BABI NA GOMA
Tunda wani abokinsa mai suna Alh. Bukar ya ƙara aure a satin da ya gabata yake jin tamkar anyiwa zuciyarsa allurar son ƙara aure, dukkan wani tunani da zai ɗarsu a ransa na jin son ya kamata ace shima ya ƙarawa kansa girma ne. tuntuni abokansa ke bashi shawarar ya ƙara aure amma yake yin biris da shawarar saboda bashi da tsarin tara mata barkatai a gida. Yanzun da yaga abokin nasa Alh. Bukar ya auro wata zuƙeƙiyar mace buzuwa mai kyawun gaske, duk da cewa bazawara ce amma da sauranta, dan duka haibuwarta biyu mijinta ya rasu.
Tunaninsa yanzu ta ina zai fara? Shi bai cika shiga shirgin mata balle ya samu wacce zai kwasa cikin sauƙi, kuma a gida ga matarsa Haj. Ikilima wacce ya tabbatar ba ƙaramin yaƙi zasuyi ba idan ta ji zai ƙara aure.
Wacce ta zo ransa ita ce, ZAHRA! Tabbas a yanzu bashi da wacce yake da kusanci da ita idan aka cire matarsa da ɗansa sai ita, kuma hujjoji da dama sun bayyana a gareshi da yaga ya cancanta ya nemi aurenta, ko ba dan shi ba dan mara lafiyar ɗansa, ita kaɗai ce take iya tafiyar dashi, ita kaɗai ce take bashi kulawar data dace, tabbas idan ya aureta tamkar ƙarawa miyarsa gishiri yayi, babu ruwansa da Haj. Ikilima da tashin hankalinta, matsalar ɗaya ce kawai, yasan babu jituwa tsakanin ZAHRA da HAJ. IKILMA, ya san kuma zamansu ba zai yi daɗi ba. Sai dai yana ji a ransa wannan ba zai zame masa ƙalubalen da zai hanashi ya tunkari Zahra da son neman aure ta ba, inyaso komai zai biyo baya sa san yadda zasu tare shi.
Da sauri ya miƙa hannu ya jawo wayarsa ya shiga laluben number Zahra, ya kara wayar a kunne bayan ya dannan mata kira. A daidai lokacin ita kuma tana can tare da tauraron zuciyarta USTAZ ALFA wanda suka rigaya suka nutse a tafkin SOYAYYARSU suna ta tafka ninƙaya, kwatsam ta tsinkayi kira a wayarta, ta ɗan ji wani yarr a jikinta saboda bata san wanene ya kira ta a wannan amintaccen lokacin a garesu ba yake kokarin datse musu nishaɗinsu, tana mamakin waye zai kira ta dan kuwa ta san dai mutanen da suke da numberta basu fi mutum huɗu zuwa biyar ba. Cikin rashin jin daɗi ta miƙa hannu ta zaro wayar, rass gabanta ya faɗi ganin sunan ALHAJI ɓaro-ɓaro a fuskar wayar, ‘lafiya kuwa Alhaji zai kirani yanzu?’ ta tambayi kanta a zuciyarta. Ganin kiran na neman katsewa yasa tayi saurin ɗaga wayar ta karata a kunnenta bayan ta ɗagawa Alfa yatsunta biyu, wato ya bata mintuna biyu.
“Zahra kina ina ne yanzu?” ta tsinkayi muryar Alhaji mai ɗauke da tambaya.
Ta ɗan ruɗe kaɗan, “Amm.. amm. Gamu… ina nan bayan side ɗin Hajiya.”
“Kina tare da Faruƙ ne?” ya sake tambaya. “A’a.” ta bashi amsa.
Ya sauke numfashi, “Ina son ganinki yanzu a falona.”
Wannan karon ƴar autar hantar cikinta ce ta kaɗa, lafiya kuwa yau Alhaji zai kirata har zuwa falon ɗakinsa? Duk iya tsawon zamanta a gidan sama da shekara ɗaya ko hanyar side ɗinsa bata taɓa takawa ba, amma yau gashi Alhaji na kiranta har falon ɗaki, to ina Matarsa Haj. Ikilima? Me ke shirin faruwa ne?
“Lafiya dai ko?” Ta tsinkayi muryar Alfa a dodon kunnenta. Ta ɗan yi firgigit kamar wacce tayi farkawar ba-zata a bacci. A ɗan daburce tace, “Lafiya, Alhaji ne ke kirana.” Bai so katsewar hirar tasu ta yau a daidai wannan lokaci ba, “Yanzu kenan sai gobe?” ya tambaya fuskarsa da damuwa.
“Ina tunanin hakan, amma zamuyi waya anjima.” Daga nan suka yi sallama ta yi sauri ta shige gidan ta nufi side ɗin Alhajin.
