Ina neman afuwa wajen kuskuren da aka samu na yin tsallaken BABI NA SHIDA wajen posting labarin da posting za ku fahimci yadda tafiyar labarin yake.
Muntasir Shehu
08164243585BABI NA SHIDA
Dawowar Zahra gidan Alh. Sa’eed ta sauya tare da kawo sabbin al’amura cikin gidan, a yanzu kusanci da alaƙa dake tsakaninta da Faruƙ ta ƙara ƙarfi sosai, koda yashe suna tare bacci ne kawai ke rabasu, sosai take bashi kulawa tamkar ta tsakanin ƊA da UWA. Tana bashi physical therapy sosai, bata barinsa cikin damuwa bata barinsa cikin kaɗaici dan kar yawan tunani ya addabi ƙwaƙwalwarsa. Zuwa yanzu da yawa daga cikin ɗabi’unsa an samu sauyin su, ya rage yawan shiga ƙunci da damuwa, yanzu yakan iya yin hira mai tsawo da mutane, yakan ji nishaɗi da farin ciki a zuciyarsa, yakan so su kasance tare da Zahra ko da yaushe, idan yana tare da ita wani irin maganaɗisu yake ji na fizgarsa gareta, baya son yawan kai hannu da take yi tana shafar kansa, yakan ji emotions ɗinsa na canzawa kan hakan, sai dai ya kasa nuna mata rashin son hakan a fuskarsa kamar yadda ya kasa furtawa da bakinsa.
A ɓangarenta itama kasancewa tare dashi yana matuƙar tasirantuwa a zuciyarta, kullum cikin nema masa kariyar Ubangiji take, kullum ƙaunarsa ƙara shiga ranta take, wata irin ƙauna mai ƙarfi da ƙarfin tasiri a zuciya da ƙwaƙwalwa.
Tsakaninta da Alhaji kuwa har yanzu tana kallonsa da irin fuskar da take kallonsa a koda yaushe, bata cika son yin kusanci da shi ba saboda hakan na taso mata da wani miki a zuciyarta, sai dai takan yi ƙoƙarin takure zuciyarta ta saki jiki a duk lokacin da suke tare. Zamanta a gidan ya ƙara sababba wani dalili da Alhajin ke ƙirƙirar musu zaman falo a duk lokacin da yake free a gida. Ba sosai take son hakan ba musamman yadda Haj. Ikilima ta sakota a gaba da dukkan masifarta da bala’inta.
Tsakaninta da Haj. Ikilimar lamarin ya ƙara tsamari kwata kwata Haj. Ikilimar taƙi sakar mata mara, kullum burinta taga tayi sanadin da Alhaji zai sallameta ta bar gidan ko ta samu sararin aiwatar da mummunan ƙudirinta, wannan dawowar da zahran tayi ba ƙaramin cikas ta kawo mata ba, musamman yadda tazo da wani irin salo na rashin bawa kowa dama ya kusanci Faruƙ, duk wasu hidindimunsa ita take yi masa da kanta, wanda bazata iya bane take neman taimakon su Kabiru. Ita kuma bata yadda dasu Kabirun ba balle ta haɗa kai dasu su aikata abinda take son aikatawa ba.
Duk wata hanya da take ganin mai ɓullewa ce ga biyan buƙatarta tabi amma babu nasara. Har wata shawara da Haj azima ta taɓa bata ta ɗauka tayi amfani da ita, wato tayi amfani da Faruƙ wajen jawo shi a jiki har ta samu ta cusa masa ƙiyayyar Zahra a zuciyarsa ta yadda shi da kansa zaisa Alhaji ya kore ta, sai dai maimakon cimma nasara, kwaɓarta ce taso ta jiƙe mata, Faruƙ ya botse mata ya kuma yi nufin faɗawa Alhaji abinda take faffaɗa masa akan Zahran. Da ƙyar ta shawo kansa ya haƙura bazai faɗawa Alhaji ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya al’amura na cigaba da faruwa har tsawon watanni takwas. Zuwa wannan lokaci wani murɗaɗɗen Al’amari ne yake shirin faruwa.
Jaririyar soyayyar da Zahra suka haɗu suka haifa ita da Ustaz Alfa ba tare da ankarewarsu ba ta fara girma. Haƙika KUSANCI tsakanin mace da namiji kan iya yin tasirin zama tsanin da soyayya zata tattaka tabi ta isa inda suke har ta tasirantu garesu ba tare da sun farga ba. Hakan ce ta faru garesu kasancewar a duk sati sukan kasance tare cikin ranaku uku zuwa huɗu, wato ranakun da suke gabatar da karatunsu, karatun nasu tuni yayi nisa kasancewar Zahra Allah yayi mata baiwar fahimtar abubuwa cikin sauƙi kuma gashi ta haɗu da ƙwararren MALAMI da ya san hanyoyin koyar da ɗalibai yadda karatu zai shiga ƙwaƙwalensu. Hakan shi yayi tasirin samar da tunanin juna a zukantansu a duk lokutan da basa tare har sukan ji sun ƙagu ranar karatu ta zagayo. Idan tafiya ta kama shi zuwa Kudu ya kanji damuwa ta yi masa sosai, ya kan ga tsayin lokutan da yake ɗauka a can, wannan tasa ya rage yawan kwanakin da yake yi a can ɗin. faruƙ yana lura da duk abinda ke faruwa tsakaninsu, hankalinsa yana tashi idan ya gansu a tare suna gabatar da karatu, wani iri abu mai tsini ne ke tokare masa ƙirji, tun yana iya jurewa har abin yaso yafi ƙarfin ƙirjinsa, ƙarshe ya dawo musu da bara-bana. Yace shi lallai yanzu sai dai a dinga yi musu karatu tare kuma ranaku ɗaya. A ganinsa hakan zaiyi tasirin rage ƙarfin alƙar data ƙullu tsakaninsu. Yasan idan yana tare dasu dole su haƙura da wani abin. Sai dai abinda bai sani ba shine, tasirin soyayya yana da ƙarfin da ba duk wani shamaki bane zai iya tareshi. Kasancewarsa tare da su bai yi tasiri ko kaɗan na hanasu aikawa da juna saƙwannin zuciyoyinsu ba.
