SHI NE MIJI NA PART 8

7 0 0
                                    

Yana budewa sheki da dauke ido su suka bayyana,duk mukace "wow". Salman a Ina ka samo wannan zoban haka?
Bai ce Mana komai ba, Sai ya tashi ya durkusa agaban salma, yace Salma will you marry me?
Hawaye cike a idon Salma tayi saurin girgiza kanta sannan tace yes! I will marry you.
Duk mukasa ihu tare da shewa.
    Kwana biyu da faruwan Haka, wani abin Al'ajabi yafaru tsakanin gidansu salma da gidansu salman, Wanda har yaja sun raba kan yaransu,Wanda yanzu ko ga maciji basa Yi da juna.
  Tana kaiwa Nan tayi ajiyar zuciya tare da mikewa tsaye tace son kayi hakuri ba zan samu damar raka ka airport ba, sabida ya zama dole nabi bayan Salma.
Tace son ka gama hada kayanka kuwa? Domin time yayi,
Ya sauke ajiyar zuciya Shima yace eh nasa su Neena su gyara min su acikin jakar da zan tafi da shi.
Tace toh mashaa Allah son Allah ya kiyaye hanya Amma idan ka Isa ka kirani kaji Koh? Tayi waje wajan Direba da ke jiranta.
  Yana Jin fitar motarsu yayi ajiyar zuciya yace uhmm! Ummi da kin san yanda nake Jin Salma Araina da Baki damu kanki akan Rayuwar su Salman ba.
Wani bangaren na zuciyarsa na karfafa shi da cewa, to me zai Hana kayi Amfani da wannan damar da Allah yakawo ka fadawa Ummi abinda ke neman kwantar da Kai ya salwantar da ci gaban Rayuwarka.
Ko Kuma ka samu uncle Sudais kafada Masa, babu haufi zai fahimce ka, Kuma zai iya mallaka maka abinda Rai da zuciyarka ke so, walwalarka da kuzarinka su dawo, ka dauko Salma ku rayu tare har Abada, ku haifi 'ya'ya masu albarka har zuwa karshen rayuwarku.
    Duka wannan tunanin Saleem yayi shi ne cikin 'yan dakikan da Basu wuce Sha biyar ba.
Ji yayi zuciyar Tana sanyi daga zafi da suyar da take yi.
       ( Tirkashi🤔, to fa! Wannan shine Ake cewa ana wata ga wata, masu karatu idan Kun San abinda zai faru Nan gaba, to na baku damar Fadi, don ni Kam ban sani ba, amma dai kada muyi hanzari, mu cigaba da bibiyar Saleem har mu ga abinda zai faru shin burinsa zai cika koko a'a)
Kansa ya rike da karfi Yana Addu'a, ahankali ya Fara Jin saukin tashin hankalin da yake ciki.
    Kokarin ficewa yayi daga gidan Kai tsaye airport ya wuce, "hmmmm! To Sai dai muce fatan Alkairi captain Saleem asauka lafiya".
           Dan taxi ya sauke ta akofar gidansu, cikin tashin hankali take tafiya, Kai da ganinta kasan ba lafiya take ba, don tafiya take kamar wacce ta Sami tabin hankali, Tana sa kafarta acikin gate din gidansu, tun kafin ta karasa shiga, jiri ya debeta, cikin sauri Mai gadi ya karasa gareta, Yama rasa wane taimako zai Fara Bata, Sai kawai ya dauketa kamar wata yarinya karama yayi main falo da ita, Yana kwalawa su Mami kira.
     Mami Jin Kiran yayi yawa yasa ta fitowa da sauri Tana cewa baba Mai gadi lafiya kuw....... Tsayawa turus, tayi sakamakon ganin Salma Ahannunsa Kuma a sume, yasa tayi saurin sa hanu ta karba Salma, Tana cewa meya faru ? Meya sameta?
       Baba Mai gadi yace wallahi hajiya Nima ban sani ba kawai ganinta nayi ta fito daga taxi zata shigo ciki kenan ta yanke jiki tafadi.
