SHI NE MIJI NA PART 6

9 1 0
                                    

Tace na...ba...ka...kyautar...Budurcina. daga yanzu har zuwa ranar da za'a Aurar da ni.
   Ba shakka hankalin Salman ya tashi, domin komai ya kasa cewa da ita tsananin tausayinta ya Gama karyar Masa da zuciya.
  Salman ahankali ya dubi Salma ki saurari abinda nake son ince da ke, shiru na Dan lokaci, Wanda Salma ta samu yin shirun kenan acikinsa, yaci gaba.
"Zan so na Amince da bukatarki, Amma kiyi hakuri ba zan iya ba, domin ko babu komai ke kamar kanwata ce, ba zan so wani ya cutar da ke ba, balle Kuma ace an waye gari ace nine na cutar da ke, gaskiya bazan iya karbar kyautar ki a wannan lokacin ba, muyi hakuri kawai har Allah yayi Mana sakamakon Alkhairi kinji Koh?"
  Ya sake mannewa da jikinsa.
  " Haba salmata, kiyi hakuri wallahi bazan iya abinda kikace ba, haka dai yayi  ta lallashi Yana jijjiga ta tamkar karamar yarinya, har ya samu ta gamsu da abinda yake ce mata".
Ta Dan gyada Kai Alamar gamsuwa.
   Ahaka har bacci ya daukesu,
Washe gari da safe Dr khaleel yazo tashin Salman, don Kar wani ya gansa adakin, Yana shiga ya tokare hannayenshi jikin kofar dakin Yana kallonsu, suna bacci Rungume da juna Sai kace za'a sace daya daga cikinsu,Dr khaleel yayi murmushi, Aransa yace " ya Allah Ina rokonka da ka nufi Auransu don Albarkacin manzon Rahama" Ameen.
Ya iso gefensu Yana murza kafan Salman ahankali suka tashi.
Yace watau bacci yayi dadi har Kun manta inda kuke Koh?😎 Cikin zolaya yace Salman ya za'ayi na kwantar da patient dinna agado Kai Kuma kazo kana damunta, ko dai ban sani bane nake treating din mutun daya a maimakon mutum biyu, kilanma ba kuyi sallah ba, Salman yace eh wallahi ya tashi suka fice, suna fita Salma ita ma tayi Tata alwalar tayi sallah, Tana idarwa Anti zainab ta shigo tace a'a Salma Anwarware Koh jiki yayi sauki, sabida anga salman😁.
Salma tayi murmushi tace wallahi Anti zainab ji nake kamar Kar naje gida, Salma tayi saurin Kama hannunta suka idasa zama agefen gadon tace don Allah anti zainab wani taimako daya Zaki min? Wanda idan kika  minshi zan tambatar da irin kaunar da kike min. Anti zainab tace to Allah yasa bai fi karfi na ba. Salma tayi murmushi tace inshaa Allahu ma ba zai fi karfinki ba. Anti zainab tace to inajinki👂.
Salma tace Daman abinda na keson ki min shine don Allah anti zainab Kar ki fadawa su Abba cewa na tashi da kaina sannan Kuma Dan Allah Ina son kullum in dinga kwana ni da husby na Dan Allah Anti zainab, ta karasa maganar kamar zatayi kuka😞.
Anti zainab da farko dai taki yarda Amma da Salma ta samata kuka😭, Sai ta yarda sabida Tana Jin Salma tamkar Yar da ta tsuguna ta Haifa.
  Salman na gudu akan titi zuciyarsa kamar takarda don haske, yaushe rabon da ya samu farin ciki irin wannan har ya manta.
Ba yadda Salman ya iya don tsananin farin cikin da yake ciki yafi gaban biro ya rubuta, Haka kuma take agun ita Salma.
    Salman Wanda ke cikin farin cikin da Umma Bata taba ganinsa cikin kwatankwacinsa ba, ya katse tunanin ta da cewa.
  " Umma Ina kwana, ya aiki, ya gida Kuma?"
Umma ta sake Baki Tana kallon sa tama kasa amsawa domin rabon da yayi Mata irin wannan gaisuwar har ta manta.
    Ya karaso kusa da ita tare da Rungumeta yace " come on" mom ki dai na mamaki Salman dinki ne, ba wani ba kinji Koh.
Tace Ina kaje jiya daddare naji karar motarka?  Yace wallahi Dr khaleel ne ya kirani wai ankawo emergency to shine fa natafi acan ma na kwana.
Tayi ajiyar zuciya tace to da sauki koh? Yace eh Alhamdulillah, sannan ya wuce dakinsa domin idan bai wuce ba to tabbas Sai ta kure shi har Sai ta gano mu sabbabin farin cikin sa na yau din Nan.
  Satin Salma daya a Asibiti aka sallamota, Wanda duk wannan kwankin tare da Salman sukayi shi, Ranar da za'a sallamota da daddare tasa Masa kuka tace husby Rabuwarmu Tana damuna, Amma ka sani ba itace babbar abinda yafi damuna ba, kamar idan na tuno da tarin yawan kwanakin da zamuyi ba muga juna ba, husby ban Saba kwanciya ni kadai ba tun da nazo Asibitin Nan ta Kara rushewa da wani sabon kuka.
  Can wani Dan lokaci Salman ya Fara lallashinta " haba wifey dama Abu Ashe baya wucewa awurinki ai ni abinda na dauka tun dazu kin manta da duk wani Abu da ya faru".
Da Zaki taimaka min Dan Allah da kinyi shiru, ya sake manneta da jikinsa, da kyar ya samu tayi shiru.
" Tace to shikenan husby nagode".
Kina nufin kin hakura? Abukace ya tambayeta, ta sake gyada Masa Kai Alamar amsa.
"Yauwa". Ya fada cikin murna " wallahi don Haka nake Kara sonki." Ya Fara juyi da ita cikin kirjinsa, Jim kadan ya Dan janyeta daga gareshi ta hanyar rabata da jikin NASA, bayan ya saurara suka fuskanci juna ta hanyar kurawa junannasu idanu.
Daga bisani yayi murmushi dubi har kin Rame, lallai na yarda ba karamar Azaftarwa kika yiwa wannan Ruhin naki ba, kin ma ci abinci kuwa? Ta sunkuyar da kanta kasa.
" Ba shakka nasan Baki ci abinci ba". Ta Dan taso da kanta ta dubeshi
"Naci Mana".
To in kinci tashi ki zubo min nawa?
Ta Dan karyar da wuya Tana murmushi "Eye? Naka? Ai duka na hada na cinye".
Har yanzu wasa suke da hannayen juna.
Suka kyalkaya da dariya har bacci ya kwashe su.

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now