Soyayyarsu ƙara girma take amma dukkan su babu wanda ya saka a ransa cewar son ɗan uwansa yake. Dukkansu babu wanda ya taɓa yin soyayya babu wanda ya taɓa yin nazari a kanta balle su fuskanci cewar lallai zuciyayon su sun karɓi wani muhimmin saƙo mai ƙarfi da tasirin gaske.
Ranar wata juma’a da yamma kasancewar ba ranar zuwan Alfa bace, dan haka suna zaune a falo ita da Faruƙ. Kwata kwata yau yaƙi sakin jiki da ita, tun safe take fama dashi amma yaƙi bata kulawar data dace.
Jikinta a sanyaye ta dube shi tace, “Beta, ya kamata ace zuwa yanzu ka daina biyewa zuciyarka wajen yin fushin babu gaira babu dalili, rayuwa fa tafiya take, girma ƙara kama mu yake, wata rana fa zakayi aure, nima zanyi kaga dole mu rabu, baka san nan gaba dawa rayuwa zata haɗaka ba, Faruƙ ba kowa bane zai iya jure abinda wani ya jure ba. Na sani lalura ce take saka shiga cikin irin wannan yanayin, amma akwai yadda zakayi ka dinga kiyaye kanka daga haka, ka sani ina iyaka bakin ƙoƙarina wajen ganin baka saka kanka cikin damuwa ba, amma me yasa kake ƙoƙarin ganin ka sanyaya min gwiwa? Me yasa kake so kaga cigaban da muke samu yana daƙilewa,? Kasan wani irin farin ciki mahaifin yake ji idan ka kasance cikin walwala? Kasan wace irin damuwa yake shiga idan kana cikin damuwa? Haba Faruƙ, ka dinga ƙoƙarin tausar zuciyarka a duk lokacin data ayyana maka yin fushi.”
Ta sauke numfashi mai ƙarfi, takai hannu da niyyar taɓa kansa amma sai yayi saurin zamewa, “Lady, nasan dama zakiyi aure zaki barni, na sani kina soyayya da Ustaz Alfa, zuciyarki tana sonsa, shima kuma yana sonki. Shikenan kije ki aure shi, amma ki sani zuciyata bazata taɓa daidaita yadda kike so ba, na sani nakasata babu abinda ba zata jawo min ba, amma bani da yadda zanyi, haka Allah yaso dani…” Hawaye suka soma zubo masa, da sauri ta isa gabansa cikin wani irin yanayi na kiɗimar jin maganganunsa. “Me yasa kake faɗar haka Faruƙ? Me yasa kake yadda da abinda zuciyarka take ayyana maka? Wa ya faɗa maka muna soyayya da Alfa? Faruƙ kayi gaggawar ƙaryata zuciyarka, kayi gaggawar cire wannan tunanin a ranka!”
“Wallahil azim kuna son junanku ke dashi, na ga hakan a fuskokinku, naga hakan a emotions ɗinku, naga hakan a saƙwannin da zuciyoyinku ke aikawa juna, Lady larurata fa bata tauye ni ga fahimtar emotions ɗin mutane a rayuwa ba, duk da ban kasance wanda yake rayuwa a cikin mutane ba amma ki sani ina yin bincike akan soyayya, na san abubuwa da yawa a kanta wanda zakiyi mamakin jin hakan daga gare ni, amma ke ina so ki kalli cikin idona ki ƙaryata ni cewa ba soyayya tsakaninki da Ustaz Alfa…”
Cikim kuka ta katse shi, “Faruƙ shin laifi ne idan nayi soyayya? Laifi ne dan na ɗabbaƙawa zuciyata sunnar ko wace zuciya? Macece nifa, Allah ya halicce ni da jin shauƙi da son abinda na gani nayi sha’awarsa, me ye a ciki dan nayi soyayya Faruƙ? Ka faɗa min meye laifina? MENE NE LAIFIN ZUCIYATA DAN TAYI SOYAYYA?”
“Cin amana! Cin amana Lady, idan har kika bari zuciyarki ta karɓi soyayyar wani to ina tabbatar miki kinci amanar wasu zuciyoyin…”
“Zuciyoyin suwa Faruƙ? Ka faɗa min zuciyoyin suwa na ciwa amana?”
Shiru yayi mata ya kasa magana, “Faruƙ ka faɗa min, na kasa gane inda maganganunka suka dosa ka faɗa min.”
“Bazan iya faɗa miki komai ba, kawai ki saka a ranki soyayyarki da Ustaz Alfa zata haifar da matsaloli masu yawa.”
“Na shiga uku! Wai faruƙ kanka ɗaya kuwa? Anya iya Asperger’s ce kaɗai matsalarka kuwa? Anya baka da other mentality problems kuwa?”
“Na sani zaki iya kirana da komai ma saboda na zan kawo miki cikas a soyayyarki… kuma sai dai ki kirani da duk abinda kika ga dama, amam sai na faɗa miki abinda yake zuciyata…”
Miƙewa tayi a guje ta nufi ɗakinta cikin kuka ta barshi a nan, dai dai lokacin kuma Hajiya Ikilima ta shigo falon, dawowarta kenan daga unguwa, ganin yadda Zahra ta bar ɗakin cikin kuka da kuma yadda taga shima Faruƙ ɗin idanunsa fal hawaye sai taji wani irin mai kama da murna ya ziyarci ranta. Sai taji tana son sanin abinda ke faruwa, da sauri ta ƙarasa gareshi ta zauna a kujerar dake gefensa.
“Faruƙ lafiya meke faruwa ne?”
“Babu komai.”
“Ah ƙaryane, yaya zan shigo in ganku kuna kuka in tambaya kuma kace min babu komai, ka faɗa min meke faruwa? Ko wani abun tayi maka?”
“Nace miki babu komai, idan baki yarda ba shikenan.”
Taɓe baki tayi tana ji a ranta kamar ta kikkifa masa mari, kwata kwata bashi da kunya a ganinta, sai ya fake da larura ya dinga sirfawa mutane rashin mutunci.
“Ku kuka sani, in tayi wari maji, dama ai duk ƙarfin alakar jini da hanta, dole wata ran a gansu a rana.” Ta faɗi ta haka tare da miƙewa tabar falon.