   Tace to nagode baba Allah yayi Albarka, yace Ameen!
Sannan ya wuce bakin gate, daidai lokacin motar Ummi yayi horn.
    Mami da zainab suka Kai Salma dakinta suka kwantar da ita akan gado, sannan Mami ta Kira Dr khaleel awaya tace yazo gida Salma Bata da lafiya, ta katse wayar, adaidai Ummi ta shigo cikin dakin, hankalinta atashe yake, ta dubi mami, tace Anti ya jikin Salma din? Kin Kira doctor kuwa?
          Mami ta tsaya Tana Mata kallon mamaki tace Eh na Kira shi, Amma ya'akayi kika San Salma Bata da lafiya?
    Nan Ummi ta shiga Mata bayanin duk abinda ya faru.
  Mami ta kalleta cikin tashin hankali zata yi magana kenan, Dr khaleel yayi sallama ya shigo, suka gaisa sannan suka fita suka bar shi da salma, ya tsaya Yana kallonta yace Salma! You have to wake-up, because Salman ma Yana can agadon Asibiti akwance tun shekaran jiya.
Yakamata acikinku asamu Mai dauriya ke ko shi,Amma bai kamata ace dukkanku roggwaye ba, you people you have to fight for your love!
Hawaye suka cicciko Masa kwarmin ido, hannu yasa a aljihu ya Ciro hank Chief fari! Ya Fara goge hawayen.
    Bayan ya Gama Mata duk wani abinda ya kamata ya Bata na treatment yayi Mata, sannan yayi sallama da su Mami akan anjima da yamma zai dawo ya Kara duba ta.
                   Umma zaune agaban Abba Tana kuka, tace Dan Allah Abban Salman kayi hakuri kabar yaron Nan ya auri wacce yake so, wallahi daf muke da mu rasa shi, Kum.......... Cikin 6acin Rai Abba yayi saurin katseta ta hanyar daga Mata hannunsa, yace Lallai Sai yau na tambatar da cewa Mata Basu da hankali, kwakwalwarku na kifaye ne, in Banda haka Taya zakice wai na bar Salman ya auri Yar gidan makiyina, bama ki kishin mijinki da Kuma Taya shi yaki, in ma mafarki kike to wallahi ki tashi tun wuri, domin kuwa aure Babu shi tsakaninsu, har abada, wallahi kinji ma na rantse Miki.
       Ke! Dakata ma kiji inshaa Allahu Nan da wata hudu masu zuwa zan daura wa Salman aure da Yar gidan Aminina Alhaji Al_mustapha. Watau yarsa Aisha. Yana Gama fadan Haka yayi waje abinsa domin ta gama Bata Masa rai sosai.
" Hmmmm! Tirkashi 🤔! Kaka kara Kaka ga Akuya ga Kura, yau ake yinta, Ina masoyan Salman kuzo muje wa Salma jaje."
      Alhaji sudais da Alhaji Basheer zaune suna tattaunawa Kuma kamar abinda suke magana akansa Yana da matukar mahimmanci, domin ga dukkan alamu suna farin ciki da abinda suke cewa, domin in kaga fuskokinsu Yana dauke da murmushi sosai,( gaskiya nayi iya yina domin in jiyo muku abinda suke tattaunawar na kasa jiyo muku domin Nima korata sukayi wai na cika Jin gulma da yawa wai Kar na fadawa Salma☹️ Amma kuyi hakuri ahankali zamu sani ai 😜).
       Karfe Tara daidai na dare Salma ta farka. Dr khaleel yace Mata sannu ya jikinki? Ta daga Masa Kai Alamar da sauki.
            Yace Salma! Ina son nabaki some Advice akan Rayuwarku ke da Salman, ya kamata ace yanzu Kun Fara Sanya want zukatarku salama. " Do not your problem slow down, you will achieve alot in life"! Kinji Koh!
