JINNA MATAR ALJAN LTTAFI NA 2 episodes 1
A birnin MISRA ASHEKARA (2589,BCE)
lokacin milkin su SlNEFARU baban KHUFU
Dasu KHAFRE da JIDETHRI alokacin da aka kirkiri gunkin sphinx anyi wata bokanya mai suna zarishat bokanya zarishat ta kasance babbar shedaniya itace shugabar dukkan aljanun birnin misra itace ke juya su, ta kasnce kuma mai son kanta da zalunci domin akan haka ta taso. Ta Dade tana shirin taga ta sami dama tayi juyin milki a birnin misra ta haye kan milkin birnin misra amma aboye tun lokacin milkin sinefaru lokacin da Khufu na lokacin samarta suke tare da bokanya zarishat atakaice masoyane sunso yin aure amma cika burinta na kwatar milkin birnin misra tasa ta ki amincewa tun lokacin. ayanzu dai bokanya zarishat ta amince zata auri kufa bayan ta gamayin shirinta na kwatar milkin kasar aboye, batare da kowa ya saniba face amintattun bayinta, alokacin da akasanar da bikin daurin auren khufa da zarishat a birnin misra garin kowa murna da farin cikin don sunsan girman soyayyar da sukewa juna tun ta yarinta ce ta juya ta zama ta gaske awannan lokacin ne sarki yabada umarni agina masa Giza pyramid don aciki zasu tare tare da abar kaunarsa bokanya zarishat awannan ginin pyramid din bokanya zarishat ba karamin bada gudun mawa tai ba don kusan ma zance ita ta Gina ita da tawagar Aljanun ta ..sai da aka,shafe shekara ashirin sannan aka kammala ginin Giza pyramid ashekara ta (2566 BCE) Kamar wasa yau ne daurin aure gari ko,ina ya dauka makida nayi masu shaye shaye nayi antaru acikin wani babbar alkarya yara da manya ana,cikin nishadi da taya sarki murnar angwancewa da masoyiyarshi an daura aure kamar yadda al,adar birnin take Khufu da gimbiya kuma bokanya zarishat suna zaune bisa kan karagar miki na alfarma kana ganinsu kaga empress da emperor awannan lokacin wata kuyanga mai suna asla tazo gefem sarauniya bokanya zarishat ta rishina tace ya shugabata lokaci yayi daza,a nuna miki cikin gidan sarauta da wajensa duk da kinsan komai amma al,adar gidance haka dole sai kin zagaya ko ina da ina kafin waduwar rana sarauniya kuma bokanya zarishat murmushi tayi don dama wannan yana daga cikin tsarin ta saboda lokacin da zasu tafi zuwa ganin gidan zata tafine da dakarun aljanun gidan sarauta da yawa saboda tsaranta sannan kuma al,adar gidan ce itama lokacin da suka futa don zagaya gidan awannan lokacin ne dakarun sumame jinshin aljanu suka sami damar shiga gidan tare da buya suna jiran lokacin futowa yayi su futo awannan lokacin sarki Khufu yana zaune bisa kan karagar milkinsa yana ta murmushin jindadi yau zai kebe da abar begensa bokanya zarishat a dai dai wannan lokacin ne wani Aljani mai suna mankas shine babban hadimin bokanya zarishat ya bayyana acikin fadar ya nufi wajen Khufu Sanin kowa ya sanshine yasa ba ai masa shamaki ba saida yaje gabda Khufu sannan ya rissina ya mika gaisuwa sannan ya tashi yaje gabda Khufu saitun kun,nan sa yace ya shugabana kamin halacci da nima dole na sakama da halacci kasani cewa matarka bokanya zarishat ta aureka ne kawai don ta kashe ka ta haye kan karagar milkin ka Khufu ya juyo zai magana sai mankas yace koyaya kayi wani mummunan mots zaka iya mutuwa kuma inka mutu zamu shiga halin tashin hankali babba. bari dai na Nuna ma kaga abunda nake nufi. Dan taba hannin Khufu yayi ahankali ahankali Khufu sai ya fara ganin samudawan aljanu duk ko ina acikin gidan sarautar ko ina hatta cikin turakarsa aljani mankas ne yace ya shugabana nasan kanada dakarun,yaki wayanda zasu iya kawar da wayan nan dakarun aljanun to amma kasani wa'yan nan su duk ba,acikin hankulan su suke ba duk ta juyar musu da hankali kayi duba da hankali kaga wai duk akanka za ai wannan barnar idan kuma kace zaka yaketa to mu dakai da ita duk zamu halaka don ta dau alkawarin indai bata sami nasaraba to zata