Zazzaɓi mai zafi ne ya rufe Zahra wanda ya hana mata fitowa tun daga lokacin har zuwa dare lokacin da Alhaji ya dawo, yana ta zuba ido yaga fitowarta amma shiru har bayan isha’i. da ya gaji ya tambayi Haj. Ikilima ko ina zahra? Taɓe baki tayi tace dashi itama tunda ta dawo daga unguwa bata ganta ba. Tsaki yaja ya miƙe da nufin yaje ɗakin da kansa, da sauri Hajiya Ikilima tayi saurin dakatar dashi. “Haba Alhaji, ka bari a sa Hajara ta duba ɗakin nata mana, kasan dai bai kamata ka dinga shiga ɗakinta ba ko?”
Ya koma ya zauna cikin sanyi jiki, ko kaɗan baya jin daɗin abinda Hajiyar take masa. Hajiya ta miƙe ta ɗauki waya ta kira ɓangaren masu aiki, jim kaɗan aka ɗaga da sallama, ba Hajara bace ta ɗaga, Sahura ce wacce itama ƴar aikin gidan ce. “Sahura zo maza ki same ni a falo.” “To Hajiya” Ta ajiye wayar ta dawo ta zauna. Jim kaɗan Sahura ta shigo falon da sallamarta, Haj. Ikiljma tace mata taje ɗakin Zahra ta duba taga ko lafiya bata fito ba, ta amsa da to ta miƙe ta nufi ɗakin zahra. A kwance ta same saman gado ta rufa da ƙaton bargo amma duk da haka jikinta karkarwa yake. Da sauri ta ƙarasa tana faɗin “Anty Zahra lafiya?” bata iya amsawa ba saboda yadda haƙoranta ke karo da juna. Da sasarfa ta juya ta koma falo ta sanar dasu Zahra na kwance babu lafiya da alama kuma zazzaɓi ne mai zafi ya rufeta. Zumbur Alhaji ya miƙe ya nufi ɗakin Hajiiya Ikilima na binshi da kallon mamaki, babu tantama Alhaji SON yarinyar nan yake, to in ba haka irin wannan kiɗima haka? Ko ita baya nuna damuwarsa idan bata da lafiya kamar yadda ya nuna haka, ai kuwa sam basu isa ba, bazata taɓa barin wannan lamari ya kasance ba.
Alhaji ya isa ɗakin nata ya sameta a yanayin da Sahurar ta faɗa masa, ya ɗan ɗaga bargon kaɗan, “Zahra zazzaɓi kike yi ne haka amma kika kasa kira ki sanar?” ya saki bargon ya juya a rikice zuwa falon, a tunaninsa zai ga Hajiyar ya kirata ta taimaka mata ta tashi suje asibiti amma sai ya tarar wayam ba kowa a falon, ya ɗauki waya ya kira ɓangaren masu aiki ya ce duk su zo su same shi a ɗakin zahra, sannan ya kira waje ya sanarwa Sammani direba da ya jawo mota zuwa bakin falon.
Su Sahura na ƙarasowa yasa su taimaka su tashe ta, suka hau gadon su biyu suka taimaka ta tashi da kyar, Alhaji faɗi yake, “Ku bita a hankali Sahura.” Da suka sauko da ita daga kan gadon saura ƙiris ta faɗi, zaraf Alhaji yayi saurin kai hannunsa ya riƙota… duk da halin da take ciki na matsanancin zazzaɓi sai da taji wani yarrr a jikinta. Nan da nan tayi saurin zamewa daga hannunsa tayi ƙoƙarin ƙarfafa jikinta dan kar ya kuma sa hannunsa a jikinta.
“muje mota maza!.” Ya faɗa tare ta ficewa duk ya ruɗe, yana fita falo ya ci karo da Kabiru yana turo Faruƙ a kan kujerarsa.
“Kai Faruƙ kana ina Antinka babu lafiya?”
Bai yi magana ba, bai kuma kalli inda suke ba, shi haushin kowa ma yake ji, yasan rashin lafiyar tata ba ta komai bace face ta maganganun da sukayi ɗazu, a ganinsa kuma duk abinda ya faɗa mata gaskiya ya faɗa. Da Alhajin ya fuskanci bazai yi magana ba sai ya umarci su Hajara da su fitar da Zahra zuwa mota, ya bisu a baya, bayan sun saka ta a motar Alhajin yace da Hajara ta shiga motar su tafi tare dan ta taimaka mata yayinda shi kuma ya shiga gidan gaba na motar gefen direba, Sammani yaja motar suka nufi wani babban clinic dake cikin unguwar. Babu ɓata lokaci aka shigar da ita ɗakin duba marasa lafiya babban likitan asibitin ya shiga duba ta. Allura kawai yayi mata tare da rubuta wasu magunguna da zata yi amfani dasu, Alhaji da kanshi ya shiga pharmacy ɗin asibitin ya siyo magungunan sannan suka tafi, sai da suka biya wani babban shago aka sai mata kayan marmari irin wanda mara lafiya zai buƙata sannan suka dawo gida.
Ran Haj. Ikilima in yayi dubu ya ɓaci, abinda Alhajin ke yi ya fara isarta, gwara ya fito fili ya ce son Zahra yake, domin kuwa idan babu so babu abinda zai sa ya dinga wannan jigilar a kanta. Saboda haushin sa da take ji yau ƙin kwana tayi a ɗakinsa, har ya gaji da kiranta a waya ya shareta ya kwanta barcinsa. Washe gari ma da haushinsa ta tashi, koda taje gaishe shi ma can ƙasa ƙasa ta gaida shi tana wani ciccin magani. Kallo kawai yake binta dashi a ransa yana mamakin halin jarabar kishi irin na mata, shi ba cewa yayi yana son Zahra balle ta ji zafinsa, kawai dan ya kula da mai kulawa dashi da ɗansa ina laifinsa? Haba sha’anin mata sai dai a barsu da halinsu.
Jikin Zahra ya warawre, sai dai har ƴar rama tayi, kamar yadda ta saba gudanar da ayyukanta kullum haka ta tashi tunda sauran duhun safiya bayan tayi sallah ta shiga kicin ta girkawa Faruƙ girki kamar yadda ta saba masa, daga nan ta shiga ɗakinsa ta same shi kwance a kan resting bed, ba bacci yake ba, idanunsa ma suna saitin ƙofar shigowa, yana ganin ita ce ta shigo ya rufe idanun nasa, kwata kwata baya son ma su haɗa idanu. Murmushi kawai tayi ta isa gareshi, ita ba zata iya fushi dashi ba, ba zata iya share shi da daina yi masa hidindimun da ta saba yi masa ba. Kanshi ta taɓa, “Beta, ya kamata a tashi a yi break fast ko?” bai motsa ba bai kuma buɗe idanun nanshi ba. “faruƙ ka tashi nace ko!” buɗe idanunsa yayi a hankali, “Good morning.”
