BABI NA TARA

36 2 0
                                    

BABI NA TARA
“Yanzu kai Alhaji wacece kake tunanin zata yarda tayi mana wannan aikin? Ka san fa wannan ba ƙaramin al’amari bane da mutum zai kalle shi sassauƙar fuska.” Hajiya Salma kenan take faɗawa Alh. Sa’eed lokacin da suke zaune a falo suna tattaunawa kan maganar. Murmushi yayi har fararen haƙoransa suka bayyana, “In dai akwai kuɗi na tabbata babu abinda zai gagara, zamu fara gwada Bareera mai aikin gidannan mu cusa mata kuɗi sosai sannan mu faɗa mata buƙatarmu, ina ganin tunda kuɗi suke so sosai ba zata ƙi amincewa ba.” Wani irin kallo take masa wanda ke nuna tsantsar rashin amincewarta, “A’a Alhaji, bamu san wacece Bareera ba, bamu san asalinta ba, kawai dai tazo tana yi mana aiki ne, kaga kuwa ba zamuyi gagancin neman ƙwayar halitta daga gareta ba, mu da muke so mu haifi nagartaccen ɗa ta yaya kawai zamu amince da mai aiki?”
“Haba Salma, ke fa zaki raini abin nan a cikinki, jininki zai gauraya da nasa, zai ci ne daga abinda kika ci, abinda kika sha shi zai sha, iskar da kika shaƙa ita zai shaƙa, sannan kuma ke zaki haifeshi ta inda ko wace mace ke haihuwa, ta yaya kike tunanin zai bijira daga kwasar dukkan abubuwan da ƴaƴa ke kwasa daga iyayensu. Ki kwantar da hankalinki Salma, wannan ba wani abu bane da za’a tayar da hankali kansa ba, matuƙar dai Bareera ta amince to falillahil hamdu buƙatar mu ta kusa biya.” “idan kuma bata yarda ba fa baka tunanin zata tona mana asiri?” murmushi yayi, “Za ma ta yarda musamman in taji maganar kuɗin da zan bata… yanzu dai tashi ki kira min ita Bareerar.” Ta miƙe jiki a matuƙar sanyaye taje ta kira Bareera mai aiki.
Bareera ta durƙusa a gabansu kanta a ƙasa cikin nuna tsantsar biyayya. Falon yayi tsit tamkar babu kowa a cikinsa, kowa da abinda ke saƙawa a ransa, daga can dai Alhaji yayi ƙoƙari yayi ƙundunbalar harshe.
“Bareera wani aiki ne muke so kiyi mana wanda indai har kin amince zaki samu maƙudan kuɗaɗe wanda na tabbata kaf cikin danginku zai yi wuya a samu wanda ya taɓa mallakar koda kwatankwacin rabin su a rayuwa.”
Gaban Bareera ya yanke ya faɗi rass, nan da nan kwanyarta ta fara aiki, wane irin aiki ne haka wannan ake so tayi da ake iƙirarin biyanta waɗannan maƙudan kuɗaɗe haka?
“Kinyi shiru ba kice komai ba Bareera.” Haj. Salma ta katse mata dogon tunani da ta fara tafiya a cikinsa. Ba tare da ta iya ɗaga kai ta kalle su ba tace, “Ina jin ku Hajiya, ku faɗi duk irin aikin ni kuma zanyi muku indai zan iya.”
“Za ma ki iya, sai dai idan kin kashe idanunki da basirarki… daga naira miliyan ɗaya zuwa miliyan ashirin zan baki matuƙar zaki yarda ki bamu ƙwan haibuwarki…”
Wata irin zabura Bareera tayi tamkar wacce kunama ta harba ba zato, yayinda nan take gumi ya ƙwace mata, ta shiga mutsu mutsu kamar mai jin bayan fitsari, bata san lokacin da kalamai suka ƙwace mata ba, “ƙwan haihuwa? Na shiga uku ni Bareera, dan Allah ku rufa min asiri wallahi ni ba ƴar iska bace.”
