SHI NE MIJI NA PART 11

9 1 0
                                    

Saleem na shiga cikin dakin ya Fara kuka tare da su maganganu masu Kama da sambatu.
Sai da yayi ma'inshinsa sannan ya tashi ya nufi toilet yayi Alwala yazo yayi sallah yayi Addu'oinsa sannan ya hau gado tare da dauko rigar Salma Wanda ta cire da safe ya rungumeta ajikinsa sannan yayi bacci.
       Abba yace sa'adatu kiyi hakuri nasan nayi Miki laifi da ban fadamiki zancen Auren Nan da wuri ba, nayi hakane sabida ban son Salma taji.
   Kinsan Allah Wallahi ko Khadija da Saleem Basu sani ba daga ni da Alhaji Basheer Sai Kuma Ali drive kawai muka sani, shima abinda yasa Ali ya sani sabida muna cikin mota mukayi maganar Kuma muka haneshi da fadawa kowa, Amma Dan Allah idan Ranki ya bace kiyi hakuri ki yafemin kinji Koh? Sa'adatu sa'ar Mata.
      Tayi murmushi tace bakomai Alhaji fatana dai Allah ya Basu zaman lafiya da zuri'a masu albarka.
Yace Allahumma Ameen sa'a, Allah yayi Miki albarka sannan ya Rungume Yar Abinsa Akirji har bacci yayi Awon gaba da su.
                       To shima dai Alhaji Basheer bai Sha wuya ba wurin fadawa matarsa Khadija, itama ta gamsu da abinda mijinta da Kuma yayanta sukayi, itama fatanan ta bai wuce Allah Subhanahu wata'Ala ya Basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Ita ko Neena idan tace tayi bacci Daren yau ita kanta ta San karya ne, sabida Azabar ciwon Kai, ga Radadin ciwo ga tunani, fargaba da damuwa.
  Ya har yanzu Yaya Saleem bai dawo ba, bare ta fadamasa abin da ke Ranta da Kuma zuciyarta game da shi.
            Washe gari misalin karfe shida da Rabi suka Isa kofar gidan yai ta yin horn, har Sai da Yan gidan suka fito, baba Bala ya bude musu gate, suka shiga ko karasa gun parking lot bai yi ba yayi parking. Ya fito sannan ya dauko ta Ahannunsa sabida ba zata iya tafiya da kanta ba, Kai tsaye ya nufi kofar da zai sadasu Reception din gidan, bai ce wa kowa komai ba, har ya shiga ya kwantar da ita akan ( leather seats) din da suka yiwa falon kawanya.
Duk Yan gidan sun taru afalon domin Jin "meya faru, Kuma A Ena suka kwana"?
    Har yanzu bai ce komai ba.
Mami tace meya samu 'yata? Mekayi Mata? Eyeh!
  Anti zainab kuwa ba tasan lokacin da ta zabga Masa Mari ba, tace ba da Kai Ake magana ba? Eyeh! Meya sameta! Ba zakayi wa mutane magana bane?
Saleem ma ya harzuka zai Masa magana kenan... Abba yai sauri katse shi da cewa.... "Salman dana! Meya faru? Meya sameku, menene salman? Gaya min maza.
         Wannan ba salman din da na sani bane".  Cikin Ruwan sanyi Abba ke tambayarsa, ba kamar su Mami ba.
       Salman ya durkushe Akasa Yana kuka sannan cikin Rawar murya da sarkewar harshe yace..
     Abba...kuyi...hakuri ba laifi na bane wallahi tallahi sherin zuciya ce da Kuma shedan, Dan Allah Abba kuyi hakuri..... Ai bai Eda maganar ba ya Kara Jin wata saukar Mari, wannan lokacin ma Anti zainab ce tana huci tace wallahi salman ka bani kunya da Kuma mamaki.
Yanzu Kai da kanka kayi wa salma Haka.. kuka ce ta kubce Mata.
           Ita ma Salma in Banda kuka ba abinda takeyi.
Mami, Saleem, Ali, baba Bala da Kuma Abba duk sun rasa bakin magana, Anti zainab ta sake yo kansa da duka, Amma Abba yayi saurin katseta ta hanyar daka Mata tsawa " zainab"!
Tsawar nan da yayi Sai da kowa na falon yayi saurin dago kansa domin sun mugun tsorata da Jin hakan.