Daga inda Haj. Ikilima ke zaune tana hango wucewarta ta window, ganin inda ta dosa ne yasa tayi zumbur ta miƙe tamkar wacce aka faɗawa ranar ajalinta. Da gaske ne abinda idanunta suke haska mata Zahra side Alhaji ta nufa.. ‘kutmelesi… abin har ya kai haka?’ ta faɗa ranta tare da saurin ficewa tayi hanyar ɗakin Alhaji dan ta ganewa idonta abinda zai faru, ‘yau koma menene ake aikatawa idanuna zasu gani…’
“Zahra na kiraki ne dan na bayyana miki wani al’amari da zuciyata ta bijiro min dashi wanda nake fatan samun haɗin kai daga gareki.” Muryar Alhaji kenan take ratsa dodon kunnuwanta bayan da ta isa falon nashi ta iske shi yana ta safa da marwa a falon. Gabanta faɗuwa yake, yayinda zuciyarta tamkar ta keto ƙirjin ta fito, wane irin al’amari ne haka? Ta tambayi kanta. “kinyi shiru baki ce komai ba Zahra.” Ya sake magantuwa a karo na biyu. “ina jinka Alhaji.”
Miƙewa yayi ya shiga takawa daga inda take durkushe zuwa bangon falon, yaje-ya-dawo sau uku, kana ya juya mata baya.
“Zahra!” ya kira sunan nata da wata irin murya data gaggauta tunano mata wasu shuɗaɗɗun al’amura, hakan kuma ya ƙara sawa gabanta mugun faɗuwa. “A rayuwa wasu lamura kan zama sanadin faruwar wasu, kamar yadda sanadin larurar Faruƙ kika zo gidannan, to kwatancin haka zuwanki gidannan yayiwa zuciyata sanadin kamuwa da matsanancin sonki! Zahra ina so ki amince min na aureki domin cike wasu manya gurabe da giɓuna da suke cikin dukkan rayuwarmu…” tunda ya ambaci kalmar yana sonta taji numfashinta na neman ɗaukewa, duk iya ƙoƙarin da tayi dan ta daurewar zuciyarta da ƙwaƙwakwarta dan ta saurari dukkan kalamansa hakan ya ci tura, ta dinga fafutuka da zuciyarta tana son saita mata nutsuwarta. Daidai lokacin aka banko cikin falon tamkar an jefota, Haj. Ikilima ce ta shigo idununta jajur cike da masifa da tashin hankali.
“Dama na san za’a zo wannan gaɓar, na san lokacin cin amanata zai zo, to wallahi baku isa ba, yau sai kin bar gidannan tunda ba gidan ubanki bane, kai kuma Alhaji wallahi baka isa ka ci mini amana ba…”
Tuni Zahra ta fice daga ɗakin cikin matsanancin tashin hankali, tafiyar sassarfa take har tana neman faɗuwa, taɓɗijam! Yau Alh. Sa’eed ya kunnowa kansa wutar da ba zai iya kashe ta ba koda kuwa zai tattaro ruwan dukka koguna dake garin, yau ya taɓowa kansa sama da kara, yau ASIRINSA ZAI TONU, yau zai san wacece ita…
Faruƙ na zaune a kan wheel chair ɗinsa, gabansa teburin computer ɗinsa ne yana research kasancewar ya fara rubuce-rubucen project. Ganinta yayi tamkar an jefo ta ta faɗo ɗakin. Yayi ƙoƙarin karkata kansa yana kallonta har ta ƙaraso gareshi ta zube a ƙasa. Ya watsar da komai ya juyo yana fuskantarta yace;
“Yauwa Lady dama jiran zuwanki nake, ina ganin lokaci yayi da ya kamata in fito in faɗa miki abinda ke zuciyata, na fuskanci idan nayi shiru zan cuci kaina, na fuskanci idan na sake Ustaz Alfa zai yi min kyakkyawan kaye… Lady ki sani tun da kika zo gidan nan zuciyata ta kamu da sonki… ina sonki Lady son ban san iyakarsa ba a zuciyata…” da sauri ta sa hannu ta rufe masa baki, so tayi ta kifa masa mahaukacin mari wanda zai dawo dashi daga duniyar rashin hankalin da ya shiga. Ita zai ce yana so? Wane irin al’amari ne wannan? Yanzun nan mahaifinsa ya gama faɗa mata makamanciyar wannan maganar shine shima zai zo mata da irinta? Anya Faruƙ yana da hankali kuwa? Anya ya san matsayinta gareshi kuwa? To yau zata faɗa masa, yau zata fasa daɗaɗɗen ƙwan da warinsa zai addabi kowa a gidan.