“Ya isa haka Bareera ya isa! Ai ba abun iskanci bane, abu ne wanda za’ayi shi a asibiti cikin abinda bai wuce mintuna biyar ba, ba zafi zaki ji ba ba komai kuma babu wanda zai sani ko ya gane, tamkar yadda ake ɗaukar jini haka za’a ɗaukin abin, kinga in kika yarda cikin mintuna  biyar zakuyi kuɗi ke da danginki…”
Girgiza kai ta dingayi tamkar ƙadangaruwa, bakinta na rawa amma ta kasa furta abinda take so ta furta. “Ki nutsu Bareera ki nutsu ki faɗa mana abinda ke ranki, kar kiji komai, idan kinga ba zaki iya ba babu damuwa ki faɗa mana, idan ma kina buƙatar mu baki lokaci ne kije kiyi tunani zamu baki, amma dai abinda nake so ki saka a ranki shine akwai maƙudan kuɗi suna nan su a jiranki cikin yin aikin mintuna biyar.”
Bareera ce ke kaiwa da kawowa a cikin ɗakin da take kwana a gidan, jira kawai take dare yayi ta sulale ta fece daga gidan, sam zuciyarta bata amince mata da yin wannan aikin ba, yaushe zata kai kanta inda za’a kasheta? Ashe dama haka masu kuɗi suke? Ashe abinda ake faɗa a kansu gaskiya ne da ake cewa masu yi musu hidima basu da wata daraja a idanunsu? Dukkan wasu buƙatunsu maƙasƙanta a kansu suke sauke su? Lallai yau ta gamsu da haka tunda gashi abin yazo kanta, wai yau ita ake cewa ta bada ƙwayar halittar haihuwarta, ko meye ma wata ƙwayar haihuwa? To in ta bada ma me zasuyi da ita? Tsafi? Dama da gaske akwai mutanen da suke yanka mutane kamar yadda ake basu labari suyi tsafi? Yau gata ita ma ta faɗo makamancin gidan ana neman wani sassa na jikinta ayi tsafi dashi, ai kuwa daga yau zamanta yazo ƙarshe a gidan, zata gudu ta koma ƙauyensu su cigaba da rayuwar talaucin da suka saba, gwara ita sau dubu da wannan abin dake shirin tunkarota.
Sai da ta daidaici lokacin da Haj. Salma ta shige ɗakinta yin sallar isha’I ta saɗaɗa ta fice da ƙullin kayanta a maƙale a hammata, ta ci matuƙar sa’a shima mai gadi ya fita masallaci sallar kuma ya bar ƙofar a buɗe, dan haka cikin sauƙi ta samu ta fice daga gidan ta saɓi hanya sai gida.
Sauka lafiya Bareera!!!!!!!
Wayar gari kawai sukayi suka nemi Bareera sama ko ƙasa suka rasa babu ita babu kayanta wanda hakan ke nuna musu ta gudu ne, jikin Haj. Salma yayi matuƙar yin sanyi, ta dubi mijin nata, “Kaga abinda nake faɗa maka ko Alhaji? Na faɗa maka babu wanda zai yarda da wannan al’amarin, duk wanda aka faɗawa haka zai ga kamar hakan cutar da kai ne.” “ki daina faɗar haka Salma, dan Bareera taƙi yarda ba yana nufin zamu kasa samun wanda zai cika mana burinmu ba, hanyoyin kama ɓera yawa garesu kuma duniya da faɗi maye ba zai ci kansa ba, ni san yadda zanyi na nemo mana mafita, kuma zanyi duk yadda danyi dan ganin na cika burina.”
*
Bayan wucewar wasu kwanaki da suka haɗu suka samar da satittika, al’amura da yawa sun faffaru, ciki har da samun nasarar yiwa Haj. Salma DASHE a mahaifarta inda aka yi aikin cikin sa’a da nasara. Tun daga wannan lokaci sai labarin samuwar ciki ga Haj. Salma ya bayyana bayan da aka yi mata ultrasound scaning aka tabbatar dashen da akayi ya zauna ɗam kuma ya fara motsi da juyi kamar yadda sauran hallitun samar da ɗa embryo suke yi a cikin kowace uwa.