kawar da kowa na kabilar mu adoran kasa kuma kalma daya zata fada hakan ta tabbata duk mu nutse karkashin kasa damu da ita mu nutse kasan wannan gini mai daraja na Giza pyramid kasani ita bokanya zarishat ruwa buyuce wato mutum kuma aljana tana da karfin shihirinda tana juya duk wani aljani babban burinta yanzu shine ta kasheka da makamin da aka fara kerawa aduniya wanda ta dade da samun makamin wata jar wukace maidauke da hatimin wani turarran Jan dutse indai ta kasheka da ita ta ta sadaukar da jininka wa shugaban shaidanu sannan ta kwanta da shugaban shaidanu na birnin dairatul shetan to kamar anbude ko fofin mashifune zuwa duniyar mune don alokacin ne zata cika cikakkiyar matsatsuba to hakan na faruwa zata Tara dukkan mutanan birnin misra tasa ayankasu atara jinin su a bawa shedanu Dan ta jawo hankalinsu wajen hada hannu su kawar da jinshin yan Adam gaba daya adoran kasa sai dai asami ruwa biyu aljan kuma mutum to kaji babban burinta ya shugabana. iya tashin hankali ya bayyana acikin fuskar Khufu amma ba Wanda ya fuskanta Dan kasance,warsa shima matsasubine yadau lokaci maitsayi yana tunani amma bai tuna komai ba juyowa yay yace yakai aljani mankas wacce hanya kake gani zamu iya bi Dan ceto rahiwar mutanan birnin misra aljani mankas yaja dogon nunfashi sannan yace hanya dayace zamu iya bi hanyar itace lokacin da kuka kwanta kaida bokanya zarishat zata gusarma da hankali sannan ta dauko wukar'nan wacce aka fara kerawa aduniya ta cakama da zarar ta cakama wani Jan haske zai ringa futa ta cikin wannan Jan dutsen dake jikin wukar yana shiga jikin ta a wannan lokacin ne zamusami damar cin mata domin indai hasken ya fara ratsata take duk wani kuzari dake jikin ta zai dai na aiki har sai hasken ya gama shiga jikin ta mu kuma kafin wannan hasken ya gama ratsata zamu cin mata mu kamata mu nannadeta da sihir,taccen tsin,ma sannan musata acikin akwakin makara sannan murufe to da zarar munyi haka bata yadda zatai ta tsira dole a nan ruhinta zai cigaban da rahiwa kodajin wannan batu sai Khufu yace to nifa shikke,nan na mutu kenan? ya shugabana kasani cewa gan,gar jikinka ce kawai zata mutu ba kyai ba kasani cewa ruhinka bazai mutuba zamu tafi dashi birnin ruhanai dake saman duniyar nan ta mu sihirtaccen garine Wanda jinshin aljanun farko suka Gina shi da tsaro mai tsauri, tsaran kwa shine wata bakar guguwa ce awajen kuma duk wanda yabi hanyar zai ringa ganin abun mamaki da dama kuma da zarar kayi magana akan abun to abun zai rikide ya koma bakar guguwa guguwar nan bazata barko tsinke ba face ya mutu irin abunda aljanun sukai kenan suma bakar guguwa ta batar dasu ayan zu dai inaga banda ni bawan da yasan taswirar birnin ruhanai a doron kasa to a can garin zamu rayu dani da ruhinka da sauran jama,ar aljanu domin mubar mutane muma mukoma wa mazaunin mu. ya shugabana a halin yanzu bokanya zarishat na gabda dawowa karka manta da tsarin mu zamu tai makeka kamar yadda kazama adalin shugaba awajen mu sai anjima take aljani mankasa ya rissuna sannan ya tashi ya tafi duk da cewa hankalin Khufu ya tashi amma yana farin cikin cewa ko ba komai dalilinsa ba za,a shafe kabilar'su a doran kasa ba a shirye yake da ya sadaukar da kansa domin jama,arsa yana cikin wannan haline sarauniya bokanya zarishat ta dawo tare da makida masu kirari nayi masu waka nayi tsabar matsatsuba ce duk inda ta sa kafa ta cire sai kaga fure mai launi2 yana futowa tare da futar da,wani sanyayyan kanshi mai sa nishadi koda sarauniya kuma bokanya zarishat ta karaso wajen Khufu sai ta risina sannan ta tako har zuwa kusa dashi cikin rangwada tana wani fari da ido harta karaso kusa dashi tana me cewa ya Rabin raina murmushin me kake? yi kaga fuskar ka kamar gonar auduga tsabar haske da sheki murmushi yay kawa yana mai cewa a zuciyar sa dakinsan yadda