BABI NA BAKWAI

28 2 2
                                    

BABI NA BAKWAI


Sannu a hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, al'amura suka cigaba da faruwa har aka samu ƙarin watanni huɗu akan takwas ɗin da suka gabata, wato Zahra ta cika shekara ɗaya kenan cif a gidan Alhaji Sa'eed.

Zuwa yanzu Zahra da Alfa sun gama yardarwa kansu suna son juna daga dukkan zuciyoyinsu, an kai jallin da kowannensu kan shiga cikin matsananciyar damuwa a duk lokacin da suka nesanta da juna.

Sosai Zahra tayi na'am da soyayyar Alfa saboda ya cika dukkan wasu sharuɗa da zuciyarta ta daɗe da gindaya mata a kan dukkan wanda taso ta aura.

Sai a yanzu take jin lallai a baya ta tauye kanta da zuciyarta tauwewa mai tsanani da ta hanawa kanta yin soyayya saboda wani ƙunsasshen ƙudiri dake ƙasan zuciyar tata.

Sarai ta sani yana da mata, amma hakan kokaɗan bai ɗaga mata hankali ba tunda tana da ilimi da wayewar rayuwar wannan zamanin, ko wace mace da halinta take zama a gidan mijinta saboda haka koda Allah ya ƙaddara aurenta da Ustaz Alfa zata shiga gidansa da salama, zata ɗora rayuwarta a kan tubalin da taje ta tarar.

Tsakaninsa da Matarsa Habiba kuwa lamarin bai dagule musu ba, Habiba tayi amfani da iliminta wajen haskawa zuciyarta rashin ribar da zata tsinta a kan wannan al'amari idan ta tashi hankalinta.

Sun zauna dashi sun fuskanci juna tare da cirewa zuciyoyinsu zargi kan ko wace gaɓa da zuciyarsu zata iya ɗorawa a kai.

Ta bashi dama yaje yayi soyayyarsa idan Allah ya ƙaddara aurensu ma ba zata ɗaga hankalinta ba.

Ya sanar mata ko wacece Zahra a gidan Alhaji Sa'eed da irin matsayinta name kula masa da ɗansa, babu wata alaƙa ta jini a tsakaninsu.

Abinda ya ɗaga mata hankali ya sa mata fargaba da tsoro duk a lokaci ɗaya shine, bata ji ya bata labarin asalin wacece Zahran ba, iyayenta da danginta, ina ta baro iyayen nata tazo gidan wani mai kuɗi tana wani aiki har na tsawon shekara ba tare da wata rana ta ziyarci gidan su ba ko ita wani yazo wajenta.

Ta tuntunɓe shi da wannan maganar, hakan kuma ya sanyaya masa jiki ainun, bai fahimci wace irin toshewar ƙwaƙwalwa bace ta rufe masa idanu ya kasa ganin hakan, ya kasa yin nazari kan hakan.

Tabbas Habiba tayi hasashe mai kyau wanda yake da buƙatar a bashi muhimmanci a bincika.

Sai dai ta wace hanya zai tunkari Zahra da wannan magana? Yaya makomar soyayyarsu zata kasance bayan hakan?

Ya sani akwai babbar matsala da tarin ƙalubale a gabansa a duk lokacin da yayi nufin kai zancensu wajen manya, idan aka tambayeshi suwaye iyayenta wace amsa zai bayar?

Bincike a cikin neman aure wata gaɓa ce mai matuƙar girma ta ƙarfin tasirin da yake tsaida turakun aure su tsaya cak yadda babu wani tarnaƙi ko ƙalubale da zaiyi barazanar turesu.

Ko namiji ne zaiyi aure a kwai tawaya mai girma gareshi idan aka samu naƙasun asalinsa balle kuma mace, macen ma ba ƙaramar matashiyar budurwa ba, mace wacce shekarun girma suka fara cimmata kamar Zahra.

A ƙiyasinsa Zahra zai tayi shekaru talatin da biyar zuwa da shida haka, kenan idan aka ƙididdige shi kansa bai fi shekaru biyu zuwa uku ya bata ba. Idan kuma aka kwatantata da matarsa Habiba zata girmewa Habibar da shekaru masu yawa, dan sai bana ma Habibar take cika shekaru Ashirin da biyar.

To yaya za'ayi wannan kwaɗon rayuwar?

*

Washegari wata ƴar Yayar mahaifiyar Zahra wacce suke kira Anty Ramlatu ta kawo mata ziyara.

Anty Ramlatu ta girmewa Habiba a shekaru dan ita yanzu haka ma ƴaƴanta uku tana goyon na huɗun, macece mai ilimi da wayewar wannan zamanin, bata da rikincin biyewa ruɗanin zamani tana amfani da iliminta a duk gaɓar da amfaninsa ya tashi.

Koda Habiba ta bata labarin abinda ke faruwa ta jinjina lamarin ƙwarai, ta kuma tausaya mata sosai amma bata ɗora ta a karkatarciyar hanya ba.

Ta nusassheta ƙwarai kan lamarin da ruyawar yanzu ta dawo, ta kuma bata shawarwarin irin yadda zata riƙe mijinta gam ta yadda ko mata uku zai auro mata nan gaba ba zata ji ɗar ba.

Sai dai Habiba bata shigo musu da zance rashin sanin ainahin iyayen Zahran ba, a ganinta wannan sirrinsu ne na cikin gida, ita mace ce, shi kuma namiji ne, yadda yaje ya rakitota ya san yadda zai ƙwacin kansa gaban Mal. Sani a lokacin da aka titsiye shi da tuhuma.

*

Alhaji Sa'eed ne a kishingiɗe kan lallausar kujerar dake cikin falon ɗakinsa, wayarsa ce a hannunsa yana duba labaran BBC HAUSA, inda aka ɗora labarin wata mata da ƴaƴanta ƴan mata guda uku da suke cikin ƙuncin rayuwa har ta kaisu ga fita yin aikatau a gidan masu kuɗi. su kuma masu kuɗin suna amfani da rashin imaninsu suna neman yaran har dukkansu suka ɗauki juna biyu, babbar cikinsu ma a gwajin da aka yi mata an samu tana ɗauke da ƙwayar cuta mai karya garkuwa jiki.

Su kuma waɗanda suka aikata musu hakan sun biya alƙalai cin hanci an kokkori ƙarar da wasu lauyoyi suka shige musu gaba dan ƙwato musu haƙƙinsu.

Wannan labarin ba ƙaramin girgiza hankalin mutane yayi ba musamman yadda suka dinga zubo fustataccen martani akan wasu marasa tsoron Allah da kanyi amfani da damar da Allah ya basu ta dukiya wajen cimma buƙatunsu a kan maƙasƙantan mutane.

Nan wasu suka dinga kawo labarai makamantan waɗannan da suka faffaru a baya amma rashin samun hanyar da labaran zasu watsu a duniya yasa laifuffukan suka dinga bin shanun sarki.


Wani labari da Alhaji Sa'eed ya ci karo dashi cikin labaran da ake turo ya matuƙar tayar masa da hankali, ya ɗauki ƙwaƙwalwarsa kacokan ya maida ita baya, wasu shekaru da suka gabata, kamar a faifan majigi haka al'amuran da suka faru cikin rayuwarsa suka cigaba da bayana a kwalbar idanunsa tiryan-tiryan kamar ana karanta labarai a gidan radio.




Muntasir Shehu
08164243585

FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1)Where stories live. Discover now