Tuni ƴan uwan Haj. Salam suka fara zuwa yi mata sambarka tare da tayata tsananin farin cikin samun wannan cikin da addu’ar Allah yasa mai zama ne. shi kuwa Alhaji Sa’eed ya ɗauki duk wata kulawa ta duniya ya ɗorata kan Haj. Salma, da ta motsa zai zaburo yace, “yaya? Lafiya dai ko? Ina ne yake miki ciwo? Me kike buƙatar a kawo miki?” haka zai saka ta a gaba yayi ta lelenta kamar ita ce jaririyar. Babu abinda take aikatawa yanzu a gidan, musamman ya sa aka nemo masa wasu dattijan mata guda biyu da kuma budurwa ɗaya suka cigaba da kulawa da ita, sannan yaje asibiti ya nemi alfarmar a bashi nurse guda ɗaya da zata dinga zuwa kullum tana duba masa lafiyarta, baya ga scaning da suke zuwa akai-akai dan a tabbatar da zaman ɗan a cikin nata.
Sannu a hankali kwanaki suka shusshula har aka samu wucewar watanni takwas, zuwa wannan lokaci tuni ciki ya tsufa, zama da ƙƴar tashi da dabara. A wannan lokacin ne wata rana da suka je scaning  aka gano wata gagarumar matsala game da ɗan dake cikin nata, wato kamar yadda yake ƙa’idar kowane jinjiri yana kwanciya ne a cikin mahaifiyarsa kansa a ƙasa yana kallon bayan mahaifiyarsa, ƙafafunsa kuma a sama yadda idan lokacin haihuwa yayi kai ne zai fara fita wato (cephalic vertex  presentation) wanda hakan ke faruwa a cikin wata na 32 zuwa na 38. Idan aka samu saɓanin haka shi ake cewa Malpresentation wanda yana iya zama breech, wato ya kasance kan jinjirin a sama ƙafafunsa a ƙasa yadda su zasu fara fita lokacin haihuwa (footling breech), ko kuma kan jinjirin a sama amma mazaunansa su ne tare da ƙafafunsa a ƙasa (complete ko flexed breech),ko kuma ya kasance kan yaro a sama kuma ya miƙe ƙafafunsa sun taɓo har zuwa kansa (frank ko extended breech) ko kuma fuska ta fara bayyana (occiput posterior position). Dukka waɗannan matsaloli ne da ka iya jawo matsaloli gurin haihuwa wanda idan ba’ayi nasarar samun management ɗin da ake yi ba wato ƴan dabaru da ake yi wajen juya ɗa ya koma zuwa daidai yadda ake so ya fito ba ana iya kaiwa ga yiwa mace c-section, wato a yanka mararta a ciro abinda ke ciki. To itama Haj. Salma ta samu matsalar malpresentation ga ɗan dake cikin nata yayinda kafaɗarsa ita ce a ƙasa (shoulder breech/transverse lie), ma’ana ita zata fara yunƙurin fita lokacin haihuwa wanda kuma hakan bazai yiwu ba sai dai ayi aiki a cire ɗan. Hankalin Alh. Sa’eed in yayi dubu ya tashi, ba abinda bakinsa ke ambata face kalmar innalillahi…
“To likita duk me yake jawo waɗannan abubuwan ne?” a ruɗe yake tambayar likitan. Cikin salon kwantar da hankali likita yace, “Ka kwantar da hankalinka Alhaji, lokaci-lokaci akan samu mata da irin waɗannan matsaltsalun wanda yana daga cikin abinda yake da muhimmanci yasa muke umartar mata masu juna biyu da su dinga ziyartar asbiti ana duba musu lafiyarsu data abinda ke cikinsu, da yawan mata sun rasa rayukansu a sanadin makamantan waɗannan matsaloli. Kuma su waɗannan matsalolin ba cuta bace ba kuma larura ba, kawai hakan yana faruwa ne cikin hukuncin ubangiji mai yin yadda yaso, sai dai akan yi wasu ƴan dabaru a likitance wajen ƙoƙarin saita kwanciyar yaron wanda duk da haka akan samu akasi ko yaron ya juya, to kafin lokacin haihuwa sai kaga ya sake komawa yadda yake, wanda ƙarshe sai dai ayi aiki a ciro shi.”