      Sun fi minti goma ba Wanda yayi magana, domin kowa jira yake yaji wani irin hukunci Abba zai yanke.
        Can Abba yayi gyaran murya sannan yace duk naji abinda kace Amma Ina son ka sani duk abinda ya faru wallahi ba  laifinka bane, laifin wannan Shashashar yarinyar Nan ce, ni yanzu bazance komai ba, illa Saleem ya zabi decision dinsa Akanta, in yaga zai it's Aurenta Ahaka to falillahihamdu inko ba zai iya ba to wallahi duk daya Aguna.
  Daman can bashi yace Yana so ba, ni da ubansa mukayi shisshigin hada su Aure, don Haka yanzu zabi ya rage ga me shiga Rijiya! Saleem Kai muke sauraro domin bazan maka dole ba, don duk daya na daukeka tamkar salihu yarda bazan Masa dole ba Haka Kai ma, Kuma idan baka min biyayya ba wallahi tallahi bazan ga laifinka ba sabida wacce na Haifa ma Bata iya min biyayya ba, bare Kai Wanda kake dan yar'uwata, Kar kaji komai Dan girman Allah Saleem ka fadi duk abinda ke zuciyarka please Kar ka cutar da kanka wajan ganin ka faranta min Rai.
                   Saleem yayi ajiyar zuciya yace Abba! Mami! Farko dai zan Fara godewa Allah da ya Albarkaceni da samun iyaye kamar ku, duk da cewa baku bane kuka haifeni Amma na godewa Allah da ya dasa muku Sona da kaunata acikin zukatarku nagode sosai, Kai ma Abba nagode sosai da wannan damar da ka bani thanks, Amma kusani Wallahi tallahi Ina son Auta har cikin Raina, ko wani fitar numfashina wallahi da sunanta yake fita, Ina son Salma Dan Allah ba don abinda ta mallaka nake sonta ba, Kuma na Shirya na Amince adaura Mana Aure da ita Ayau din Nan.
          Na Fara son Auta tun ran da na Fara ganinta Sai dai ban fadawa kowa ba, har Sai da nazo shekaran jiya nake fada Mata cewa Ina sonta Kuma da Aure, Amma tace min ita Tana da Wanda take so. Bayan Kuma Ummi ta fadamin duk halin da ake ciki, hakan ne ma ya Kara karfafamin zuciyata akan na Aureta in tallafi Rayuwarta Kuma in cike Mata sauran gurbin da Salman ya rage.
     Ya juyo gun Salma wacce har yanzu Bata daina kuka ba. Yace Auta! Don Allah ba don ni ba, ki Amince ki Soni Kuma ki kaunace ni, ki daukeni Amatsayin mijinki Kuma uban ya'yanki na har Abadan, kamar yadda kika Shirya yi tare da Salman! Please! Ni ba makiyinki bane masoyinki ne ni please Salma Accept me please!
Bata ce komai ba illa ma kukanta da ya tsananta.
           Abba yace to Saleem munji duk abinda kace Kuma mungode Allah yayi maka Albarka tare da zuri'a dayyiba." Aka Amsa da Ameen ya hayyu ya Qayyun".
Sannan yace kowa yaje ya shirya zuwa gun daurin auren kafin lokaci ya kure, domin yanzu karfe takwas daidai, kafin karfe biyu inshaa Allahu suna Kano.
                       SALMAN Yana shiga gida yayi parking motarsa ya wuce dakinsa. Umma na zaune afalo, bai ma ganta ba zai wuce kenan Umma ta kirashi ya Dan dawo da baya yace na'am Umma.
    Tace baka ganni bane da zaka wuce bama wannan ba shin a Ina ka kwana? Kuma meya sameka afuskarka? Yace Dan Allah Umma don soyayyar da Annabi( Sallallahu Alaihi Wasallam) Umma ki rabu da ni, kuma Dan Allah idan na shiga ciki Dan Allah na hadaki da Allah karki bar kowa yazo inda nake har ke Umma please 🙏🙏, Yana Gama fadin Haka yayi saurin wucewa dakinsa domin bai son Jin abinda zata Kara cewa.
Ta koma ta zauna shuruuu! Damuwa karara afuskarta.