“Morning, da fatan lafiya ka tashi.” Tasa hannayenta ta fara ƙoƙarin tashinsa, saurin dakatar da ita yayi, “No, zan iya tashi, jawo min wheel chair ɗin kawai.” Kallon sa tayi cikin wani irin yanayi na rashin jin daɗi, sai dai bata ce komai ta janyo masa wheel chair ɗin ta koma gefe ta zuba masa idanu taga yadda zai sauka daga resting bed zuwa wheel chair. A kiciniyar da yake ta sauka daga gadon ya zame ya faɗo ƙasa tim kamar an yadda buhun kaya, da gudu ta ƙarasa gunsa tana faɗin, “ Ka gani ko, kaga abinda ka jawowa kanka, zan taimaka maka ka hanani gashi yanzu kana neman jiwa kanka ciwo, ka fiye gardama da taurin kai wallahi.” Sosai yaji haushin furuncinta, hakan yasa ya yunƙura da dukkan dabarunsa ya tashi ya zauna kan wheel chair ɗin ba tare da ya bari ta kuma taɓa shi ba. Da kansa ya tura kujerar har zuwa wajen cin abinci. Jikinta a sanyaye ta miƙe tabi bayansa, sai dai koda ta isa gurin cin abincin kujera jawai taja ta zauna ta zuba masa idanu taga ta yadda zai yi serving ɗin kansa. Ya fuskanci manufarta, dan haka ya buɗe muryarsa iyakar ƙarfinsa ya ƙwala kiran Hajara, sai dai girman gidan da kuma tazarar dake tsakanin inda suke da su Hajara suke da kuma rashin ƙarfin sautinsa yasa kiran nashi bai je inda suke ba balle ta san ana kiranta,ya sake ƙwala kira a karo na biyu amma shiru, har yayi nufin tura kujerar ya isa ga babban teburin falo dan yayi amfani da waya yayi kira sai ga Haj. Ikilima ta fito daga kicin hannunta riƙe da plates ta biyo ta wajen cin abincin, ajiyar zuciya ya sauke yace, “Yauwa Mommy, taimaka ki haɗa min tea ɗin nan dan Allah.” Kallonsa tayi sama-ƙasa ta watsar, “Ni ce ma zaka sa na haɗa maka tea dan kunya bata cika maka ido ba? Ko kuwa ni kuku ce da zaka saka ni yin serving ɗinka? Mtsew!” taja dogon tsaki ta wuce abinta. Zahra bata ji daɗin abinda ya faru ba ko kaɗan, taso tayi masa komai amma halin da yake nuna mata yasa take ganin gwara ta dinga ƙyale shi kan wasu abubuwan dan ya fahimci amfaninta gareshi. Tashi tayi ta shiga haɗa masa tea ɗin ba tare da ta tanka masa ba, sai da ta haɗa masa duk abinda ta san zai buƙata akan ɗan ƙaramin teburin sa ɗan madaidaici wanda tsayinsa yake dai dai yadda zai iya amfani dashi, ta tura masa teburin tare da komawa kan kujera ta harɗe hannaye a ƙirji ta zuba masa idanu.
Alhaji ya fito cikin shirin fita ofice, kai tsaye dinning section ɗin ya nufa dan karyawa, tun kafin ya ƙarasa ya fara yiwa Zahra magana, “A’ah… patient jikin ya warware kenan?” kanta a ƙasa ta amsa, “Jiki yayi sauƙi Alhaji.” “To masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi da lafiya, ameen.”
Kujera yaja ya zauna a bakin kafcecen Dinning table ɗin, Zahra ta miƙe da sauri ta shiga haɗa masa abin karyawa. Kallon Faruƙ yayi da ya maida hankali kan shan tea ɗinsa da soyayyen dankalin turawa, “My son.” “Na’am daddy good morning.”
“Morning, da fatan ka tashi lafiya.”
“Lafiya lau Daddy.”
“Ina fatan dai kayiwa Antinka sannu da jiki.”
“Nayi mata.”
“Ok.”
Zahra ta gama haɗa masa abin karin ta tura masa, sannan ta ɗauki wasu plates ta ɗibi abinda zata iya ci ta juya da nufin tafiya.
“Ina kuma zaki je?” muryar Alhaji ta katsi hanzarinta, bata juyo ba ta bashi amsa, “Zanje ɗaki ne, Ina son gabatar da wani abu ne.”
“Amma ai kamata yayi ki fara tsayawa ki karya tukun sai kije kiyi duk abinda zakiyi.”
“Akan lokaci nake son gudanar da aikin.”
“OK shikenan babu damuwa, idan baki fito ba har na kammala break ɗin to sai dai ince sai na dawo.”
“A dawo lafiya, Allah ya tsare” bata jira taji ameen ɗinsa ba ta wuce.
Wani tunani ne yazo ransa, kamar wani abu mara daɗi ya faru tskanin Zahra da Faruƙ, tun jiya ya kamata ya fuskanci hakan, amma sai ya ta’allaƙa hakan ga yanayin Faruƙ ɗin ne da in abinshi ya motsa sai ayi masa magana sau ɗari yaƙi tankawa. A shigowarsa falon a yanzu ma ya kamata ya tabbatar da hakan duba da yanayin da ya same su a ciki kowa na harkar gabansa, yasan dai idan lafiya-lafiya baya taɓa zuwa ya same su ba tare da suna manne da juna ba.
“My son, ko wani abu ya faru tsakaninka da Antinka ne?”
“A’a, babu abinda ya faru.”
“Ka faɗa min gaskiya.”
“Gaskiyar kenan Daddy.”
“Amma ai ban saba ganinku cikin irin wannan yanayin ba.”
Faruƙ yayi shiru saboda ya fara gajiya da tambayoyin mahaifin nasa, kawai sai ya maida kansa ya cigaba da kurɓar tea ɗinsa, ko da ya fuskanci butsancin nashi zai motsa sai ya rabu dashi ya cigaba da karyawarsa, amma ya saka a ransa zai zuba musu idanu yaga iya gudun ruwansu.