“Yanzu menene mafita Doctor?”
“Mafitar shine zan haɗa ku da likitan mata ɓangaren haihuwa, obstetrician wanda shi zai ƙara fito muku da abin fili da kuma dukkan sauran abinda ya dace.”
“Dan Allah Doctor ka gaggauta haɗa mu dashi, wallahi bana so in rasa matata.” A matuƙar rikice yake magana. “ka kwantar da hankalinka Alhaji, na faɗa maka za’a samu mafita insha Allahu za’a dace, likitan kuma bari in kirashi yanzu sai in baku address ɗinsa kuje ku same shi.” Ya faɗa yana kara wayar tasa a kunne dan kiran likitan.
“Doctor amma baka ganin sakamakon yin wannan dashen ne aka samu wannan matslar?” alhaji ya tambaya cikin rashin hayyaci. Da sauri Doctor ya tareshi, “No, kokaɗan ba haka bane, babu ruwan wancan aikin da wannan matsalar, ita wannan kamar yadda na faɗa maka ana samun mata a lokuta da yawa da irin matsalar wanda kuma ƴaƴan naturally aka same su ba dashe ba, kaga kenan hakan baya nufi sakamakon DASHE aka samu wannan matsalar… hakan yana iya faruwa sakamakon juyin da ɗa ke yi a cikin mahaifiyarsa tun daga lokacin samar dashi yana gudan tsoka zai dinga juyi cikin ruwan mahaifa wanda yana girma damar juyin nashi yana raguwa, to a irin haka ne idan lokacin haihuwa ya kusanto jariri na ƙoƙari saita kansa zuwa hanyar ƙofar mahaifa (birth canal), idan aka samu akasi ya juya ba daidai ba sai ya zauna a yadda yake musamman idan lokacin haihuwa ya kusanto, amma ina mai tabbatar maka wasu matan ma sai ya rage mintoci su haihu ɗan nasu yake juyawa kuma su haifeshi lafiya, saboda haka wannan ba abin ɗaga hankali bane.”
“Shikenan Doctor na gamsu da bayananka, yanzu ka ƙoƙarta ka haɗa mu da likitan.”
“Shi nake kira yanzu.” Cewar likitan.
Likitan ya samu ya haɗa su da obstetrician Dr. Usman Khalid wanda ya zauna ya fayyace musu dukkan abinda suka shafi abnormal fetal lie, wato rashin daidaituwar kwanciyar ɗa a cikin mahaifiyarsa wanda ya ka iya zama longitudinal (a tsaye, kai a ƙasa ko a sama) da kuma transverse (wanda yaro yake a kaikace, kafaɗarsa ta zama ita ce zata fara fita yayin haihuwa), da sauran abubuwan da suka shafi malpresentation (kamar su breech, brow, face da kuma shoulder, (irin matsalar ita Haj. Salman kenan). Ya kuma tabbatar musu akwai ƴan dabaru da ake yi da ka iya taimakawa yaro ya koma kwanciyarsa daidai duk da babu tabbacin kashi ɗari (100% assure) na samun nasarar hakan, amma ana ƙarfafawa mata masu juna biyu gwiwar yin hakan dan yana taimakawa.
Daga ciki a kwai abinda ake cewa ECV (External cephalic verson) wanda ake amfani da hannu wajen juya yaro, kokuma yoga-like poses, yadda mai juna biyu zata dinga motsa jikinta ta hanyar sunkuyo tana dafa gwiwarta sannan ta ɗaga ta banƙare tana tura ƙugunta gaba. Ko kuma hanyar yin amfani da sauti, kasancewar ko wane ɗa yana jin sauti daga cikin mahaifiyarsa, yana jin dukkan abinda take faɗa hakan kuma na iya taimakawa yasa shi ya motsa ya canza kwanciyarsa zuwa daidai idan an dace, ana iya dabarar yin amfani da sautin radiyo ko head phone a kara a cikin yadda abinda ke cikin zai iya jin sautin.
