum. Kuma kaga dukkan magungunan da aka bata sun kasa tasirin samar da ƙwayayen, to why not kuyi amfani da dabarun zamani tunda Allah yasa kuna son haihuwar sosai wato ayi IVF (In Vitro Fertilazation)?”
“IVF?” Ya faɗa cikin zaro idanu, kana ya ɗora “Wallahi likitoci kusan biyar daga ƙasashe daban daban da muka ziyarta sun bani makamanciyar shawarar nan, sai na gaza yin ammana da maganar dan ina ganin kamar hakan ya saɓawa addini.”
“No, kokaɗan hakan bai saɓa da addini ba, hakan ba laifi bane sam.” Cewar likita.
“Wani likita balaraben egypt yaso muyi hakan tun shekaru uku da suka wuce da muka je ƙasar dan sake duba mu kan matsalar rashin haihuwar, to a lokacin na so na amince amma sai nayi tunanin gwara in fara gudanar da bincike kafin hakan… amma yanzu Doctor ta yaya kake ganin al’amarin zai kasance?”
Murmushin fuskar likitan ya faɗaɗa, “Wannan abu ne mai sauƙi Alhaji, kawai kuna buƙatar wacce zata yi donating ƙwan haihuwarta ne da za’a ɗauka a haɗa da naka a ƙyanƙyashe su a incubator, wato artificial fertilization. Daga cikin danginka ko da dangin matarka ko kuma wata wacce kuka amince da ita zaku samu tayi donating.”
“Doctor me yasa sai wata? Me yasa baza ayi amfani da na ita Salma ba?”
Likitan yana murmushi yace, “Ƙwan haihuwar matarka yana da raunin da bazai iya fertilizing ba koda a cikin mahaifarta balle a na’urar injin bature, dole wata zaku nemo tayi donating.”
Jikin Alhaji Sa’eed yayi sanyi matuƙa har ya kasa cewa komai, ƙwaƙwalwarsa ta tafi tunanin lamarin dake faruwa tsakaninsu da matarsa, Allah ya bashi dukkan wani jin daɗi na rayuwa tunda ya bashi tarin dukiyar da zata sama masa dukkan abinda yaso a rayuwarsa. Shekarunsu goma sha biyu da aure da matarsa Haj. Salma amma basu taɓa samun haihuwa ba, da farko-farkon aurensu ta taɓa samun ciki sau ɗaya shima bai je ko ina ba ya zube, tun daga nan kuma wani abu makamancin wannan bai sake faruwa ba, tun suna haƙuri da zuba idanu har suka gaji suka fara fita neman maganin haihuwa, sunje a ƙalla ƙasashen duniya sama da guda goma a mabambantan lokuta amma nasara taƙi samuwa, anyi gwaje-gwaje an tabbatar Haj. Salma ita ke da matsalar rashin ovulation wato rashin samar da ƙwan haihuwa duk da cewar kuwa tana al’ada amma al’adar na zuwa mata da rikice-rikice wanda suna daga cikin dalilan anovulation ɗin da ke damunta.
Da farko Haj. Salma da kanta ta bawa Alhaji shawara da ya je ya nemi wata ya aura tunda shi lafiyarsa lau ita ce mai larura, sosai ya nuna mata fushinsa kan maganar ya kuma sanar da ita kar ta sake kawo masa irin wannan maganar, yana tsananin son haihuwa tamkar rufewar ido, amma baya jin hakan zai zama dalilin da zai saka shi yaje yayi wani aure, idan yayi auren yana da tabbacin ita wacce zai aura ɗin tana haihuwa tunda ba a fuskarta zai gani ba kamar yadda bai gani a fuskar ita Haj. Salaman ba cewa tana ɗauke da wata larura da zata hanata haihuwa ba. Jikinsa yana bashi wata rana Haj. Salma zata haifa masa ƴaƴa kamar yanda a karon farko ta taɓa ɗaukar ciki, kullum wannan dalilin yake kalla yaji a ransa bai gamsu ace har abada matarsa ba zata haihu ba.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke tare da sake maida hankalinsa ga likita, “Yanzu doctor yaya za’ayi ayi wannan al’amarin? Idan aka yi IVF ɗin ta yaya zamu ji a jikinmu cewa ɗan da za’a samar ɗan mu ne har mu ji soyayyarsa irin wacce iyaye ke ji a game da ƴaƴayen da suka haifa tunda ba da jinin matata za’a samar dashi ba?”