nakeji da tsanarki da bakin,cikin wannan lafazin naki da ba zakice haka,ba . basu dau wani lokaci ba sai sarauniya bokanya zarishat tace Rabin raina kazo mu tafi turaka na gaji da yawa kuma na kagu najini na kwanta acikin faffadan kirjinka mai ni,ima wanda na dade ina jiran ranar da zai zama mallakina murmushi Khufu yay sannan ya kamo hannunta yana mai cewa abunda sarauniya tace shi za,ai haka dai suka shiga cikin ginin Giza pyramid duk inda suka bi bayi da kuyangi ne suke zubewa suna kawo gaisuwa koda suka karasa shiga turakar da aka,tanadar musu anriga an garata tana fudda wani kanshin dadi an baza wasu fure launin jajaye akan gadon kai dakin ya futa kai tun azamanin da mutanan misira suna da kwakwal wa wajen kirkira. tun kafin sukarasa gado sarauniya kuma bokanya zarishat ta fare cire kayanta tana tawowa kusa da Khufu bata karaso ba har saida ta gama cire suturar jikin ta tai tumbur sannan ta zo dai dai Khufu ta kama hannun sa ta zaunar dashi akan wannan tattausan gadon tana me shafa goshinsa awannan lokacin ne wani Abu daga jikin hannunta ya futo ya shiga cikin goshin Khufu take ya rasa tunanin shi awannan lokacin ne sarauniya kuma bokanya zarishat ta kwatar da Khufu ta ciremai rigar jikinsa sannan ta dauko wukar'nan wacce aka fara kerawa a duniya tare da hawa kan cikinsa tana mai karanto wasu dalaziman tsafi Wanda bamsan me take cewa ba daga karshe ta cakawa Khufu wukar take wata irin kara ta fara futowa daga sassan cikin ginin Giza pyramid hankalin mutane ya tashi daga masu gudu sai masu suma kai wannan karar ma ta zubarwa damasu tsowon ciki cikinsu a wannan lokacin ne wannan wukar ta fara futar da wani Jan haske ta jikin Jan dutsen sihirin koda ya fara shiga jikin. Sarauniya kuma bokanya zarishat sai ta fara wata irin rawa da,ka da kirjinta tan wata irin siririyar kara kamar mace ta shide a dai dai wannan lokacin ne aljani mankas da tawagar sa suka bayyana tsulum acikin turakar Khufu suka kama sarauniya kuma bokanya zarishat suka daureta da sihirtaccen tsumma kafin ta gama komawa dai dai sannan suka sata acikin sihirtacce akwakin gawa awannan lokacin ne aljani mankas ya dauko wata irin kwalba ya tattaro wannan Jan hasken ya Tara aciki sannan ya rufe sannan ya cire wukar da aka fara kerawa a duniya daga cikin kirjin Khufu itama aka nannadeta da sihirtaccen tsun'ma sannan aljani mankas yabada umarni da a dauki bokanya zarishat zuwa karkashin kasan Giza a binne ta ta yadda ba Wanda zai kara tuna ta a doran kasa ..Mutuwar Khufu ta tayarwa da mutanan birnin misra hankali sunshiga halin damuwa bayan angama biking mutuwar Khufu aka Nada sabon sarki Wanda ya kasance jinin Khufu ne domin Dan kanwar,sa ne uwa daya uba daya bayan gama bikin mutuwar aljani mankas ya hada jama,ar aljanunsa suka bar birnin misra bari na har,abada suntafi tare da kwalbar da ruhin Khufu yake ciki saida sukai tafiya shekara daya a hanya, shunsha wuya da ba kadan ba kafin su sami shiga birnin ruhanai kaidar grain ne duk Wanda ya fara sa kafarsa acikin sa to shine zai milki ya zama sarki hakance ta fara da aljani mankas don shine ya fara shiga birnin koda aljani mankas ya shiga sayya dauki sihirtacciyar wukar nan ya yanki han nunsa take jini yai tsattuwa daga jikin hannunta nasa,wajen sihir,tacciyar kofar birnin yaje yasa yankakken hannu ya fara rubuta kamar haka BIRNIN KHUFU yana fadar wasu dalashiman tsafi bayan wani Dan lokaci sai ya dubi mutanan aljanun yace dasu daga yau shine sarkinsu kuma daga yau basu ba duniyar mutane domin na rife kofar shigowa da ta fita kuma bazata taba budewa ba saida jinina kona tsatstsona WANNAN SHINE ABUNDA YA FARU A SHEKARAR(2566,BCE) JINNAH MATAR ALJAN KASHI NA BIYU EPISODES1
YOU ARE READING
jinah matar aljan book2 ep1
FantasyThis story Its fantasy story abaut Devils who want destroy a wold