Sai dai dukkan waɗannan dabarun ba wai suna nufi da anyi ake samu nasara ba, a’a, abin dace ne, ana gwadawa ne ko za’a dace. Sai kuma addu’a, a dage da addu’ar neman sauƙi da haihuwa lafiya, babu abinda ya gagari Allah.
Haka suka dawo gida jikinsu a matuƙar sanyaye, iya kuka Haj. Salma ta sha shi, tun Alhajin yana bata haƙuri da rarrashi har ya gaji ya zuba mata idanu.
Anyi ƙoƙarin gwada duk wata dabara da za’ayi dan ganin abinda ke cikin Haj. Salma ya daidaita amma nasara bata samu ba, ƙarshe dole sai dai ayi c-section a cire mata ɗan. Lokacin da aka shiga da ita ɗakin tiyatar tamkar gawa haka a wuce da ita akan gadon asibitin saboda matuƙar wahalar da tasha. Shi kuwa Alhaji kuka sosai yake saboda irin kalaman da ta dinga furtawa masu kama da bankwana kafin a shiga da ita ɗakin tiyatar.
An samu nasarar ciro mata yaro namiji wanda tun daga lokacin aka fuskanci a kwai matsala ta rashin cikar halitta a jikin yaron, har likitocin da sukayi aikin sun fara tunanin ko lokacin haihuwar yaron bai yi ba? Amma kuma da aka duba file ɗinta sai aka ga lokacin haihuwarta yayi, kawai Allah ne yaso yaron yazo a haka da rashin cikar wasu ɓangarori a jikinsa.
A ka cigaba da ƙoƙarin ceto rayuwar Haj. Salma dake fafutukar rayuwarta, sai dai duk yadda likitocin suka so su hanata tafiya lahira Allah ya fisu iko da hakan, kuma ya fisu buƙatar tafiyar tata, saboda haka bayan kamar mintun goma sha biyu da yin aikin ta ce ga-garinku-nan.
Tsayawa kwatanta irin tashin hankalin da Alhaji Sa’eed ya shiga da jin mutuwar Haj. Salma ma ɓata lokaci ne, yanke jiki yayi ya faɗi bai kuma dawo hayyacinsa ba sai bayan kwana biyu, yana farkowa sunan Salma ya dinga kira, babu wanda bai tausaya masa ba, kwata kwata ba ta ɗan nasa yake ba ta Haj. Salma kawai yake. Da ƙyar aka samu ya dangana sannan aka rakashi ƙabarinta yayi mata addu’a sosai yana kuka, sai da aka zo aka janye shi aka maida shi gida sannan ya daina kuka.
Bayan sati biyu aka zo masa da maganar yaron, buɗar bakinsa sai yace, “Me zanyi dashi? Me zanyi da abinda ya zama silar rabani da farin cikina? Da na san cewa sanadin zuwansa duniya zai tafi min da tawa duniyar da ban roƙi Allah ya bani shi ba, da banyi ta fafutuka akan neman samunsa ba, da munyi ta zaman mu babu ɗa, amma yanzu gashi ɗan ya samu amma babu CIKON FARIN CIKI, ku janye min shi dan Allah…” wani abokinsa mai suna Alh. Salisu ne yayi saurin katse shi, “Haba Alhaji Sa’eed kar ka bari shaiɗan ya rinjiyeka kaje kayi saɓo mana, menene amfanin waɗannan maganganun da kake? Haba! Sai kace ba musulmi ba, kamar baka yarda da ƙaddara ba, ko ka manta cewa dukkan mai rai sai ya koma ga mahaliccinsa ta kowane irin sanadi? Yanzu me salma tafi buƙata a gurinka da ya wuce addu’a? ka kyautata mata zaton rahamar Allah da ya nufa ƙarshenta ya zama daga cikin waɗanda kanyi dace da mutuwar shada.” Haka suka cigaba da bashi baki har ya dangana, ya karɓi ɗan nasa yayi masa addu’a yayi masa huɗuba da suna UMAR FARUƘ, sai aka zaɓi a dinga faɗa masa FARUƘ ɗin kasancewar sunan mahaifin marigayiya matarsa Salma. Tun daga nan kuma sai matsanancin son  yaron ya shiga ransa musamman da ya kasance yaron yazo a nakashe, nan ya nemo waɗanda zasu dinga kula dashi, so dai mai tsanani yake wa yaron wanda da yana da iko ko ƙuda bazai bari ya taɓashi ba matuƙar dai zai cuce shi.