Dariya sosai likitan yayi har kyakkyawan farin gilashin dake maƙale a saman karan hancinsa na shirin zamewa ya faɗi, yayi saurin tararsa a lokacin da yake cewa, “Kar ka manta fa da ƙwan halittar haihuwarka za’ayi amfani, kuma koda ba’ayi amfani da ƙwan matarka ba ai idan an gama rainon embryo ɗin a cikin incubator za’ayi transferring ɗinsa zuwa mahaifarta ne, kaga kenan ita zata yi rainon cikin ta kuma haifeshi kamar yadda ko wace mace take yi, ta yaya kake tunanin zata ji a ranta ba ɗanta ta yi dakon cikinsa ta haifa ba?”
“Shikenan Doctor, zanje muyi shawara tukanna, duk matsayar da muka yanke na sanar da kai.”
“OK ba damuwa Alhaji, Allah ya ƙara mana lafiya ameen.”
Da yake sun riga sun biya duk wasu kuɗi da aka cajesu sai Alhajin ya miƙe ya zaro wasu rafar kuɗin ya miƙawa likitan na ihsani, likitan ya karɓa yana zuba godiya, ya tura kuɗin cikin ƴar ƙaramar drawer ɗin jikin teburinshi sannan ya miƙe ya takawa Alhajin, sai da ya raka shi har bakin motar sa yana cigaba da ƙara masa haske a kan abinda ya shafi IVF da irin alfanun da hakan ke dashi musamman ma gurin irinsu masu tsananin buƙatar haihuwa. Sun ɗan jima suna tattaunawar sannan sukayi sallama ya shiga motarsa ya samu Haj. Salma na nazarin wata jarida kamar wacce babu damuwa a tattare da ita, tabbas Haj. Salma akwai tawakalli da miƙawa Allah lamura, shiyasa ma baya tunin zai samu haɗin kai da goyon bayanta kan lamarin da ya tabbata zata yi masa kallon kamar yahudanci ne da kuma ƙoƙarin saɓawa Allah, amma dai zai zauna ya nusassheta idan yaci sa’a ta amince shikenan yana maraba da hakan tunda shi ‘ɗa’ yake so indai zai za’a same shi.
Wani irin kallo Haj. Salma ke aika masa mai cike da ma’anoni da yawa lokacin da ya je mata da maganar IVF. “haba Alhaji, yanzu rufewar idon naka har ya kai haka? Ta yaya kake tunanin zuciyata zata gamsu da wannan al’amari? Yaushe zan yarda in aikata saɓon Allah?”
Yayi saurin tararta, “Ba saɓon Allah bane Salma, neman mafita ne, kuma an bamu dama mu nemi mafita kan dukkan abubuwan da suka zamo mana da mushkila a sha’anonin rayuwarmu, kuma an tabbatar min hakan ba matsala bane, please Salma ki amince min, ki taimaka min in samu magaji a rayuwata…” ya ƙarashe maganar cikin wani irin yanayi da yake bayyanar da tsantsar damuwar dake cikin ransa. Jikinta yayi sanyi sosai har ta kasa yin magana. Ya miƙa hannu ya ruƙo nata hannun, “Salma ki yarda dani bazan taɓa ɗoraki a hanyar da ba zata ɓulle dake ba, ki amince da wannan mafitar Salma dan Allah.” Wani tunanine ya faɗo ranta, sam bai kamata tayi masa haka ba, idan ta tuna irin ɗimbin halarcinsa gareta, shekarunsu goma sha biyu da aure bata taɓa haihuwa ba kuma an tabbatar matsalar daga gareta ne, da yaso sai yayi wani auren, ya auro wacce zata zo ta haifa masa ƴaƴa wanda kuma haka ke nufin komawar ragamar komai na gidan hannunta sai dai ita ta koma ƴar kallo, a gefe guda kuma ga yayar Alhajin da ta sako ta a gaba kullum cikin bawa Alhaji shawarar ya ƙara aure take, amma saboda irin tsananin son da yake mata ya toshe kunnuwansa ga dukkan wata shawarar da za’a bashi. Tabbas bata da abinda zata saka masa dashi face bashi haɗin kai tunda itama tana son ace yau ta haihu ta bar abinda ko bayan ranta zai dinga yi mata addu’a. saboda haka cike da sanyi jiki ta nuna masa amincewarta. Ba ƙaramin farin ciki yayi ba da amincewar tata, ya janyo ta jikinsa ya rungume cikin tsananin farin ciki, a ransa yana jin kamar ya samu ‘ɗa’ ya gama.
