SHI NE MIJINA PART 4

12 1 0
                                    

Watau Kai dai Salman har Abadan bara kaji maganar mu ba Koh? Sau nawa zamuce ka fita harkar Yar gidan Alhaji sudais ne Eyeh?
Umma ta shiga cikin dakin Alhaji sultan, ta zauna akusa da shi sannan tace Alhaji dama ka daina Bata lokacin ka akan wannan yaron domin shi dai Allah yayi shi mara Jin tsoron iyayensa.
  Ta juyo Tana huci, ta kasa saisaita fushinta ta kasa 6oye Anger din da ta taso Mata, don Haka kallonsa kawai tayi ba tare da tace Masa komai ba.
  Ta dago idanunta jajir ta dube shi, cikin kakkausar murya tace " SAlMAN".
    A firgice ya dubeta sabida shi dai a tsawon rayuwarsa bai ta6a Jin ko  da kuskure ta ambaci sunansa na Ainihi ba, Sai dai tace Masa Hassan sabida ranan da aka haifesu shi da salma, Sai ake kiransu yan'biyu watau  Hassan da usaina, Sai ki ranar da taje park ta Kama shi da babban laifi, watau ganinsa da Salma suna was apark, bayan Kuma sunsan da an raba su, fargaba Bata barshi ya amsa ba.
   Taci gaba da cewa, " duk abinda kuke ciki Kai da salma mun sani, tunda bamuyi Kama da wa'anda basuje makaranta ba, Amma muna son Jin sahihiyar amsa daga Bakinka Tunda Allah ya Hana hukunci akan zargi".
   Ya girgiza Mata Kai Alamar Yana sauraronta kafin ta jefo Masa tambartata da ta shafe taraddadinsa !
     Wacece yarinyar da kake satar hanya ku fita tare? 
Ba tare da nuku-nuku ba Kai tsaye yace," SALMA Sudais!"
  Ta sake cewa Amma meye condition din da na baka?
Yayi shiru bai ce da ita komai ba.
Umma ta girgiza Kai" Kai tsaye abinda zan iya cewa shine, ban Amince ba! Me ka gani Ajikin wannan yarinyar, Salman ban da son zubar Mana da kima da mutunci? Ta fid da manyan idanunta.
  Salman tun daga kansa har yatsar kafarsa gumi yake, duk da ssanyi Split dake neman daskarar da mutanen dakin. Tun da ta Fara magana bai ce Mata komai ba, Haka da ta dire Tana sauraron Jin ta bakinsa Amma ya Gaza ce mata komai.
Ta nuna shi da Dan alinta cikin matsanancin fushi taci gaba da magana," idan kana son zaman lafiya da mu,to ka bar maganar salma, idan fa har  ni na haifeka nayi nakudarka bayan daukarka cikin mahaifata har tsawon watanni Tara cikin halin kaka- nikayi.
Ba ta Yi isar da zan hada jini da ita ba, wannan kawai itace maganarmu, idan kaki Kuma kada kaga laifinmu akan duk abinda ya biyo baya. In ba haka ba wallahi zaka sha mamaki, kana iya tafiya wannan kenan.
    Cikin rashin kuzari Salman ya tashi ya nufi dakinsa Yana zuwa ya kwanta akan gadonsa ya Lula duniyar tunani, iyakar hangensa bai ga hujjarsu Umma kwakkwara guda ta haramta Masa abinda yake so ba, zuciyarsa ga salma! Wanda yake da yakinin an halicci zuciyarsa ne tare da sonta, kowanne bugunta Kuma ke tafiya tare da kaunarta
   Don Haka hakikatan baima San takamaman inda son Salma yake ba specifically azuciyarsa, balle yasa wuka ya yanko matashi, tunda ya mamaye zuciyar duka, Sai dai su Umma su tsigeta gaba daya( zuciyar) daga shi har ita kowa ya huta.
Bayan kaduwa da tsorata, Yana cikin mamakin Ashe halin mutum Yana canzawa Haka farat daya daga Mai kirki da sanin ciwon Kai zuwa Mara kirki da tunani?
       To idan ma yaje gun Salma yace Mata ya fasa auran? A me zata dauke shi? Fiye da wannan ma, Yaya rayuwa zata kasance idan babu Salma a cikinta? Menene hujjarsu na cewa lallai Sai ya rabu da SALMA.
   Shi fa ba wai so kawai yake yiwa Salma ba, har da son ya tallafi rayuwarta ya ingantata, idan har bai aure ta ba wani ne can da bai San darajarta ba bai San mutuncinta ba zai aure ta.
A yadda mazan yanzu suka mayar da aure kamar Sanya Riga da tube ta. Bai yi aunin ba Sai ji yayi wani ruwa Mai zafi Yana fita daga idonsa, da yakai hannun ya sharesu, wasu ne suka Kara shimfidowa aguje, wannan karon bai Yi wata yunkurin sharesu ba Haka ya kyalesu, suka you ta shatata, ko don bakomai zasu rage Masa suyar da kirjinsa keyi.

    A gida ko office cikin Yan kwanakin Nan Salman ya Gama fita daga haiyacinsa ya rufe wayoyinsa ya kasa aiki a office, gashi ya kasa fadawa Salma halin da yake ciki.

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now