Kwanci tashi asarar mai rai, kwanaki masu tsananin gudu suka shuɗe kamar giftawar iska, yawansu ya tattara ya bada makwanni wanda suma suka tattara suka samar da watanni, daga nan kuma sai shekaru. Yau gashi an wayi gari Faruƙ ya shekara bakwai a duniya, abubuwa masu yawa sun faru a cikin waɗannan shekaru, ciki har da gano larurar da Faruƙ ke ɗauke da ita ta Asperger’s baya ga sauran naƙasun da halittun jikinsa ke ɗauke dashi, ƙafufuwansa ba zasu iya taka ƙasa ba saboda tamkar babu ƙashi a jikinsu, sannan kansa a karkace yake, idanunsa sunfi kama da na MAGE, sannan bakinsa baya iya fitar da kalmomin magana yadda suka dace, zuwa lokacin iya kuɗin da Alhaji Sa’eed ya kashe akan neman lafiyar yaron nan sun isa su zama jarin wani matshin mai kuɗin, sun firfita ƙasashe da dama neman lafiya, amma yadda suka je haka suke dawowa, an bashi shawarar ya gwada na gargajiya, shima ya gwada babu nasarar ƙarshe dai ya haƙura ya zubawa sarautar Allah ido.
A daidai lokacin kuma yaga dacewar yayi aure kasancewar tun da salma ta bar duniya bai sake tunanin yin wani aure ba, ta ɗansa kawai yake. A yanzu ne yake ganin ya dace ya nemo wacce zata cigaba da kula masa da gida da kuma mara lafiyar ɗansa. Cikin haka suka haɗu da Haj. Ikilima da tazo masa da lulluɓin kura, bazawara ce irin masu aurar  masu dukiya ɗin nan dan su yashe musu dukiya sannan suyi ta zuba wulaƙanci da rashin mutunci har sai an gaji an sake su. To shi dai Alhaji Sa’eed san hali ba bai san cewa kara da kiyashi zai ɗaukawa kansa ba, shi dai kawai yaga mace cikin hijabi yayi tunanin ta Allah ce ya ɗebe ta ya kaita gidansa wanda ko cikakken sati ba tayi ba ta fara nuna hali tun a kan Faruƙ inda tace ita ba kula da nakasasshe tazo ba. Alh. Sa’eed yasha mamakinta matuƙa, ashe haka take? Shiyasa yake ji tunda ya rasa Salma baya jin akwai wacce zata  maye gurbinta. Haka nan ya cigaba da zama da ita da halinta yana lallaɓawa har kawo wannan rayuwa da suke ciki ta yanzu….                                                                                                          
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Alhaji Sa’eed ya sauke bayan ƙwaƴwalwarsa ta gama tunano masa wasu al’amura da suka faru suka shuɗe, wannan tunanin da yayi sai yaji babu abinda yake buƙatar gani face wata yarinya da wani al’amari ya shiga tsakaninsu, ko a ina zai ganta? Ko tana nan a raye? Idan tana nan a raye yasan yanzu ta girma, shekaru ashirin da biyu ai ba wasa bane, ya tabbatar in dai tana nan a raye zuwa yanzu tayi aure, tabbas  zai so ya ganta, zai so ya ganta ya nuna mata wani gagarumin al’amari. Zai so ya ganta dan ya nemi yafiyarta, zai so ya ganta dan bayyanar wasu abubuwa masu yawan gaske…

FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)Where stories live. Discover now