Tace thanks alot Dr khaleel.
Yayi murmushi ya Mike yace to Bari na wuce gida Sai da safe kenan.
Tace okay Allah yakaimu.
        Kwanaki ke juyawa a hankali su koma satittika, satittika su ba da watanni, watanni su bada shekara, kamar yadda rayuwa take akullum kenan.
      To Haka CE tafaru da su Salman, domin yanzu watansu uku, Kuma suna cikin koshin lafiya domin yanzu Yan aikin gidansu suna matukar taimaka masu ta hanyar sadasu da juna, walau ta waya ne, kokuma ta hanyar fita da su, shiyasa ma yanzu suka kwantar da hankalinsu waje daya, har iyayensu suka Fara murna cewa yanzu 'ya'yansu sun dawo bayansu.
      Yau ma kamar kullum Salma Tana dakin anti zainab kwance makale da wayar baba Mai gadi suna hiran soyayya da Salman, Wanda Shima Yana dakin Musa Mai gadin gidansu, domin tun da abin Nan ya faru aka kwace wayoyinsu har yanzu ba'a Basu ba.

               Saleem yayi murmushi ya kai dubansa, ga zoben hannunsa. Lumshe idanuwansa yayi Yana tuna Ran da yaga zoben.
      Bayan tafiyarsa da kwana biyu ya tsinci zoben acikin jakarsa, Wanda ga dukkan alamu su Neena ne suka saka Masa aciki, to a Ina suka ga zoben?
    Yayi saurin Ciro wayarsa daga caji ya Kira numbern Ummi, bayan sun gaisa ne, Ummi taci gaba da yin Masa fada akan yayi aure.
Aransa yace Ummi kesss! Amma afili Sai yace inshaa Allahu Ummi da zaran na dawo zan gabatar muku da matar da zan aura.
Cike da zumudi Ummi tace "wow" great that's my son, son what's her name and her place....
Yace Ummi very soon you will all know her and you will love her more than I do. By the way Ummi where Neena?
Tace suna main falo, ta kwalawa Neena Kira, Tana zuwa ta Bata wayar ita Kuma  ta fita.
      Neena tace Yaya Saleem Ina yini, ka Isa lafiya, ya aiki?
Yace lafiya Lau, Dan Allah Neena da kuke hadamin Kaya Kun ga wata zobe Haka?
Tace Eh ni ma nasa maka acikin jakarka, akarkashin gado na gani.
Yace okay thanks, ya katse wayar.
        Umma zaune adakin ta abin duniya duk ya isheta domin yau sauran sati biyu ayi bikin salman, gashi har yanzu ta kasa fadamasa, musamman ma yanzu da taga Yana cikin farin cikin don Haka ba zata fadamasa ba, sabida Bata son abinda zai wargaza Masa farin cikin da yake ciki gaskiya ita bazata iya ba, domin ba za'a ji mutuwar uwar sarki abakinta ba, Sai dai shi uban gayyar ya sanar Masa da bakinsa, Amma ba ita ba.
         Shi kuwa Salman yanzu bashi da sauran matsala domin yanzu kusan kullum Yana tare da salmarsa awaya, in Kuma Yana son ya ganta ne zai yi wa Anti zainab ko baba maigadi ko Ali Direba magana, su Kuma Susan yadda zasu you har su hadasu.
    Yanzu matsalar su daya ce, yadda zasu mallaki junansu gaba daya, Wanda har yanzu sun kasa samun mafita.
                  Ya bat da Kama yayi shigar English wear blue jeans, white shirt, white cambas, black jacket and facing cap. Ya tun karo gidan Kai tsaye dakin baba maigadi ya shiga.
Anti zainab Tana ta waige waige can take yafato baba, yazo tace Ina yake?
Yace Yana dakina, tace to you maza ka kirashi yazo.
Baba ya juya da sauri ya shiga dakinsa yace kayi maza ka shiga karfa ka Dade sosai kaji Koh Dan Allah!