MUGUN GANI
Washe gari da safe Hajiya Ikilima ta samu Alhaji a ɗakinsa yana shirin fita ofice, ta taimaka masa ya gama kintsawa sannan ta gabatar masa da buƙatar ta na son zuwa asibiti ganin likita, a cewarta tun jiya take jin jikinta babu daɗi tana so taje a duba mata BP ɗinta.
Ba tare da Alhaji ya kalleta ba yace, “Yau kam gaskiya cikin hanzari nake balle in sauke ki, kin san ana samun go slow a hanyar sosai, saboda haka sai dai Sammani ya kaiki ko kuma ki jira zuwa gobe sai muje tare.”
“Sammanin kawai ya kaini dan bazan iya jira zuwa gobe ba.”
Yana ɓalle maɓallin rigarsa ƴar ciki yace, “Shikenan, ki buɗe drower ki ɗauki kuɗi.”
Miƙewa tayi da hanzari ta nufi ƴar madaidaiciyar drower ɗin ta buɗe ta zari rafar kuɗi ta miƙe ta koma wajensa.
“Nawa kika ɗauka?”
“Dubu Ashirin ne.”
“Sun ishe ki?”
“Eh zasu isa.”
“Yawan ƙorafin ki ne bana so shiyasa nace ki ɗauka da kanki dan karki zo daga baya kice min kuɗin da na baki basu isheki ba.”
Ya saka babbar rigarsa, ta tashi ta ɗauko masa hularsa wacce tasha wanki sai ƙyalli da ɗaukar ido take, ita ta ɗora masa hular a kansa sannan ta ɗauki turarukansa masu ƙamshi ta fesa masa, yayi matuƙar yin kyau sosai, babu wanda zai ce ya kaiwa shekaru sittin da ɗoriya hari saboda tsabar hutu da jin daɗi.
A tare suka jera har zuwa falon inda suka iske Zahra da Hajara mai aiki suna hira, Faruƙ na gefensu yana danna computer ɗinsa. Kusan tare suka gaida Alhajin da Hajiyar, Alhaji ya amsa cikin sakin fuska yayinda ita gogar ta amsa kamar yadda ta saba. “my son game ɗin ce ko kuma research kake yi?”
“Eh ina duba wani abu ne.”
“Madalla, a dage a cigaba da bincike, ammm wai ni yaushe ne ma zaku yi exam ne?”
“Nan da two weeks ne.”
“OK, ina sauri ne, idan na dawo sai muyi maganar.”
Ya juya ga Zahra, “Malama Zahra’u sai na dawo.” Ta amsa tayi masa addu’ar da ta saba. Bayan fitarsa Haj. Ikilima ta sanar da Sammani direba ya shirya zai kai ta asibiti nan da ƙarfe goma, daga nan ta wuce ɗakinta dan shiryawa.
Duban Faruƙ Zahra tayi, “Beta, ashe an kusa zama graduate?” murmushi ya bayyana a fuskarsa har ya bar abinda yake a computer ɗin ya ɗago ya kallesu, “na kusa in zama cikakken Geographer.”
“Very good, idan ka gama zan mu dinga zama da kai kana bani labarin yankunan duniya da abinda ya shafi ɓangarorinta.”
“Ko yanzu kike so ai zan baki.”
“Um um, abin zai yi mana yawa, ga karatun Ustaz Alfa ga naka? Ai sai kaina ya fashe.”
Sunan Ustaz Alfa d ta faɗa shi ya canza masa yanayin fuskarsa, ɓacin rai ya bayyana, shi baya son idan suna hira ta dinga sako zancen Alfa, ya fi so ta bawa kowa lokacinsa, bayan son tana haɗa cakuɗa musu lamuransu da juna, a yadda yake ji a ransa yana gaf da sa Daddy ya sallameshi in yaso sai yasa ya nemo masa wani malamin ya ƙarasa Saukar ALQUR’AN ɗinsa da saura kaɗan ya sauke.
“Ya ya dai beta?”
“Ba komai.” Da alamun ɗacin rai cikin maganarsa, ta fuskanci dalilin canzawarsa, ranta ya ɗan sosu, ta rasa dalilin da yasa yaron nan yake mata haka, ita fa yanzu ta gama amincewa kanta tana jin son Alfa a ranta duk da har yanzu abin nasu bai bayyana a zahiri ba, amma tana mamakin yadda Faruƙ yake ɗaukar lamarin, kamar KISHI yake da hakan, damm taji gabanta ya faɗi da wannan tunanin, cikin gaggawa ta kori tunanin dan bata so ma ya zauna a ƙwaƙwalwarta balle zuciyarta ta samu damar sarrafa shi har amsa ta fito fili wacce take da yaƙinin amsar zata iya yi mata ƙamshin-mutuwa…
Fitowar Haj. Ikilma ne ya katse mata duniyar tunanin data shilla, “Hajara je ki kira min Sahura kuzo ku gyara min toilet ɗina.” Cikin biyayya ta miƙe ta nufi sashensu na masu aiki dan aiwatar da saƙon Hajiyar. “Faruƙ zan je asibiti yau ko zaka raka ni kaga gari?” maimakon shi Faruƙ ɗin yaji ko ya zargi wani abu cikin abinda Hajiyar tace sai Zahra ce taji dukan zuciya kwatankwancin wanda taji ranar da kunnuwanta suka jiyo mata hajiya ikilima na maganar bin hanyar da zasu kashe Faruƙ ɗin, a gaggauce ta miƙe, “Kiyi haƙuri Hajiya, Faruƙ bazai iya fita ba saboda yana da allergy da ganin motoci, idan yaga manyan motoci zai tsorata ne kuma komai na iya faruwa ga lafiyarsa…” wani mugun kallo da Hajiyar ke watsa mata bai sa ta dakata daga abinda take faɗa ba.
“Ke dalla yi min shiru, an faɗa miki ni duk wasu tsare-tsarenki na ƙarya zasuyi tasiri a kaina? Ko kuwa kina so ki nuna min kin fini ƙaunar Faruƙ?”
“Ba haka bane Hajiya, ina tsoron…”
“Kina tsoron kar na fita dashi in jefer dashi ne ko me?”
“Ba manufa ta kenan ba… kawai..”
“Ke ni kin ishe ni, (ta juya ga faruƙ) kai faruƙ zaka bini ko kuwa? Kaga ya dace ace kana fita kana ganin yaya duniya take musamman kai da kake karatu da ya shafi duniyar ciki da wajenta.”