WANENE ALH. SA’EED?
Yaro ɗan matashi da bai zai wuce shekaru goma ba a duniya, duk wanda ya ganshi take zai kawo a ransa cewa lallai wannan yaro rayuwarsa na cikin ƙalubale kuma tabbas cikin ƙunci da matsin rayuwa yake. Tun yana ƙanƙaninsa yake gwagwarmayar rayuwa, shine shiga kasuwa yin dako ko yin wanke-wanke wajen masu sayar da abinci, shine bin ƴan garuwa yana dafa musu kura idan an gama su ɗan yafa masa abinda zai yi wasu ƴan buƙatunsa. Shine bin wajen masu wankin mota yana yi musu aiki suna ɗan sallamarsa, kusan duk wasu ƙananan sana’o’in hannu da na ƙarfi daidai yadda zai iya yana yi. Yaro Sa’idu kenan wanda ya kasance maraya da ya rasa uwa tare da ƙarancin dangi na kurkusa. A halin yanzu yana hannun abokiyar zaman mahaifiyarsa wacce suka zauna da mahaifiyar tasa har lokacin da ta bar duniya. Bayan rasuwar tata ruƙonsa ya koma hannun Baba Lami wacce ta kasance ita ce uwar gida wacce ita ma take da ƴarta mace mai suna Balaraba. Bayan shekaru biyu da rasuwar mahaifiyar Sa’idun shima mahaifin nasu mai suna Mal. Jafaru ya fara rashin lafiyar ajali, wacce yasha matuƙar wahala kuma dukkan wani abinda ya mallaka ya ƙare gurin neman magani daga ƙarshe kuma ya mutu ba tare da ya bar musu komai ba sai gidan da suke ciki.
Bayan rasuwarsa sai rayuwar Sa’idu ta shiga garari, kafin rasuwar mahaifin nasu yana zuwa makarantar firamare amma bayan rasuwar sai zuwa makarantar ya gagara saboda babu mai ɗaukar nauyin karatun nashi. Baba Lami tana sana’arta ta sayar da koko da kosai da safe, tana sayar da goro sannan tana sayar da alala, saboda haka bata da matsalar komai ta cigaba da zama a gidan tare da ƴarta Balaraba tana bata kulawa yayinda shi kuma Sa’idun komai nasa ya koma kansa, abinci dai tana bashi amma sauran abubuwan buƙatun rayuwa sai dai ya fita ya nema da kansa. A cikin kujiba-kujibar aikin da yake yi ya samu ya tara kuɗi masu yawa ya maida kansa makaranta ya samu ya gama primary har ya shga secondary.
Lokacin da ya gama ƙaramar sakandire ƙarfinsa ya fara kawowa saboda haka sosai ya dinga yin aikin ƙarfi har ya samu ya kuma mayar da kanshi babbar sakandire. Cikin hukuncin ubangiji ya samu yaci jarabawar kammala babbar sakandire wacce gwamnati ta biya musu daga nan ya fara tunanin ɗora karatun nasa zuwa gaba da sakandire ɗin dan a lokacin ya san muhimmancin karatun yana ganin bashi da wata mafitar da ta wuce haka a rayuwarsa, ya san cewa ilimi ne kaɗai zai fitar dashi daga irin rayuwar da ya tsinci kansa a ciki, ilimi ne kaɗai zai zame masa tsanin da zai tattaka har ya kai ga matakan nasara a rayuwa. Wannan dalilin yasa shi ya fara tunanin yadda zai yi ya shiga babbar makaranta saboda har lokacin bashi da wata cikakkiyar sana’a sai kame-kame. Tunanin gadonsa na gidan da mahaifinsu ya mutu ya bari ya fara yi, koda yajewa da Baba Lami wannan maganar ai sai ta ɗora hannu aka fashe da kuka tana faɗin zai tona musu asiri sama da shekaru talatin suke zaune amma yau rana tsaka zaizo da maganar a sayar da gida saboda son tona musu asiri. Duk yadda yaso ta tsaya ta fuskanceshi amma taƙi ta birkice masa sosai yadda dole a ƙarshe ya tashi ya bar mata gidan. Kai tsaye gidan yayar tasa Balaraba ya nufa kasancewar lokacin tuni tayi aure, ya sanar mata buƙatarsa ta son a saida gidan a bashi kuɗin yaja jari ya kuma shiga makaranta, ya samu goyon bayanta ƙwarai kasancewar ita tana ƙaunarsa, ko lokacin da suke gida ma tana taimaka masa da wasu abubuwan, ita ta shirya taje ta fahimtar da mahaifiyar tata inda ta bata shawarar ta siyi gidan da kuɗinta in yaso sai ta cigaba da zama a gidan kuma gidan ya zama nasu su kaɗai kenan babu tunanin raba gado tunda dama shi gado komai daren-daɗewa sai an raba shi. Sosai tayi ammana da wannan shawarar daga nan tasa aka kira dilallan gidaje suka zo sukayiwa gida kuɗi aka kuma kira malamai masu raba gado suka zo suka fitar masa da kasonsa, Baba Lami ta sayi gida ta biya kuɗi aka bawa Sa’idu iyakar abinda ya dace a bashi daga nan ya shiga fafutukar neman shiga makarantar gaba da sakandire.