      Yayi murmushi yace inshaa Allahu nagode sosai, Kai tsaye dakinta ya wuce Yana shiga ya sameta ta fito wanka kenan, Tana daure da tawul daidai cinyarta.
      Tana ganinsa atsaye tasa ihu, shi Kuma ya bude Mata hannayensa, tazo da gudu ta rungumeshi.
   Tace meya kawo ka Nan? Yace Au! Baki San abinda ya kawo ni bako? To shikenan Bari na wuce abina.
    Ta sake manne shi sosai ajikinta, tace am sorry love!!
Yayi murmushi, yace Ina Mami zata da yamman Nan?
   Ta Dan tabe bakinta kadan tace danta ne ya dawo,shine kaga take ta sauri Haka. Yace Yaya salihu ne ya dawo?
Tace a'a Yaya Saleem ne Dan gidan Ummi Wanda yake London shine ya dawo yau.
Sai da gabansa yafadi, Amma Sai yayi ta maza yace okay Amma meyasa Baki bita ba?
  Tace banyi ra'ayin binta ba, Kuma......... Horn din da suka ji ne ya katse Mata sauran maganar ta.
    A lokaci guda suka Isa bakin window, mezasu gani😳?
Motar Mami da na Abba suka shigo at once.
      Fitsari ne kawai Salma Bata yi ba,amman ta rude iya rudewa.
Shi ko Salman numfashinsa Yana fita da sauri sauri, kirjinsa kuwa Yana dukan 100_100.
          Jin anbude kofar dakinsu duk suka juyo a razane, Salma ko har da ihu,  anti zainab ta karaso wurinsu ta rike hannunta, tace Salma ni ce fa.
Salma tace anti zainab yau mun shiga uku🙆 duk tabi ta rikici.
     Zainab tace Salma ki nutsu manah! Kiji abinda zanc........ Suka ji muryar Mami a dai dai bakin kofar dakinsu Tana Kiran zainab.
                   Salma na Shirin sake ihu kenan, Salman yayi saurin rufe Mata Baki da hannunsa sannan yayi cikin toilet tare da ita.
     Suna shiga, Mami na shigowa dakin, Tana bin ko Ina da kallo tace zainab Ina Salma ? Kuma Karan me naji dazun?
   Zainab cikin hardewar harshe tace Am.....sa....Salma....ta....Tana..toi.... let, Kuma ba'a yi wata Kara ba.
Mami dai Bata yarda ba ta sake duban zainab dakyau tace SALMAN yazo Koh?
   Zainab tayi saurin dago kanta Tana kallon Mami cike da mamki da Kuma fargaba, tace a'a Mami bai zo Nan ba.
Mami ta harareta Sai da. Gabanta ya sake faduwa.
Mami tace to in bai zo Nan ba, to ya'akayi kamshin turarensa yake Nan? Domin duk fadin street din Nan ba Mai irin kamshin Nan, Sai shi kadai!  Zainab ki fada min gaskiya!
          Anti zainab yadda taga ran Mami ya 6ace yasa tayi saurin zubewa akasa ta rike kafar Mami tace Dan Allah Mami kiyi min Rai , wallahi Salman bai zo Nan ba, in kuma Baki yarda ba toh ki duba ko Ina adakin Nan.
Mami ta juya tafara duba ko Ina har karkashin gado Sai da ta duba, Tana Shirin bude kofar toilet kenan, Abba ya kwala Mata Kira, har ta bude kofa zata fita kenan, Sai Kuma ta dawo, ta nufi toilet din.
    Zainab ta zazzaro idanuwa waje, gabanta naci gaba da faduwa, babu abinda take ambato Sai sunayen Allah.

     " Ni Kam, tsabar rudewa ce ta sa naji cikina ya Fara murda min, don Haka ku tsaya ni na samu nutsuwa. Yanzu aka Fara (war) din, kada kubari a baku labari ku biyoni,
Daga taku
Lawiza Muhammad
( Maman ihsan)

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now