“Bazan iya karya dokar larura ta ba, kawai kije abinki ba sai na fita ba, kamar yadda Lady ta faɗa miki idan naga manyan motoci komai zai iya faruwa dani.” Cewar Faruƙ.
Tsaki ta buga ta juya fuuu tayi ɗakinta. Bayan fitarta Zahra ta taka ta isa gareshi, “Beta, ko da wasa kar ka yarda wani dalili yasa Hajiya ta fitar dakai daga gidan nan.” Tana faɗar haka ta juya ta nufi ɗakinta cikin wani irin yanayi mara daɗi da sanyin jiki.
Babban Asibitin unguwar mai suna HOMEWAY SPECIALIST HOSPITAL babban asibitin ne na masu kuɗi, (privet hospital) sai kuma masu rufin asiri da ƙarfin zuciya da kanyi ƙarfin halin zuwa dan a basu ingantacciyar kulawa. Haj. Ikilima ta fito daga cikin asibitin zuwa harabar ajiye motoci bayan taga likita ya gama dubata, tana isa bakin motar ta kira Sammani direba ta miƙa masa wata takarda ɗauke da list ɗin abubuwan da take buƙata, ta zuge jakarta ta duntso kuɗi ta miƙa masa tace ya shiga wani babban mall dake kusa da asibitin yayi mata siyayyar abubuwan data rubuta a takardar. Sammani ya karɓa ya nufi mall ɗin ita kuma ta zagaya gaban motar ta jingina da ita, ta zaro wayarta ta buɗe wasu hotuna ta shiga nazarinsu.
Daidai lokacin itama Habiba ta fito daga asibitin bayan ta ga likitar yara ta duba Saleem da yake fama da matsananciyar mura da tari a ƴan lokutan, cikin sassauƙar shiga take ta daidai arziƙinsu, kanta sanye cikin niƙabi ta ɓoye fuskarta. Kamar ance ta kalli ƙasa ta kai dubanta kan wasu takardu yashe a ƙas, kuma ga dukkan alamu takardun masu muhimmanci ne tunda ga tambarin asibitin nan ɓaro-ɓaro a jikinsu, ta sunkuya a hankali ta ɗauki takardun ta shiga jujjuyasu, ta ɗaga kai ta shiga nazarin mutanen dake shawagi a farfajiyar asibitin, kai tsaye bata san wa zata tunkara da takardun ba tunda bata buɗe taga sunan dake jiki ba, koma ta buɗe ɗin taga sunan ta ya zata gane mai su a fuska, kawai sai ta fara shawarar ta kaiwa masu gadi, har ta fara tafiya ta doshi gurin masu gadin sai ta biyo ta hanyar da Haj. Ikilima ke jingine jikin kafceciyar motarsu, kawai sai taji jikinta ya bata ta yiwa hajiyar magana taji ko takardun nata ne, ta matsa sosai gareta tayi mata sallama. Kadaran-kadahan Hajiyar ta amsa mata tare da juyowa tana nazarin fukarta dake saye cikin niƙab.
Miƙa mata takardun Habiba tayi cikin sauri tare da cewa, “Waɗannan takardun na gani a bakin ƙofar asibiti shine na kawo ki duba ko naki ne.” bata karɓi takardun ba ta ajiye wayarta dake hannunta a saman gaban motar ta shiga zuge jakarta dan ta duba ta gani ko nata ne, daidai lokacin ita kuma Habiba hankalinta yayi kan kafceciyar wayar ta Hajiya Ikilima dake ajiye saman gaban motar, kamar hoton mijinta take gani tare da wata, nan da nan ta murje idanunta ta ƙara matsawa sosai gaban motar tana ƙara leƙa wayar, rass gabanta yayi mummunan faɗuwa, bata ko tantama wannan hoton mijinta ne tare da wata mace da suke fuskantar juna a bisa fararen kujeru da teburi a tsakiyarsu, kamar karatu suke amma kamar kuma hira suke mai daɗi aka ɗauki hoton saboda yadda fuskokinsu ke cike da murmushi sunawa juna aike ta cikin wani shu’umin kallo… kamar ma basu sani ba aka ɗauki hoton, duk wannan nazarin Habiba tayi shi ne cikin abinda bai gaza sakwanni goma zuwa shabiyar ba, tuni ta ruɗe ta gigice har bata san lokacin da takardun suka zame daga hannunta suka faɗi ba. Hajiya Ikilima tayi saurin ɗagowa ta kalleta bayan ta gama caje jakar bata ga takardun sakamakon gwaje-gwajen da akayi mata ba, tabbas waɗannan takardun nata ne, wata ƙila lokacin da take ƙoƙarin tura su cikin jakarta ne suka faɗi ba tare da ta sani ba, cikin sauri tace, “Wallahi takarduna ne… a’ah ya kuma kika jefar da takardun?”
Da sauri Habiba ta sunkuya ta ɗauko su ta miƙa mata, tun Hajiyar bata gama riƙewa ba ta sakar mata ta bar gurin a gaggauce kamar wucewar iska, Hajiyar na ƙwala kiranta dan tayi mata godiya amma ina tuni Habiba ta kai bakin gate ɗin asibitin. Taɓe baki Hajiyar tayi a fili tace, “Anya wannan lafiya take kuwa? Koma dai menene tunda ta kawo min takarduna shikenan, Allah ya raba bawa da wahala.” Daidai lokacin Sammani direba ya ƙaraso da niƙi-nikin manyan ledojin siyayyar da ya yiwa Hajiya, boot ɗin motar ya buɗe ya saka kayan a ciki sannan ya buɗewa Hajiyar gidan baya na motar ta shiga tana masa sannu.
Habiba kuwa tunda Allah yasa yau tayi MUGUN GANI gaba ɗaya ta rikice ta fice a hayyacinta, babban tashin hankalinta bai wuce matar da ta gani tare da mijinta a hoto ba, da gani ƴar masu kuɗi ce duba da yanayin shigar dake jikinta, a ina mijinta ya samo ƴar masu kuɗi? meye alaƙar mijinta da wannan Hajiyar da har hotonsa ya shiga wayarta, to ko ƴar Hajiyar ce suke soyayya da mijinta?
Kafin wannan lokacin bata taɓa sanin wacece Hajiya Ikilima ba, babu wani abu da ya taɓa haɗasu bare ta san cewa a gidansu Hajiyar mijinta Alfa ke koyar da karatu.