           Yana shiga dakinsa ya sunce ya daura tawul ya sakarwa kanshi shawa Amma zuciyarsa taki yin sanyi, A azabce take matuka da zazzafar soyayya wadda shi kansa bai San ya zai yi ya Amayar da ita, ko ya samu sassauci azuciyarsa,
Cikin bacci yaji Umma na buga Masa kofa. Idanunshi jajir Kuma sunyi mitsi-mitsi  cikin mugun bacci Mai dadi, Sai yayi tsaki kawai ya kwanta Abinshi, har ta gaji ta wuce.
                   Karfe biyu daidai duniya ta sheda daurin auren Dr Salman da Aisha, da Kuma captain Saleem da Salma, hmmm to Sai dai muce Allah ya Basu zaman lafiya Allahumma Ameen.
                Amare sun tare a Gidajen Anqwayensu lafiya, Salma acikin garin kano aka Kai ta, babban gida ne Mai tsarin gaske a unguwar lamido crescent, Wanda ke rufe cikin Ash girgijejen gate. Gidan farin fenti ne da maron colour, kana shigowa cikin gate din gidan mikakkiyar kwalkace wadda zata sadaka da rumfar Adana motoci, idan kayo gaba kadan grass carpet ne Wanda zai Kai ka bakin kofar reception din gidan.
          Acikin reception din matattakalar bene take wadda zata sadaka da falon sama da yake kunshe da dakunan bacci.
   Dakunan bacci hudu ne acikin falon daya na captain Saleem, daya na Salma, daya Kuma na yara idan Allah ya Basu, Sai na karshe Wanda idan sukayi Baki zasu sauka adakin.
Sai baskwatan ( boys quarter) Nan Kuma masu aikace aikacen gidan ne suke cikinsa.
                  Aisha kuwa ankaita Nasarawa G.R.A itama kusan gidanta daya ne da na salma, A yanayin tsarinsu. Kwanan Aisha hudu ba tare da ta ga ko kyayar Salman ba.
Shi ko Yana can gidansu adakinshi duk ya fita daga haiyacinsa, da kyar Umma ta sama yau ya fito har yayi wanka Kuma ya yarda yau zai je nassarawa gun Amaryarsa.

    Salma ta Sha fada tare da nasihohi da Kuma nusar da ita manufar hadata Auren da akai da Saleem, sannan aka rufe da doguwar Addu'oin tare da Sanya musu Albarka. Sai kusan karfe goma Saleem ya dawo ya Sami Anti zainab ( domin Salma ta Hana ta komawa gida) Tana faman Rarrashinta wacce bai San dalilin kukan nata ba, nan dai shi ma ya zauna asanyaye ya kasa fadin komai, don gaba daya neman kalmar da zai furta yayi ya rasa.
           Washe garin bayan idar da sallah, wanka da Karin kumallo, Salma na falo anti zainab nayi Mata kitso , Saleem ya shigo tun daga bakin kofar anti zainab ta Fara tsokanarshi." Angon Salma kasha kamshi to azo abiyani kudin kitso". Yana Daman dariya yace " anti zainab ai yau abinda yafi biya ma zanyi making, Amma Sai kin kammala tukuna".
    Ya karaso ya zauna Yana kallon kitson yace " shi Kuma wannan ya sunanshi? Anti zainab ce ta bashi amsa " Calabar kenan". Ya sake yin dariya yace " lallai kam, ga Calabar Nan". Ya kalli salma, Ranki ya Dade, Amarya zuwa anjima ni Kuma Sai kiyi min cross river Koh? Shi da anti zainab suka kyalkyale da dariya, ita Kam Salma harara ta jefa Masa.
       Ya Mike Yana fadin Amma ba yau Zaki koma bako? Tace " yanzu ma kuwa inshaa Allahu, na barka da Amaryarka. Ya kalli agogo, Dan Allah anti zainab ki bani minti Ashirin zuwa talatin yanzu zan dawo.
Anti zainab tace Dan Allah Saleem karka dorawa kanka wata dawainiya ni ba bakuwa bace ko kafin ta rufe bakin tuni har ya Kai bakin kofa. Ya juyo Yana kallon Salma yace please Dan Allah karki barta ta tafi har Sai na dawo.
              Bayan ya dawo ne ya Bata kayan da ya siyo Mata kunyar abin yaba Anti zainab, don hidimar tayi yawa.
Yana kwance adakinshi yayi rigingine Allah ne kadai ya San abinda yake tunani, Salma ce ta turo kofar dakin ta shigo ba Bata lokaci tace " anti zainab ta Gama shiri zata tafi".
