SHI NE MIJINA PART 3

13 1 1
                                    

Tayi kasa da kanta cikin Jin kunya tace to bakomai Allah ya shige Mana gaba."Ameen"

WATA Biyar cur! Iyaye sun hadu sun tattauna yadda za'ayi hidimar bikin, kafin a kammala shirye shirye, yayin da cikin wata na shida komai ya kankama aka kammala da komai, iyayen sa'adatu suka mallaka Masa sa'adatu a matsayin matarsa ta sunna.
To Sai dai muce Allah yaba da zaman lafiya "Allahumma Ameen".
Da daddare aka raka sa'a gidan mijinta, gayyar mutane sosai 'yan Kai Amarya, sun Fara zama a Takai kafin ya samu aikin zama cikeken alkali a high court na cikin garin maitama Abuja, Wanda ayanzu suke da zama a kwarinpa Estate.
SUDAIS da Sa'adatu cinye junansu ne kawai Basu Yi ba, sabida so da kauna, a shekararsu daya da aure ta haifi salihu.
Bata Kara haihuwa ba, har Sai da salihu ya shekara shida kafin Allah ya Basu Salma, daga Nan haihuwa ta dauke Mata dif!

WAYE SALMAN SULTAN DAURA!
Salman sultan Dan asalin garin daura ne, mahaifiyarsa SARATU( umma) mahaifinsa kuwa cikeken Dan siyasa ne, Yana zaune da iyalensa Anna kwarinpa Estate Shima Kuma gate din gidansa Yana kallon gate din gidansu salma, da baban Salma da baban Salman Abokaine sosai, domin ko lokacin da baban Salman ya zo kwarinpa a gidansu salma ya Fara zama kafin har Allah ya hure Masa nasa na kansa, yaransa uku, Aisha itace babba tayi aure a Kano, Sai Habeeba ita ma tayi aure a jigawa, Sai Kuma Salman Wanda aka haifeshi Rana daya da salma. Dakkansu suna da hadin Kai da fahimtar juna.
Sannan in ba ka sani ba Kai da kake waje bazaka iya tantance Dan gidan Alhaji sudais da na Alhaji sultan ba, sabida hadin kansu . Salman da Salma sun taso da so da kaunar junansu, tamkar uwa daya uba daya. Shiyasa Alhaji sudais ya dauki duk wani nauyi na karatun Salman har izuwa Fara aikinsa, don ya kula irinsa daya da Salma wato wajen son karatu.
SAlMAN wankar tarwada ne mai matsakaicin jiki, dai dai gwargwadon tsayi Yana da sexy-eyes gasu Farare ne tas! Yana da Kyawawan gashin gira da na ido Wanda suke bakake, Yana da Karan hanci Sai Dan madaidaicin bakinsa gashi da dumpul, gashin kansa kuwa abin gwanin ban sha'awa gashi ne kamar na larawaba. He looks take away and he so muah!( 😏 Karfa kuce na fola Masa😁) .
SALMA kuwa farace kyakkyawa Mai kyan diri da kyatuwar halitta, Bata da jiki sosai, hakan ya Sanya Kyawawan halittun fuskarta dacewa da madaidaicin jikinta me kyan diri, yawan tsafta da son gayu irin na Salma ne ke Kara burge mutane da ita, Amma abin daya fi komai burgewa da ban sha'awa agareta shi ne hakuri da son Addini, Tana da ilimin zamani da na Addini Bata yi aure ba Sai da ta mallaki kwalin masters, Amma duk da Haka tafi karfi a bangaren addini, alokaci daya suka Gama makaranta da Salman sun gama suna da shekarunsu kwaya ASHIRIN da BIYAR jal a duniya.
Wanda sun Sha gwagwarmayar a lokacin da suke school, domin a lokacin iyayensu suna gaba da juna shine har ya shafi rayuwar ya'yansu, Wanda sabida tsananin gaba har ta Kai suna gayawa junansu bakaken maganganu Wanda bai kamata suna wa junansu Haka ba, Kuma sun raba so da kaunar da ke tsakanin Salman da salma.
Lokacin da suke secondary school Abban Salman ya cire Salman daga school din ya Mai da shi wata school, sabida baya son suci gaba da soyayya.
Haka ma take agun Abban salma, watau Shima dai ya cire Salma daga school din ya kaita wata. Wanda Basu San cewa duk school daya suka sake kai yaran ba.
Salma ta Sha fada akan Salman domin ita ta tsanin wata tace Tana sonsa ko Kuma ta yabashi to Sai ta tsayar da yarinya ko waye ubanta kuwa, Sai tayi Mata kashedi idan Kuma takiji to tasan abinda zai biyo baya, watau Sai sun kwashe Yan kallo Aranan.
Haka ma take awajen Salman irin yanda Salma take Yi Shima Haka take, idan ma yaga ka cika kallonta da yawa zai zo har inda kake ya tsokale maka Ido, yace me kake gani? Ire iren abubuwan Nan sunsha faruwa har magana yaje kunnan iyayensu.
Lokacin da suka shiga jami'a Salman da Salma suka kuwa ci sa'ar cin wannan jarabawan suka samu damar zuwa jami'ar A Abuja University.
Salman Yana bangaren likitoci ( doctor)
Ita Kuma Salma bangaren girke girke don acewarta tafi son ta iya girki sabida ta rinka yiwa abin kaunarta salman, domin ita aganinta iya girki ne kawai zai sa namiji yakara sonki ,Kuma namiji ba zai so Yana cin abincin waje ba, in ba naki ba.( Wannan haka yake Salma gaskiya kinyi tunani Mai kyau, Amma yanzu yan'matanmu na zamani ba ruwansu da wannan tunanin su dai kawai suyi karatu su samu aikin yi domin su kece raini acikin jama'a ba don su samu ladar aure ba, hmmm Allah yasa dai mudace Ameen). Don ita ko lokacin da take karama Tana shiga kitchen ta Taya Anti zainab da maminta aikin abinci, shiyasa ta taso da son iya abinci da Kuma kwalliya ( hattara dai iyaye masu korar ya'yansu idan sun shigo kitchen yayin da ake dafa abinci to wallahi wannan ba gata bane ba Kuma tarbiya bane don Haka ku tasa kyayar yaranku aduk lokacin da zaku shiga kitchen ku koya musu kala kalar girki iya gwargwadon iyawar ku)
Salma Tana son ta ga ta iya sana'ar hanu, don ita aikin gwamnati baya gabanta Sam!
Sun gama digiri dinsu ba tare da sun San cewa a makaranta daya suke ba, har Sai da suka dawo gida.

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now