“Kai Faruƙ kana da hankali kuwa? Kasan me bakinka yake faɗa kuwa? Ka san ni wacece a gareka kuwa? Ni fa UWA ce a gareka, KAI ƊANA NE!!! Daga jini na aka samar da kai fa…”
“Ƙarya ne Lady! Ƙarya kike kice ke uwata ce, mahaifiyata ta riga ta rasu, ke baki isa ki haife ni ba.. na sani ba kya sona, Ustaz Alfa kike so, amma ki sani muddin kika auri Alfa sai na mutu a ranar…”
“Ya salam! Innanlillahi wa innailaihirraji’un! Wannan wace irin masifa ce haka? Faruƙ ni kake ƙaryatawa? Ashe zaka iya ƙaryata mahaifinka? Ashe zaka iya ƴaryata wacce tayi dakon cikinka har ka samu kazo duniya? Ka yarda dani faruƙ WALLAHI KAI ƊANA NE, ka nutsu in baka labari, ka saurareni in faɗa maka yadda lamarin ya kasance….”
“Bazan saurareki ba Lady, baki da abinda zaki faɗa min in yarda in har ba kalmar amincewa SOYAYYATA zaki faɗa ba… idan har kika ƙi amincewa da soyayyata tabbas kin cika MAƘARYACIYA, domin ke da bakinki kika furta cewa ni MASOYI NE a gareki kuma ki sani na fara sonki ne tun ranar farko na zuwanki gidan nana, tun lokacin da Daddy yace zai aura min ke…”
“Dan nace kai masoyi ne a gareni shine zai zama so na aure? Kai baka san irin SO dake tsakanin uwa da ɗa ba? Haba Faruƙ! Ka shiga hankalinka mana, ka tsaya na faɗa maka yadda akayi ka zama ɗana…”
“Na faɗa miki bana son jin komai a bakin idan ba cewa zakiyi kin yarda da soyayyata ba…” ta miƙe a gigice tana ja da baya, “Na shiga uku ni FATIMA ZAHRA SA’EED! Faruƙ dan Allah ka daina furta wannan kalmar a gareni, ka taɓa ganin inda UWA ta yi soyayya da ƊANTA da sunan aure? Ka daina Faruƙ! Ka daina! Ka shiga hankalinka Faruƙ!”
“Na sani dama ba tun yau ba kallon MAHAUKACI kike min, amma ki sani, koda Allah ya hallice ni a haka bai tauye ni daga samun SHAUƘI da jin soyayyar ƴa mace a zuciyata ba, ke dai kawai kice ba zaki so ni saboda larurata, ba zaki so ni saboda ba zaki iya jure hidimomi na ba, amma ki sani duk abinda kike tunanin Alfa zai miki nima zan iya, idan kina kallona a mai rauni to ki cire wannan tunanin a ranki, ki bani dama ki gani…” a guje ta sake komawa ta rufe masa baki, “Kayi shiru Faruƙ! Kayi shiru! Wallahi idan ka sake furta haka sai na kikkifa maka mari…” Sosai take kuka ta miƙe tsam tayi hanyar waje da gudu... gammm! Taji tayi karo da wani abu, da sauri ta ɗaga kanta, wa zata gani? ALHAJI SA’EED! Alh. Sa’eed ne a tsaye a bakin ƙofar ɗakin ya gama jin dukkan abinda suka ce, idanunsa sun kaɗa sunyi ja zur kamar garwashin wuta. Da ƙarfi yasa hannu ya fincikota ya shaƙe mata wuya tare da tura ta jikin bango. Da wata irin kausasshiyar murya yake faɗin, “Wacece ke! Waye ya turoki cikin rayuwarmu,? Me kika zo yi cikin rayuwarmu? Ko ki faɗa min yanzun nan wallahi ko in kasheki!!!”
Faruƙ ya faɗo daga wheel chair ɗinsa ya dinga jan ciki yana so ƙaraso gurinsu, faɗi yake, “A’a Daddy! A’a Daddy! Kar ka kasheta Daddy kar ka kasheta, ina sonta ina ƙaunarta, kuma kai da bakinka ka taɓa cewa zaka aura min ita! Wallahi idan ka kasheta Daddy nima sai na kashe kaina…”
TAMMAT BI HAMDULLAHI
Ƙarshen littafi na ɗaya, sai mu tara a littafi na biyu dan jin yadda rikicin zai kaya. Yanzu ne aka gama tufkar, warwarar sai a littafi na biyu.
Ko yaya zata kaya tsakanin Zahra da Alh. Sa’eed da kuma ɗansa Faruƙ? Ina labarin Haj. Ikilima kuma? Wane mataki zata ɗauka kan Zahra da Alh sa’eed? Burinta na kawar da Faruƙ zai cika kuwa? Ina labarin Habiba da maigidanta Ustaz Alfa?
Sai naji daga gareku.
WhatsApp no: 08164243585
YOU ARE READING
FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)
General FictionLabari a kan wani mai kuɗi (Alh. Sa'eed) wanda Allah ya wadata shi da komai na jin dadin rayuwa, sai dai abu ɗaya ne ya gagareshi wanda a kan fafutukar neman abun idanunsa suka rufe ya aikata wani al'amari wanda shi ya zama silar ginuwar labarin. A...