SHINE MIJINA part 12

4 1 0
                                    

Salman an tura shi kwas ( course) akan aikinsa a Nigerian embassy na kasar London Wanda zai yi tsayin watanni Tara.
Salman yayi murna da wannan tafiyar ko babu komai zai yi nisa da Aisha na Dan wani lokaci Mai tsaho.
       Aisha Tana falonta tayi tagumi tasa tv agaba Amma azahirin gaskiya ba shi take sauraro ba. Don tayi nisa acikin tunani. Aisha! Aisha!! Aisha!!! Tare da dan dafata akafadarta.
    Agigice ta dago ta dubi wacce ta dafata Bata San sanda tayi ajiyar zuciya ba tace anti safiya!
Sannu da zuwa ya gida? yasu mommy da daddy? Yaushe kika zo?
Anti safiya tace duk lafiya Lau sunce ma in gaisheki, shekaran jiya na zo baban Amir ma yace in gai da ke.
     Tayi murmushi tace Allah sarki Ina amsawa, Amma meyasa baku zo tare ba?
Tace wallahi yau yaje bauchi shiyasa bamuzo tare ba.
Tace Allah sarki, Allah ya dawo Mana da shi lafiya Allahumma Ameen.
Tace anti mezan kawo Miki na ci ko na sha? Ta Mike har zata wuce, anti safiya tayi saurin rike Mata hannu ta zaunar da ita suna facing juna.
   Tace Sis Aisha meya sameki duk kin bi kin zabge Haka? Eyeh please tell me for the sake of Allah.
  Aisha nan da Nan idonta ya shiga zubar da ruwa Sai kace an bude famfo, tace anti safiya bazan iya boye Miki duk abinda ke damuna ba, sabida duk acikin dakinmu nafi shakuwa da ke Sai Kuma Yaya Habib. Domin ku kadai ne nake zuwa muku da damuwata ko wata iri ce kuma ku min maganinta, ba Sai kin hada ni da Allah ba zan fadamiki, sabida har yanzu a Aishata nake.
Tace Anti safiya watau tun lokacin da kuka kawoni gidan nan, ban taba samun kwanciyar hankalin ba, bare Kuma in samu wata alaka ta tsakanin miji da Mata, Tana kuka Tana fadawa Anti safiya duk halin da take ciki.
     Anti safiya wacce tayi shuru kamar ruwa ya cinyeta, ta sauke ajiyar zuciya cike da tausayin kanwarta ta, tace Aisha kiyi shuru Haka Nan Dan Allah mahakurci ma wadaci kinji Koh! Mahakurci shi zai dafa dutse har ya Sha romonta.
Cigaba da hakuri tare da addu'a har Allah ya kawo Miki mafita ya karkato Miki da hankalin mijinki. Sannan Abu nagaba da zance Miki shine ko da wasa karki sake ki fadawa kowa sirrinki . Taimako daya zan Miki shine akwai wani magani da zan Baki Yana da kyau sosai don ko ni nayi amfani da shi koma yayi min don lokacin da baban Amir shima ya Fara min irin wannan halin wata kawata ta kawo min shi. Inshaa Allahu idan na koma kaduna zan siya Miki Sai in ba wa baban Amir ya kawo Miki, domin Yana yawan zuwa, so Sai na ba shi.
        Amma fa da daddare (night) Zaki saka Masa sachet daya acikin abin sha, irin su tea, drinks Dade sauransu Amma Banda abin ci. Kinji Koh! Inshaa Allahu komai zai yi daidai, ki cigaba Kuma da addu'a.
          Aisha tayi ajiyar zuciya tace anti ba fa wai kwanciyar aure ne fa baya son yi da ni ba! A'a SOna ne fa bai yi kwata-kwata Ina son ka fahimce hakan.
Anti safiya tace na sani ai shiyasa ma nace zan Baki maganin sabida idan har ki kayi Amfani da shi to wallahi duk abinda kike nema Zaki samu ke har ma da so da kauna ke dai kawai ki Bari ya Fara saninki Amatsayin ya'mace  kawai shikenan an wuce gun😉 sauran bayanan zasu biyo baya Wallahi sis ki yarda da ni kawai.
    Aisha toh anti bakomai nagode sosai Allah yasaka miki da Alkhairi Ameen.
Tace to yanzu Ina Salman din ya shiga?
   Aisha tace ai yayi tafiya yau da safen Nan, ni ma bansani ba mairo ce Mai aiki take fadamin dazun Kuma wai ba yanzu zai dawo ba, Sai yayi wata Tara kafin ya dawo.
Anti safiya ta qwalalo ido 😳 waje tace Aisha kinsan abinda kike ce min kuwa? Kina nufin wata Tara zai yi kafin ya dawo! Aurenku yanzu wata nawa?  Aisha tayi murmushi tace yanzu watanmu Tara da aure.
  Anti safiya ta sake qwalalo idanuwa😳 waje tace Aisha...... Sauran maganar makalewa yayi a makogaronta, sakamakon Aisha da take Mata dariya, tsakaninta da Allah takeyi kuwa har Tana rike cikinta domin wallahi ta Bata dariya Sosai.
   Anti safiya ma cikin dariyar ta daka Mata duka tace wannan ba abin dariya bane, idan fa aka kirga zaman aurenku da Wanda zai yi kafin ya dawo, watanni goma Sha takwas kenan, shekara daya da wata shida fa Aisha.
          Tace to Allah na tuba anti Sai me? Nayi ma wata da watanni ma, shekara da shekaru ma agidanmu ba abinda ya sameni balle Kuma Dan shekara daya da rabi.
         Anti safiya tace kinci gidanku! Da can da Nan daya ne? Can gidan ubanki ne, Nan ko gidan mijinki ne, babu yadda zasu zama daya.
Nan dai sukaci gaba da tsokanar junansu har Aisha ta manta da wani miji wai shi Salman. Har dare yayi sukayi wankansu sukaci gaba da hiransu har sarkin Satan Nan ya daukesu ( bacci).

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now