A makarantar ne ya haɗu da wani abokin arziƙi da ya nemi da ya dinga zuwa kasuwarsu ta canjin kuɗi, babu gardama ya amince ya fara zuwa kasuwar, ashe a nan silar ariziƙinsa yake. Saboda riƙe alƙawari da amana yasa tun daga yaro har ya zama mai gidan kansa, gashi kuma ya ɗauki wasu daga cikin kuɗinsa ya zuba a cikin harkar wacce cikin hukuncin ubangiji arziƙi ya fara samuwa. Cikin wannan lokaci Baba lami tayi wani ciwo wanda yaci kuɗi sosai sai da komai nata ya ƙare, Sa’idu shi ya cigaba da kula da ita da ƙarfinsa da aljihunsa kasancewar ita Yaya Balaraba mijin nata ba wani mai kuɗi bane, hasalima manejin rayuwa take musamman ma yadda ya ƙara aure ya auro mata wata mara mutuncin yarinya kasancewar bata taɓa haihuwa ba, ita kuma yarinyar da ya aura Karima tana shigowa ta fara zuba ƴaƴa kamar karya, wannan yasa ta samu waje take zubawa Yaya balara rashin mutunci. Larurar Baba Lami tasa ta tattara ta koma gida ta cigaba da jinyar mahaifiyar tata har zuwa lokacinda rai yayi halinsa ta koma ga mahaliccinta bayan ta gama neman yafiyar Sa’idu kan hali ko-in-kula ɗin data nuna ga rayuwarsa.
Bayan rasuwarta Sa’idu ya kasance bashi da kowa da ya rage masa face Yayarsa Balaraba saboda haka bai yada ita ba sai ya riƙeta kamar mahaifiyarsa kasancewar dama a kwai tazara mai ɗan nisa a tsakaninsu, dukkan shawarwarinsa tare suke yi.
Rayuwa ta cigaba da tafiya har ya samu ya kammala NCE ɗinsa daga nan kuma ya mayar da hankali kan kasuwancinsa na canji kuɗi wanda a hankali abubuwa suka fara haɓaka, sai gashi cikin lokaci ƙanƙani Sa’idu ya fara tara dukiya mai yawa, cikin haka ya samu yakai yayarsa ta sauke farali shima yaje ya sauke, bayan ya dawo sai ya fara fafutukar yin aure inda ya samu wata ƴar gidan manyan mutane waɗanda suka kasance masu rangwamen tattalin arziƙi ya aura, wato Salma.babu daɗewa da yin auren Salma ta samu juna biyu wanda tukwicinta ya zama zuwa makka sauke farali, sai dai abin rashin daɗin shine bayan gama ibadar hajin kafin su dawo cikin ya zube, haƙiƙa lamarin bai yi musu daɗi ba ƙwarai, amma babu yadda suka iya haka suka tattaro suka dawo cike da damuwa bayan sun sake yin addu’o’in Allah ya basu wani rabon. To fa tun daga wannan lokacin shiru kake ji babu alamun samun wani cikin har tsawon wani lokaci. Da lamarin ya tsawaita wata rana da Haj. Balaraba taje gidan ta bashi shawarar suje asibiti a duba lafiyar Salmar ko ta samu wata matsala sakamakon ɓarin da tayi. Koda suka je asibitin aka dubata aka tabbatar da babu wata matsala daga nan suka dawo suka cigaba da addu’a da zuba ido.
