SHI NE MIJINA part 13

1 1 0
                                    

Nan shima Alhaji Sudais ya Fara kwallo da ita duka yake kamar Allah ne ya Aiko shi.
    Saleem ko kuka yake Yana cewa don Allah Abba ka barta don Allah!!! Abba Kar kaji Mata ciwo don Allah ku Hana shi dukanta.
Gashi shi ba Daman ya tashi balle ya Hana Abba dukanta domin dukan Nan da Abba yake Mata yayi yawa jinsa yake har cikin ransa.
  Ai ko ba Wanda yayi yunkurin hanashi domin taba kowa haushi akan abinda tayi wa Saleem, Sai kace ba dan'uwanta ba.
       Abba don kansa ya gaji da dukanta sannan ya barta yayi waje Abinsa Yana hucin bakin ciki, domin har Yana hawaye.
   Mami tayo kanta zata daketa
Saleem na ganin Haka yasa ihu tare da cewa don sonki da manzon Allah (s.a.w) Mami ki barta wallahi ji nake kamarni kuke duka.
      Ta juyo cikin fushi tace Saleem in har ka dauke ni da mahimmanci to Ina son yau din Nan Kuma Ayanzu ka SAKI Salma!
Sai da gabanshi ya bada darrrrammmmm...mmmm!!! Yayi saurin rintsa idonsa tare da fadin innalillahi wa Inna ilaihir rajiun!!!
Yace Mami kiyi hakuri, Amma ko da Zaki kasheni ne wallahi ba zan taba rubutawa Salma takardar saki ba, balle Kuma bakina ya furta, Mami! Wallahi har Abadan in kunga na rabu da Autarmu( Salma) to wallahi cikin biyu ne akayi daya ko dai na mutu ko Kuma itace ta mutu, ko da ace kullum zata Rika yankan Naman jikina bazan taba rabuwa da ita ba, Ina sonta ina kaunarta har karshen numfashina.
          Ummi da Alhaji Basheer sukayi ajiyar zuciya domin Dansu yayi abinda ko da bayan ransu ne iya abinda zai yi kenan, sannan ba duk maza bane zasu iya abinda Saleem yayi ba, Sai Jan jarumin namiji, lallai yau Dansu ya nuna musu cewa shi din namiji ne mashaa Allah.
    Alhaji Basheer ya shafa kan Saleem yace Allah yayi maka Albarka Kuma Kai ma Allah ya baka zuri'a masu albarka da jinkai, suka amsa da Ameen ya hayyu ya Qayyum.
   Sannan ya fita waje shima.
Mami da Dr mansir Suma sukayi waje. Ummi ta karaso gun Salma ta daga ta suka zauna akan kujera.
     Ummi ta dubi Salma dakyau sannan tace Salma meyasa kikayi was dan'uwanki Haka? Eyeh Salma!
   Cikin kuka Salma tace Dan Allah Ummi kiyi hakuri ki gafarta min🙏, wallahi sherin shedan ne, Ummi ba yadda banyi ba don ganin Yaya Saleem bai zo kusa da ni ba, Amma hakan ya cutura, nan ta kwashe duk abinda ya faru Daren shekaran jiya ta fadamata.
Ummi tayi ajiyar zuciya tace meyasa Zaki haramta Masa abinda Allah da manzansa suka halatta Masa Eyeh salma?  "Annabi Mai tsira da Aminci yace Allah ya tsine wa duk matar da taki mijinta ya sadu da ita aduk lokacin da yake so, to mala'iku zasu ta la'antarta ba zasu daina ba har Sai lokacin da ta yarda da shi ( bukhari/Muslim)
Mace tayi gaggawar baiwa mijinta hakuri aduk lokacin da ta ga yayi fushi, tace Masa Dan Allah kayi hakuri bansan abinda nayi zai Bata maka rai ba, ka yafemin Dan girman Allah.
Mace tayiwa mijinta dukkan irin aikin da ake bukata ayishi agida.
Mace ta zama Mai tausayawa mijinta, kamar yadda uwa take tausayin danta".  Salma yanzu acikin wa'annan wanne kikeyi aciki, ta tsaya Tana kallon salma, hmmmm idan na fahimce amsarki babu ko daya daga cikin su, hmmm Allah yakyauta.
Salma ni mahaifiyace a gare ku da ke da Saleem Baki da bambanci da shi, domin duk jini daya suke amfani da shi, Dan Allah Salma kiyiwa Allah ki sassautawa dan'uwanki please 🙏.
Cikin kuka salma tace Ummi nasan nayi kuskure Amma Dan Allah ku yafemin.
Ummi tace bakomai muma Allah ya yafemu dukka, sannan idan mijinki ya farka ki nemin yafiyarsa.
Tace inshaa Allahu Ummi nagode, wai waya fadamuku Yaya bai da lafiya?
         Ummi tace Dr mansir ne ya Kira Alhaji Amma bai same shi ba shine ya Kira Abbanki ya fadamasa jiya da daddare to adaren suka zo gidanmu shine muka kamo hanya.
   Satin Saleem daya aka sallamo shi ya dawo gida, Kuma a ranan su Ummi da Mami suka koma gida, bayan doguwar nasihar da Ummi tayi musu, Mami Kam in Banda zagin Salma da takeyi ba abinda tayi.
       Watan Saleem uku cif! Ya warke garas! Wanda salma ce ke kula da shi Amma har alokacin ba abinda ya canza daga tsanar da Salma keyiwa Saleem, Kuma tun daga ranar bai Kara niman ta ba da sunan wai ya karba hakkinsa na aure ba a'a, ya barta har Sai lokacin da ta yarda Dan kanta sannan, Kuma ya daina kwana adakinta Sai dai a nashi.
          "Tirkashi! Abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, ku fa Yan masoyan AL-IHSAN WRITES me kuka gani shin zai iya"?

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now