Wani sashi na zuciyarta yana ƙoƙarin ƙaryata mata zargin da ya dasu a zuciyar tata amma tana ƙin baiwa sashen muhimmanci, babu wani dalili da zaisa ta kasa gane taswirar mijinta a ko’ina ne, tana jin ko makancewa tayi ta warke ba zata kasa gane fuskar masoyinta a cikin tarin fuskokin da idanun nata zasuyi tozali dasu ba. Babban abinda take tsoro shine kar mijinta yayi gamo da ƳAR MASU KUƊI ta canza masa halaye da ɗabi’unsa, ta sani sarai kuɗi kanyi tasiri matuƙa wajen canza halayen mutum daga masu kyau zuwa marasa kyau, komai zai iya faruwa. Tana da ilimi ta san cewa mijinta ya auri mata uku bayan ita ma ba laifi bane, wacce zai aura ɗin wace iri ce, shin zata yarda tayi rayuwa irin wacce suka fara shimfiɗawa kansu ko kuwa zata zo da wasu sauye-sauye? Wasu irin sauye-sauye ne zata shigo mata dasu? Yaya zata iya haɗa rayuwarta data ƴar masu kuɗi da MIJI ƊAYA?
Nutsuwa ta kasa zuwar mata, girgiza kanta kawai take tamkar sabuwar kamun mahaukaciya, Saleem dake bayanta shima yana addabarta da kukansa na jin ciwo, jijjigashi kawai take tana so ya tsaigata mata da kukan ta samu ta nazarci abunda ke shirin tunkaro su. Ta samu mai adaidaita sahu wanda babu kowa a cikinta ta faɗa masa unguwar da zai kaita, taci sa’a yace ta shiga bayan sun daidaita kuɗin da zata sallameshi. A cikin adaidaitan ta cigaba da tunane-tunanenta har suka iso inda zata sauka, ta fito ta sallame shi sannan ta taka a ƙafa ta nufi gidan kasancewar a kwai ƴar tazara daga bakin titi zuwa gidan nasu.
Da ƙyar ta samu ta danne zuciyarta ta aiwatar da aiyukanta na gida. Wajen la’asar Alfa ya shigo gidan kasancewar yana gari, daga gidan mahaifinsa Mal. Sani ma yake. Tun a yanayin yadda ta amsa masa sallamar yasha jinin jikinsa, sai dai shi abinda zuciyarsa ta hasaso masa yasha bambam da abinda ke faruwa, a tunaninsa jikin ɗan nasa ne har yanzu babu sauƙi shine hakan ya saka mata damuwa, a irin yadda ta ƙwallafa ranta a kan ɗan zata iya shiga kowace irin damuwa in har ɗan zai kasance cikin rashin lafiya.
“Ya ya jikin Saleem ɗin? kun samu ganin likitan kuwa?” ya jefo mata tagwayen tambayoyin. Ba tare da ta maida hankalinta gare shi ba tace, “Jikinsa da sauƙi, mun ga likita, anyi masa gwaje-gwaje ance sanyi ne ya shige shi kuma yana buƙatar kulawar gaggawa dan lamoniya (pneumonia) zata iya kamashi.”
“Ya salam! Kinga illar yawan shan ƙanƙarar dana ke ta faɗa miki ko? Tun kafin cikin yaron nan ya tsufa nake hanaki yin amfani da ƙanƙara amma kika ƙi, to yanzu gashi kinga abinda sakamakon hakan ke shirin haifarwa.”
“An rubuto masa magunguna, likita kuma ya tabbatar min da yana da muhimmanci a siya masa dukka magungunan ayi amfani dasu.”
Hankalinsa bai tashi ba dan da kuɗi a tare dashi, yau ya karɓi albashinsa na koyarwarsa a gidan Alhaji Sa’eed, saboda haka babu ɓata lokaci ya karɓi katin ya nufi wani shagon siyar da magani ya siyo, ya ci sa’a kuwa an samu dukka magungunan sai dai sun ja kuɗi da yawa, amma babu damuwa tunda lafiya ake nema, a kanta kuwa sai inda ƙarfi ya ƙare.
“Umman Saleem ki daure ki saki ranki mana, damuwa ba ita zata saka Saleem ya samu sauƙi ba.”
“Hmmm NAMIJI KENAN!” Ta ayyana hakan a ranta, ita abinda take ji a ranta daban shi kuma inda ya dosa daban. Kamar ta faɗa masa yau taga hotonsa shi da budurwarsa, amma sai ta danne zuciyarta tayi alƙawarin ba zata taɓa faɗa masa abinda ya faru ba da bakinta, sai dai in ya fahimci hakan a gaɓoɓinta ta wajen rashin walwarta da rashin kuzarinta, kuma ko ya nemi yaji dalili zata tafi dashi a yadda ya ɗauka, wato rashin lafiyar Saleem ne ya haifar mata da damuwa.
Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yammaci Ustaz Haruna Alfa ya iso gidan. Kai tsaye cikin gidan ya nufa kamar yadda yake yi a wasu lokutan, suka gaisa da Hajiya Ikilima dake zaune a falon gabanta ɗan ƙaramin teburi ne da aka jera mata kayan marmari take sha. Daidai lokaci Zahra ta shigo falon cikin kwalliyarta mai ɗaukar hankali, tayi kyau sosai tamkar wata sarauniyar kyau ta nahiyar Africa. Cikin murmushi Alfa ya amsa mata sallamar tata a ransa yana yaba kyan da tayi. “ka ƙaraso kenan.” Ta tambaya.
“Allah yayi min isowa.”
“To sannu da zuwa, bari in fito da Faruƙ ɗin ko.” Bata jira yace wani abu ba ta nufi ɗakin Faruƙ ta sameshi a kan wheel chair ɗinsa gabansa da teburi da computer, hannusa riƙe da biro yana rubutu, ga dukkan alamu dai jotting wani darasin yake saboda ƙaratowar lokacin jarabawarsu. “Faruƙ ka ajiye rubutun nan muje muyi karatu Mal. Alfa ya ƙaraso.” Kamar bai ji mai tace ba ya cigaba da rubutunsa, “Magana fa nake yi kana jina.”
“Kuje kuyi karatun kawai, abinda nake yi yana da muhimmanci bazan iya dakatawa ba, kin san mun kusa fara exams.”
