BABI NA ƊAYA

106 8 2
                                    

BABI NA ƊAYA

Mutane huɗu ne a cikin tangamemen falon wanda aka ƙawata shi da luntsuma-luntsuman kujeru masu barazanar haɗiye wanda yayi katarin zama a kansu. Alhaji Sa’eed da mai ɗakinsa Hajiya Ikilima suna zaune a kujera ɗaya mai cin zaman mutum uku, yayinda wata matashiyar mace take zaune a wata kujerar dake daura data su Alhajin tana fuskantarsu. A zaune akan kujerar marasa lafiya wato, wheel chair, wani matashin yaro ne, wanda karkataccen kansa ke a sunkuye, yayin da hannayensa ke saman mariƙin kujerar, shanyayyun ƙafafuwansa suma suna gurin da aka tanada dan ajiye ƙafa a jikin kujerar.

Falon yayi tsit! Baka jin sautin komai sai na bugun zuciyar mazauna falon. Ga dukkan alamu kuma wata muhimmiyar magana suke tattaunawa, shiru ya ratsa tsakaninsu.

Matashiyar budurwar nan ce ta katse dogon shirun nasu ta hanyar daidaita zaman farin gilashinta a saman siririn karan hancinta sannan ta nisa tace,

“Ka kwantar da hankalinka Alhaji, ina mai tabbatar maka FARUƘ zai samu tsantsar kulawar data dace a wajenta fiye da wacce ya samu a wajena, na santa sosai tsawon lokaci, she is very responsible (tana da maida hankali) akan duk abinda takeyi, na tabbata zata bawa Faruƙ cikakkiyar kulawa, musamman yadda kwanannan ta gama wani course akan clinical psychology, zai taimaka mata matuƙa wajen kula da Faruƙ.” Tayi shiru tana nazarin fuskar Alhajin wanda zuwa yanzu wani kaso daga cikin tarin damuwar data bayyana a allon fuskarsa ta fara raguwa.

Alhajin ya juya ya kalli matarsa Hajiya Ikilima wacce tunda suka fara tattaunawar bata tsoma musu baki ba, sai dai kallo kawai da take bin bakunansu dashi ta wani tattaɓe baki kamar wacce ake gulmar mahaifiyarta a gabanta. Ya sake dawo da dubansa ga budurwar, muryarsa a sanyaye yace, “Duk ba wannan nake ji ba Asiya, abinda nake tunani shine gaba ɗaya kwaɓar tamu ɗanya zata dawo jagab, duk wani cigaba da aka samu zai tashi a banza,  yanzu sai mun sake shan wata wahala kafin Faruƙ ya yarda da wacce zata zo, ko kin manta irin wahalar da muka sha a baya kafin kema ya yarda dake?” ya jefa mata tambayar yana tsareta da idanu, kai tsaye kuma ta amsa masa da cewa, “Ban manta ba Alhaji, amma ina da yaƙinin hakan bazai kuma faruwa a wannan karon ba, kamar yadda na faɗa maka tun farko cewa ZAHRA cikakkiyar PSYCOLOGIST ce, ta san aikinta matuƙa, Faruƙ zai samu cikakken therapy daga gareta, da duk wata kulawa data dace fiye da yadda ya samu a wajena.”

Cikin sallamawa Alhajin ya maida allon bayansa ya jinginar jikin makarin kujerar tare da dunƙule hannayensa waje guda yace,

“Shikenan Asiya na gamsu, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, ke kuma ina miki fatan alkhairi ina kuma matuƙar godiya da taimakonki gareni, ina fatan Allah ya baku zama lafiya ke da angonki ya baku zuriya ɗayyiba.”
“Ameen!” Asiya da Hajiya Ikilima suka amsa a tare, daga nan ta miƙe tana faɗin, “Bari muyi sallama da abokin nawa ko?” ba ta jira wani ya tanka ba ta ƙarasa gaban wheel chair ɗin da Faruƙ ke zaune ta zauna zaman dirshan tare da tanƙwashe ƙafafu.

“Ammm, Bamboy! (sunan da take faɗa masa kenan) yau ba magana kuma?” ta faɗa tana leƙa fuskarshi dake sunkuye, ko motsi baiyi ba balle ya ɗago kan. “Bamboy magana fa nake kana jina, ko so kake yau mu ɓata?” ta sake faɗa a karo na biyu. Har ila yau dai baiyi ko gezau ba, da taga bashi da niyyar ɗago kan sai tasa hannayenta biyu ta ɗago mishi karkataccen kan nashi, ga mamakinta hawaye ne shaɓe-shaɓe a zane a allon fuskarsa suke atisayen tseren gudu.

“Ya salam! Kuka kake Bamboy, haba ɗan ƙanina, meye abin kuka kuma?” Tayi saurin miƙa hannu ta janyo jakarta ta zuge ta zaro tissue ta shiga goge masa hawayen, dai dai lokacin shima alhajin ya taso yazo gabansu ya tsugunna cikin wani irin yanayi mara daɗi da yake tsintar kansa a duk lokacin da yaga Faruƙ cikin damuwa. Ita kuwa hamshaƙiyar wato Hajiya Ikilima miƙewa tayi ta taɓe baki tare da yin magana can ƙasa-ƙasa yadda ba za’a ji ta ba. “Wahalallu, a haka zaku ƙare cikin bautar gangar jikin da ruhi ne kawai ke motsi a tare da ita.” A ranta kuma tana aiyana lokacin cikar ƙudirinta tare da sabunta tunani akan sabon shirin da zata ɓullo dashi musamman a wannan lokaci da za’a samu sauyin mai kula da Faruƙ ɗin.

FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)Where stories live. Discover now