BABI NA UKU

42 4 0
                                    

      

BABI NA UKU

“Abban Saleem! Akwai abinda yake damunka wanda kake ɓoye min, wannan yanayin baƙo ne a gareka, ka daure ka faɗa min abinda yake damunka.”

Idanu ya zuba mata ba tare da ya iya tankawa ba, shi kan shi mamakin kan shi yake, tananin mace? Tabbas lamarin baƙo ne gare shi.

Tunda ya dawo gida ya kasa aiwatar da ayyukan da ya saba, tunaninta ya cika masa kwanya, idan ya rufe ido zanen fuskarta ne ke shawagi a allon idanun nasa.

Ya kasa fahimtar me hakan ke nufi, bai taɓa yin soyayya ba, ko ita mai ɗakin nasa ba soyayya ce ta haɗa su ba, shi yasa ya kasa gane zuciyarshi ta kamu da tsananin sonta lokaci guda.

Mikewa Habiba tayi daga inda take zaune ta dawo kusa dashi ta zauna, hannunta tasa ta dafa kafaɗar shi,

“Abban Saleem…”

“Maman Saleem! Ki kwantar da hankalinki babu abinda ke damuna illa wani baƙon al’amari da naci karo dashi a yau, kiyi haƙuri ba wani abu nake ɓoye miki ba.”

Ya miƙe tsaye yana kai dubansa ga agogon dake manne a bango,

“Lokacin karatu ya kusa, bari nayi azama saboda yau muna da babban baƙo na mussaman, Ustaz Ahmad Yashi ne zai ziyarce mu yau, ya kamata in hanzarta.”

Kallo ta bishi da shi har ya isa bakin ƙofa, da ƙyar cikin nauyin harshe ta iya cewa “A dawo lafiya.”

Ya amsa “Ameen.” Tare da ɗorawa da cewa, “Yauma kuna buƙatar tsiren ne ko kuwa.” “A’a, ka dai tahowa da Saleem pampers.”

Bayan fitar sa zama tayi kan kujera ta shiga nazari.
  
  WANENE USTAZ ALFA?

Ainahin sunansa HARUNA, Asalinsu mutanen Katsina ne, neman ilimi ya kawo mahaifinsa Kano wanda kafin nan ya zaga garuruwa da yawa dan neman ilimi, a wani zama da yayi a garin Damaturu Malaminsa ya bashi auren ƴarsa mai suna Binta.

Binta ruwa biyu ce, mahaifiyarta bafulatana ce mahaifinta kuma bahaushe ne, tana da kyau daidai gwargwado ga kuma ilimi data samu a gurin mahaifinta, sun zauna da mai gidanta Mal. Sani lafiya cikin kulawa da kyautatawa juna har Allah ya albarkace su da haihuwar Haruna.

Haihuwar Haruna babu daɗewa Allah ya karɓi Alaramma Yakubu wanda hakan yayi dalilin tashin Mal. Sani daga Damaturu suka nufo kano wajen wani Babban malami wanda yake abokin Alaramma Yakubu.

Binta tasha kukan rabuwa da danginta musamman yadda take da ɗanyen goyo kuma haihuwar fari, da farko mahaifiyarta taso tirjewa amma sai wan mahaifin Bintan ya tsawatar yace koda Alaramma na raye bazai hana Sani tafiya da matarsa ba.

Dole suka dangana, ta tattara komatsanta suka nufo kano inda sani yayi musu alƙawari  idan ya samu  matsugunni zai zo ya taho da ƴan uwanta suga gidan.

Bayan dawowarsu kano suka cigaba da gudanar da rayuwarsu, Mal. Sani ya samu gida wanda ya siya da kuɗinsa da aka saida gonar gadonsu aka basu kuɗin, sannan ya zuba jarin siyo dabbobi da sayar dasu a kasuwa.

Bayan Binta ta yaye Haruna ta kuma samun wani cikin, daya isa haihuwa ta haifi ɗiyarta mace Hadiza, bayan Hadiza aka haifi Faisal wanda daga kanshi haihuwa ta tsayawa Binta.

FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)Where stories live. Discover now