SHI NE MIJINA PART 5

14 2 2
                                    

  CI GABAN LABARI
 
Dr khaleel Yana zaune a office dinsa, Dr Salman ya shigo cikin rashin kuzari bude  kofar Dr khaleel Yana kallon shi, gaba daya ya zube yayi duhu  Idanuwansa manya masu sheki sun zurma ciki, hakan bai Hana shi bayyana kyakkwansa ba.
  Ya zauna agefen Dr khaleel cikin bakaken ( leather seats) din da sukayi wa office din kawanya.
Kafin Salman ya furta wani abu, Dr khaleel ya katse shi da cewa.. meya faru? Meya same ka? Meya zabgar da Kai Haka? Salma ce damuwarka Koh? Gaya min maza, wannan ba Dr Salman din da muka sani bane?
Duk Yana Masa wannan tambayar ne acikin tashin hankali da damuwa.
    Ya dago ya kalli Dr khaleel idanuwanshi da suka kada sun koma jajir cike taf, da kwalla wadda babu Alamun za'a Bata damar zubowa saboda dauriya irin ta namiji da rashin son nuna karaya.
Cikin rawar murya yace a'a ba laifin Salma bane, hasalima su Umma ne, Nan ya fadawa  Dr khaleel halin da suke ciki shi da Salma, daga karshe Kuma yace wallahi shi da Salma sun kasa sanin meye dalilin iyayensu nakin aura masu junansu da Kuma meye takamemmen gabarsu!
Dr khaleel zai yi magana kenan wata nurse ta shigo da gudu tace doctors an kawo wata yarinya Emergency ne domin tayi doguwar Suma, numfashinta ba daidai yake ba: Dr khaleel najin Haka yace to kiyi maza kije kusa Mata oxygen tare da Bata taimakon duk da ya dace, kafin mukaraso kinji?
Tace okay sir, sannan ta sake fita da gudu.
  Dr khaleel ya kalli Dr Salman yace tashi muje Koh?
Dr Salman yace a'a wallahi bazan iya komai ba ayanzu Haka ka tafi kawai, ni Kam gida nayi domin na samu na Dan huta.

Da sauri Dr khaleel ya dauki wayarsa Yana Kiran Dr Salman anyi sa'a wayar Salman Tana kunne, ya sanyata acaji nesa da shi kadan, Yana kwance gefen gadonshi.
  Sarai yaji kararrawar Amma bai yi niyyar budewa ba, Sai Kuma ga Kiran waya dole ya Mike zuwa gareta, ga mamakinsa Kiran Dr khaleel ne da sauri ya amsa wayar.
Dr khaleel yace Dan Allah Dr Salman duk inda kake kayi sauri kazo Asibiti ( hospital) please make show you come, wallahi it's Emergency.
  Cikin rashin kuzari ya tashi ya dauki key din motarsa da wayoyinsa ya duba agogon wayarsa yaga is about to 11:00pm na dare, ya fi minti uku Yana tunanin wani irin Emergency ne wannan da khaleel ya Kira sa haka! Ya kunnan motar ahankali ya Fara yin reverse.
Dr Salman yayi horn maigadi ya bude mishi Yana barka da zuwa, amsawa kawai yayi sannan ya faka motarsa agefen cikin rumfar Adana motoci ( park lord) ya fito ya doshi cikin hospital, dai-dai da fitowar Dr khaleel daga office dinsa yace Salman thank God ka samu isowa da wuri zo muje ka gani.
Dr khaleel Yana gaba Dr Salman na binshi abaya  har dakin Aminity na female ward din inda yarinyar ke kwance.
  Da sauri Dr Salman ya karasa gaban yarinyar ya Kama hannunta, wannan lokacin kuka ne sosai ya kwace Masa da ya fahimci halin da salmarsa take ciki.
  Anti zainab ta matso kusa da Salma, don ganin kamar ta bude idonta  tace " Salma ga Salman yazo, Ashe a hospital dinsu aka kawo ki, Allah nagode maka da ka sake hada yaran Nan awuri daya.
  Dr khaleel yace anti zainab Ina su Alhaji? Tace ai sun tafi gida Sai Kuma gobe in Allah yakaimu lfy.
Yace to don Allah Zaki iya......ba.....Rin....su....Salman.... Su biyu su kwana Anan? Domin su Dan fahimce junansu.
  Anti zainab tayi shiru, tafi minti Arba'in Tana tunani, kafin tace bakomai Allah dai ya shige Mana gaba, to bara naje cikin masallacin da ke cikin hospital na kwanta domin wallahi na gaji sosai, tayi musu sallama ta wuce abinta.
Salman ya dubi Dr khaleel yace meyasa baka kirani tun da wuri ba? Dr khaleel yayi murmushi yace Amma baka da hankali Koh? Ta Yaya zan kiraka lokacin da iyayenta suke Nan ai ni nayi ma hamdala da ka tafi Basu zo sun ganka anan ba.
Kai kaji abinda su Alhaji ke fada kuwa? Dazun da anti zainab ke Masa magiya akan su ceci rayuwar Salma, su barta ta aure Wanda take so!
Hmmmm! Cewa yayi wallahi ko zata mutu wallahi Sai dai ta mutu Amma ba abinda ya damesa Kuma wallahi aure da Saleem babu fashi Sai anyi shi da izinin Allah kuwa, sannan Kuma yace duk ranan da anti zainab tasa ke yin Masa magana akan lamarin Salma to wallahi abakin aikinta.
  Wajajen 11:30pm Dr khaleel yayi musu sallama tare da fatan Alkairi.
Salman ya tashi ya dawo kusa da Salma Shima ya kwanta akusa da ita, wato akan gadon Asibitin domin ita kadai ce a dakin.
   Yace wifey Kinga yadda kaddara(fate) tazo Mana ko lokaci daya! Salma ta juya tare da rungumeshi tace husby, bansan me su Mami ke nufi da mu ba, Nan ta shiga gayamasa duk abinda yafaru har lokacin da ta Suma.
   Shima ya fadamata yadda sukayi shi da Ummansa yace wallahi Nima na kasa sanin abinda ya kawo gabarsu lokaci daya Haka,
  A manne suka da juna kamar tare aka haliccesu, Salma tace Yaya SAlMAN, Ina son nayi maka wata kyauta Wanda ba kowa bane yake iya samunsa Sai Wanda Allah ya nufeshi da samun kyautar.
   Salman yace "wow" wannan wata irin kyauta ce haka?
   A narke ta dube shi, hakan ya Bata damar fadar abinda ke cikin ranta, ta sake mannewa ajikinsa, sannan tace....


Dan Allah ku rinka comment  sabida yin comment dinku ne zai sa na samu karfin cigaba da kawo muku w wannan novel din

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now