A ɓangaren sana’arsa kuwa likkafa ta cigaba sosai, domin kuwa ba iya ƙasar nan yake harkar canjinsa ba, yanzu har ƙasashen wajen yake fita kan harkar, zuwa lokacin tuni sunansa ya koma ALHAJI SA’EED BABAN NAIRA. A fitar da yake zuwa ƙasashen waje ya samu damar fita da Salma aka cigaba da dubata inda aka gano matsalarta ta anovultion. Wato mahaifarta tana da matsala wajen samar da ƙwayayen haihuwa ko kuma ta samar da su a mafi ƙarancin awo da rauninsu ba zai iya sawa su ƙyanƙyashi kansu tare da ƙwan haihuwar ɗa namiji ba, (fertilization) Daga nan suka ɗorata akan magungunan da zasu taimaka wajen inganta tare da samar da sinadaran da zasu taimaka wajen bayar da umarni ga sassan dake da aikin samar da ƙwayayen su samar dashi. Sai dai kuma mutum na nashi Allah ma na nashi, kuma na Allah shine daidai, kuma Allah mai yin yadda yaso ne ga wanda yaso a lokacin da yaso, da yaso sai magungunan suka ƙi yin tasiri inda daga ƙarshe likitoci suka bashi shawara ya gwada yin IVF (In vitro fertilization) dan kuwa ana dacewa. (IVF na nufin ƙyanƙyasar ƙwayayen halittar mace da na namiji a cikin sarrafaffiyar na’urar bature yadda zasu haɗu su samar da embryo, wato gudan halittar da ake samar da mutum daga gareta, idan aka samar da embryo ɗin sai a ɗauke shi a mayar cikin mahaifiyar mace inda zai cigaba da rayuwa tamkar a ciki aka samar dashi har zuwa lokacin haihuwa.)
Da farko Alh. Sa’eed bai gamsu da wannan shawarar ba dan haka ma bai bata muhimmanci ba dan shi yafi so ya samu ɗa ta hanyar da kowa ya samar da nashi, ba ya son kwaɗanta lamarin da wasu sinadarai na bature. Allah ya jarrabe shi da tsananin son ɗa, yana son ɗa so mai tsanani da ba zai kwantantu ba, kullum lissafin shi idan Salma ta haihu zai yiwa ɗan ko ƴar kaza… zai yi masa kaza… zai siya masa kaza… zai kai shi kaza… abubuwa dai barkatai marasa iyakar lissafi. Duk inda yaga yaro yana jin kamar ya sace shi ya gudu, yana jin dama ace ɗansa ne, yana jin dama wata rana a haifa masa kanar wannan, yana jin dama ace kuɗi suna iya siyan ‘ɗa’ da ya fitar da ko nawa ne ya siya.
Cikin haka wata rana aka wayi gari da rasuwar Haj. Balaraba yayarsa, mutuwar ba ƙaramin girgizashi tayi ba, ya dade bai dawo cikin hayyacinsa ba, kullum kuka yake yana faɗin shikenan ya rasa kowa da komai a duniya, shikenan yanzu bashi da komai a duniya. Da ƙyar aka shawo kansa ya dangana ya koma ya cigaba da rayuwarsa, amma duk lokacin da ya tuno da Balabara sai yayi kuka dan ita kaɗai ta nuna masa ƙauna tun bayan barin mahaifiyarsa da mahaifinsa duniya, mutuwarta kuma ta ƙara masa tsananin son ganin ya haihu ya samu magaji, dalilin da yasa kenan koda Dr. Mansur yazo masa da shawarar yin IVF ya ji ya amince a wannan karon, matarsa kaɗai ce zata zame masa matsala kuma ita ma yanzu ta amince, to yanzu saura da me?
YOU ARE READING
FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)
General FictionLabari a kan wani mai kuɗi (Alh. Sa'eed) wanda Allah ya wadata shi da komai na jin dadin rayuwa, sai dai abu ɗaya ne ya gagareshi wanda a kan fafutukar neman abun idanunsa suka rufe ya aikata wani al'amari wanda shi ya zama silar ginuwar labarin. A...