Ya cire hannunshi daga goshinshi ya Mike tsaf Yana kallonta. Yanayin fuskarta ya Isa ya isar ma da sakon zuciyarta, da gani ba tambaya tafiyar anti zainab ne ya Ruguza Mata lissafi, ya zuba Mata idanu kawai Yana kallonta.
   Ba walwala a fuskarta tace " na Bata sakonka tace ta gode sosai. Sai a wannan lokacin ne suka kalli juna ido cikin Ido, Amma tayi saurin dauke fuskarta. Duk da Haka ya fahimci ta Sha kuka sosai, don har a wannan lokacin bai yi magana ba, Sai ajiyar zuciya kawai takeyi.
         Ta juya zata koma gun anti zainab, taji Saleem ya Kira sunanta" Salma"! Ta tsaya kawai ba tare da ta dawo baya ba, ya karasa inda take tsaye ya tsaya abayanta daf da ita, " Salma ... Salma Dan Allah ka saki Rayuwarki na gaya Miki aduk lokacin da kika bukaci ganinsu Mami wallahi zamuje ki gansu inshaa Allahu, so ki daina tayar da hankalinki Dan Allah".
H

awaye ne masu zafi suka sauko Mata bisa kunci da sauri yasa hannu ya share Mata su tas! Yace in har Ina kusa da ke salma to wallahi bazan taba barin hawayanki su zuba akasa ba inshaa Allahu, sannan cikin wani irin salo Mai cike da dabara ya nemi hada jikinshi da nata da runguma.
Amma Ina, tuni ta gane shi ba Bata lokaci ta janye jikinta kawai ta fice daga dakin, ta barshi tsaye ya ma rasa abin yi.
   Karfe biyu da minti goma Saleem yasa drive yakai anti zainab gida suka bar kanon dabo  suka dauki hanyar Abuja, duk da dauriyan da Salma ta soyi akan Kar tayi kuka, Amma Ina Sai da tayi, shi kansa Saleem Sai da idanunshi suka canza kala, sabida tausayin ta. Har dare Salma Bata sauko ba,duk da cewa ta hakura ta daina zub da hawayen, fuskanta Kam har awannan lokacin ba sauki, Tana yin sallar isha'i ta shige toilet tayi wankanta sannan tayi kwanciyarta.
   Ko da Saleem ya bita dakin, bai ga fuska ba, bare ya nemi wani bayani, yayi zaune bakin gadon, ya saka wannan ya saka wancan.
Daga can ta juyo ta wurga Mai harara, ba shiri ya tashi ya koma dakinshi ya Bata wuri.
                      Aisha Tana zaune afalo Tana kuka. Salman yace ke! Malama kiyi wa mutane shiru ko bake kika CE kinji kin gani Zaki aureni Haka ba? Eyeh! To don me Zaki zo yanzu kina damun mutane da kuka, idan wai kina Yi ne don na tausaya Miki ko Kuma na Fara sonki to wallahi kinyi karya Kuma kinyi kuskure, adalci daya zan iya Miki shine, duk abinda kikeso na game da Jin dadin Rayuwarki zan Miki shi, Amma ki cire duk wata dangartaka  ta da ke Amatsayin Mata da miji.
Kuma daga yau ko amafarki kika shiga dakina Wallahi tallahi kiyi kuka da kanki domin ko ni bansan irin abinda zan Miki ba, ki zauna kawai a idan Allah da Kuma iyayenki suka ajiyeki,  Kuma daidai da Rana daya kika sake kaki shiga sabgata wallahi tallahi kiyi kuka da kanki, kiyi Rayuwarki nayi Rayuwata kinji na fada Miki, Kuma ko gaisuwarki bana bukata  ke! ganinki ko magana da ke ma bana bukata Dan girman Allah na hadaki da Allah please please please Kar ki shiga harkata please 🙏, kinji Koh? Ta girgiza Masa kai Alamar Eh.
Cikin tsawa yace ba da ke nake magana ba? Baki da Baki ne?
Cikin sauri tare da wasu hawaye masu matukar zafi tace naji Kuma inshaa Allah zan kiyaye Allah ya huci zuciyarka.  Yayi tsaki sannan ya tashi ya barta anan Tana cin gaba da kuka, yayi dakinsa.

Hmmmmm😳😳 mu dai ci gaba da zuwa koya kuka ce masoyan Al- ihsan writer yanzu aka Fara sharan fagen 😁😁 karku damu

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now