SHI NE MIJINA part 1

48 3 2
                                    

Wallahi Wallahi wallahi!!! Sai kin auri SALEEM ko da kuwa Zaki mutu Sai kin auresa, Shashasha kawai dabba Mara hankali wacce Bata San inda yake Mata ciwo ba. Mtswwww! Ya juya ya fita abinsa.
SALMA ta juyo gun Mami tace don Allah don son Annabi mami ki yiwa Abba magana don wallahi bana son Yaya Saleem domin kuwa Ba Shi bane mijina Yaya SAlMAN SHINE MIJINA Tana kuka Tana magana, ta ci gaba da cewa Mami don girman Allah ki taimakeni ki cice reyuwata Dan Allah.... Mami ta katseta cikin tsawa ke! Bari kiji abinda zan gaya Miki wallahi ko da kin mutu Sai ankai gawarki gidan Saleem. Mami ta tureta daga rikon da Salma tayi Mata sannan ta wuce cikin dakinta Rai a6ace.
SALMA ta dafe kanta da takeji kamar zai tsage taci gaba da kuka Mai ratsa zuciyar duk Mai sauraro, numfashinta na fita da sauri da sauri  zuciyarta kuwa kamar zai fito daga cikin jikinta.
Zainab Yar aikin gidan ta shigo domin kaiwa Mami sakon da ta aiketa Subhanallahi! SALMA! Ai Bata San sanda ta watsar da abinda ke hannunta ba ta karaso inda Salma take tace Salma lafiya kike kuwa? Meya sameki? Ina su Abba? Salma kiyi magana manah!
Salma wacce ta Fara fita daga haiyacinta ta dago kanta Tana kallon zainab tace Anti zainab Dan Allah ki taimakeni wallahi mutuwa zanyi, ta dafe kirjinta tasa ihu wayyo Allah kirjina Anti zainab zan mutu ki taimakeni wayyo kirjina!!! Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Ta yanke jiki tafadi sumanmiyya.
Zainab iyakacin firgita ta firgita Bata San sanda ta rungumeta ba. Kuka take na fitar hankali Dan Allah Salma ki tashi, ya kike son SAlMAN yayi da rayuwarsa idan bakya duniya eyeh! Ki tashi dan Allah. Mamiiiii! Abbaaa!

SHEKARU ASHIRIN DA BIYAR BAYA
ASALINSU MAMI ( SA'ADATU)
Mutane garin Takai ne karamar hukuma ce dake cikin birnin Kano, galibin jama'ar Takai Fulani ne da Hausawa Farare da bakake.
Kasuwar Takai Tana ci ne ranar talata. Don Haka kamar kowacce talatar  Sa'adatu Tana Nan bakin kasuwa Tana siyar da nononta Wanda kowa yake kokarin yaga yasiya agunta sabida nata Mai kyau ne ba tsirki, shiyasa daga ta fita zai kare duk da ba da wuri take zuwa ba Amma zata siyar, Arana Tana siyar da nono sau uku, yau ma kamar kullum Tana zaune a inda ta Saba zama.
Yan'mata nawa ne kindirmonki Yana da tsada kuwa?
Ta dago ta kalleshi sannan ta Mai da kanta kasa cikin kunya tace cikin muryarta na fulanin  Wanda hausa bai Gama zama bakinta ba tace shin ka taba ganin kindirmona yayi tsada?
Daya daga cikin su fulanin tace sa'ade wannan mutun din Nan shine yake zuwa duk ranan kasuwa Yana siyan kindirmonki Kuma duk zuwansa da zaiyi Sai yace Miki kindirmonki Yana da tsada kuwa? Toh ai shi nufinsa anan shine kindirmonki Yana da arha kuwa, koke Baki ganewa ne.
Sa'ade tayi murmushi sannan tace au wallahi shab! Na manta Dan Allah kayi hakuri na nawa zan baka?
Yayi murmushi Shima yace nawa ne dukka?
Tace Sai dai na auna sabida na Dan siyar, sannan ta shiga aunawa har ta gama tace na dari takwas ne. Ya yarba sannan ya Bata kudinta ya hau kekensa ya wuce.

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now