Bata son lokacin da wani ɗan ƙaramin tsaki ya suɓuce mata ba wanda Faruƙ ɗin ya ji shi tamkar zubar wuta cikin kunnuwansa har yayi gaggawar karkata kansa ya kalleta. “Wallahi Faruƙ matsalolinka suna da yawa, babu mai iya maka sai Allah.” Ta juya tayi tafiyarta cikin jin haushinsa. Ta samu Alfa a falo ta sanar masa kawai suje suyi karatun su kaɗai Faruƙ ɗin na yin wani abu. Kamar dama haka yake so a yadda yaji a ransa, shi kwata kwata ma yanzu bai fiye jin daɗin karatu da yaron ba, yana kawo musu ƴan matsaltsalu yanzu cikin sha’anin karatun.
Tare suka jera suka fita daga falon cikin wani yanayi kamar MATA DA MIJI. Haj. Ikilima binsu da kallon farin ciki take yi, ba tun yanzu ta fuskanci akwai soyayya a tsakaninsu ba, shiyasa wasu lokutan take shiga ɗakin dake kusa da inda suke zama suyi karatun tayi ta ɗaukarsu hoto ba tare da sun sani ba, sai ta zauna tayi ta nazarin hotunan dan ta tabbatar soyayyar suke ko kuwa? Yanzu dai ta tabbatar, kuma taji daɗin hakan, a ganinta hakan zai kuɓutar da Alhajinta ga bijira ga soyayyarta, gwara can ta ƙarata da Alfan, dama shine daidai ita, kuma taci alwashin zata ƙara zage damtse wajen bada gudunmawarta dan ƙarfafa soyayyar ta hanyar Ustaz Alfa tunda akwai girmamawa a tsakaninsu.
Kamar yadda suka saba bayan kammala karatunsu, sai suka lula wata duniya mai nisan gaske, wata duniya mai cike da tarin farin ciki da aminci ga zukatan da suka ziyarceta, wata duniya mai ɗauke da wasu kyawawan lambuna da ƙoramai masu shatatar da wani irin ruwa mai cike da launi da fatsi-fatsi, wasu abubuwa masu kama da zanen heart na ta shawagi a tsakaninsu. Saƙonni suke aikawa juna daga can ƙarƙashin zukatansu masu bayyana ainahin matsayin da kowannensu ke dashi a cikin duhu da hasken zukatan.
Faruƙ na ɗakinshi damuwa tayi masa yawa, tun bayan fitar Zahra yaji damuwa ta dabaibaye masa zuciya, abinda ya saba ji a duk lokutan da aka samu kaɗaicewa tsakanin ta da Alfa ya ji na sukan zuciyarsa. Ba zai iya jurewa ba, gwara suma yaje ya hana su jin daɗi da farin cikin da jikinsa ya bashi a yanzu suna can suna jiyar da juna.
Ya jefar da biro da takardar hannunsa ya tura wheel chair ɗin tasa ya bar ɗakin, a falon yaci sa’ar samun Hajara tana gyara gurin da Haj. Ikilima ta gama shan kayan marmarinta.
“Yauwa Hajara dan Allah taimaka ki kaini waje gurin karatu.” Cikin girmamawa ta amsa da to, sannan ta ajiye tsumman dake hannunta na goge-goge ta kama hannun kujerar ta turashi.
Kwatsam! Suka ga mutum a kansu, a zahiri hakan baiyi musu daɗi ba, ba ƙaramin ɓata ran Zahra yayi ba, har yanzu ta kasa gane manufar yaron, birkicewar sa tayi yawa, tabbas ta yarda ba iya larurar asperger’s ce kaɗai ke saka shi wannan butsancin ba, abin nashi yayi yawa fiye da sanin da tayiwa halayen masu irin larurar a matsayinta na mai ilimi kan sanin halayyar ɗan adam musamman kuma a ɓangaren cutukan da ke canza halaye da ɗabi’un ɗan Adam. A kwai wani al’amari bayan wannan da ya kamata ace ta fahimta a kansa, tabbas kuma zata sauya shirinta a kansa, zata gudanar da wani bincike na musamman akan waɗannan canje-canje da ake samu daga gare shi a waɗannan lokutan.
Gyaran muryar da Alfa yayi yace, “Akaramakallahu Malam Faruƙ ne ya bayyana?” shine ya dawo da ita daga duniyar tunanin da shula.
“ Na kasa zama ni kaɗai ne a ɗaki shiyasa nace a kawo ni nan muyi karatun tare.” Cewar Faruƙ ɗin.
Sam Zahra bata gamsu da abinda yace ba, tasan ba haka bane a zuciyarsa, amma sai ta bishi a hakan kamar yadda taga Ustaz Alfa ya yi.
*
Misalin ƙarfe goma shaɗaya na daren ranar Zahra na ɗakinta a zaune a tsakiyar gado ta baza littafanta na psycology, wayarta ce a hannunta tana gudanar da bincike kan halaye da ɗabi’un masu ɗauke da cutar asperger’s. dukkan abinda ta tarar ba baƙo bane a gareta ta riga ta sanshi a kan masu ɗauke da larurar. Tayi tsaki ta kashe data connection ɗin wayar ta yasar da ita gefe, hannayenta duka biyu tasa ta dafe kanta dake sara mata. Gashi dai ta ƙara yin bincike kan sababbin wallafe-wallafen da aka yi a kan asperger’s dama sauran larurori masu kama ko alaƙa da ita, irinsu autism duk tayi amma bata ga wani abu mai kama da abubuwan da Faruƙ ke bijiro musu dashi ba. Yanzu kawai abinda ya rage mata shine yin nazari da ƙwaƙwalwarta tare da yin amfani da zahiri da nazarin ayyukansa da kalamansa da ƙwayar idanunsa yadda suke fitar da saƙonnin da zuciyarsa ke ɗauke da su. Waɗannan sune hanyoyi da zata nutsu ta bisu ko zata dace ta gane ina Faruƙ ɗin ya sa gaba!
Wannan kenan!
YOU ARE READING
FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)
Ficção GeralLabari a kan wani mai kuɗi (Alh. Sa'eed) wanda Allah ya wadata shi da komai na jin dadin rayuwa, sai dai abu ɗaya ne ya gagareshi wanda a kan fafutukar neman abun idanunsa suka rufe ya aikata wani al'amari wanda shi ya zama silar ginuwar labarin. A...