SHINE MIJINA PART 10

17 1 0
                                    

Washe gari Salma ta tashi duk idanuwanta sun kumbura sabida kukan da taci jiya da daddare.
Suna zaune ita da su anti zainab abakin gate.
     Zainab tace salma jiya ya'akayi Mami Bata ga Salman ba?
Tace uhmm! Watau lokacin da mukaji kuna magana har kika Mata rantsuwa Amma Bata yarda ba har tazo zata bude kofar toilet, ni da husby muka rasa yadda zamuyi Sai kawai muka shiga cikin shawa, inda ma Allah yataimaka na cikin shawar ne kawai yake ganin na waje.
    To muna shiga Sai Husby ya bude shawar ruwa ya Fara jikamu, to lokacin da Mami ta bude kofar Sai ni Kuma na Fara Waka cikin toilet din, Kuma Daman Mami ta tsani mutum Yana toilet Yana magana ko Waka,Nan zaka Fara Shan zagi da fada har Sai ka gwammaci da dukarka tayi ma zaifi sauki akan fadanta, sabida fada ma har ta manta abinda ya shigo da ita toilet din har ta fita, Kuma kusan wani Abu wallahi wayar Husby Yana akan washing hand base, Amma Bata gani ba, Dan Allah anti zainab kiyi hakuri mun saki rantsuwa akan karya.
             Tayi murmushi tace bakomai Salma tunda dai mun tsira, Allah ya rufa Mana Asiri.
     Baba maigadi yace ai da Naga motar su Alhaji Sai da na tsure, ba abinda nakeyi illa addu'a kawai.
       Ali yace ai baba Bala baka Kai ni ba don ji nayi kamar nayi ihu da Alhaji yace min mukoma gida kawai ya fasa zuwa.
        Anti zainab tace dubesu, kuna wani maganar ku acan, ni Kuma da aka runtsa da ni acikin dakin fa?
Baba Bala yace Kuma fa Haka ne wai! Zainab ya kikayi ne?
  Ta watsa musu harara tayi banza da su.
         Suka Yi dariya Amma Banda Salma, wacce takeji kamar ta mutu, sabida abinda Saleem ya fada Mata Daren jiya, domin jiya ko Runtsawa batayi ba, Tana neman mafita, Amma har yanzu Bata samu ba.
    Ali yace Salma lafiya kuwa kike kinyi kuka Koh?
Duk suka dube ta, sannan sukace Salma meya sameki?
    Kuka ya kwabce Mata, Nan tashiga fada musu duk abinda Saleem yace Mata jiya.
    Duk jikinsu yayi sanyi Kuma sun tausaya Mata sosai, ace wai yarinya kamar Salma wai ita ce acikin irin wannan halin.
    Zainab ta kamo hannayenta tace to ke yanzu mekika ce Masa?
Cikin kuka tace shine har yanzu na kasa samun mafita, Dan Allah anti zainab ku taimakeni Dan Allah! Kuka yaci karfinta dole tayi shuru da maganarta.
       Zainab tace to munji Kuma inshaa Allahu zamu Nima Miki mafita Amma kafin Nan Ina San kije ki kwanta ki Dan huta zuwa anjima Sai muci gaba da magana har Allah yasa mu samu mafita, kinji Ko 'yarta ta kaina.
Da kyar suka samu tayi shiru har ta yarda zata je ta Dan kwantan kamar yadda suka bukata sannan ta wuce zuwa dakinta.
    Zainab tayi ajiyar zuciya tare da dubansu baba Bala tace to yanzu menene shawaranku Anan?
Ali yayi saurin cewa kawai ta hakura ta dau dangana ta aure shi.
Da sauri zainab da Bala suka kalleshi, sukace Ali kasan abinda kake cewa kuwa? Salma ce za'a tunkara ace Mata ta aure Saleem, bayan Kuma kasan irin son da take yiwa Salman gaskiya Ali ka sake kawo wata shawara Amma ba wannan ba.
  Ali yace dole ta aure shi ko Tana so ko  Bata so! Sabida ranar da naje dauko su Alhaji da Alhaji Basheer daga Airport sun dawo dubai  naji suna maganar hada auren Saleem da Salma, Kuma har sun saka ranar bikin wata hudu, sannan sukace bazasu fadawa iyayensu Mata ba, balle Kuma su Salma din Kuma ko da zasu sani Sai ana gobe daurin aure ko Kuma ranar daurin auran.
Sannan suka ja min kunne akan Kar na fadawa kowa idan ba Haka ba to zan rasa aikina, Wannan shine dalilina nacewa gwara kawai ta hakura ta Amince da Saleem Amatsayin shine mijinta ba salman ba. Kuma wannan maganar da nake fada muku yanzu Haka jibi ne daurin auran! 😳 Sukace jibi fa Ali? Yace inshaa Allahu.
Sukayi shiru Sai dai wannan ya kalli wancen, sukace to yanzu wa zamu tunkara da maganar Nan, Salma ko Salman? Ali yace ai Shima Salman din zai yi aure Amma da dukkan alamu bai ma sani ba domin A jiyar  Alhaji sultan yabawa Alhaji invitation card wai dansa zaiyi aure don Haka wai Alhaji yakai yarsa kasuwa domin dansa yafi karfinta wallahi! Kar kuga rashin mutumcin da yayiwa Alhaji, sannan ya wuce abinsa, Alhaji murmushi kawai yayi sannan yace min Ali kagani koh? Nace Masa ai Sai hakuri Alhaji Allah dai ya zabar Mana mafi alkhairi kawai.
😳 Sukace kana nufin Shima Salman din aure zaiyi? Hmmm! Wannan shine Ana bikin duniya Ake na kiyama....
Washe gari da safe Anti zainab ta Kira salma, tace Daman akan maganar ki ne, to agaskiya mun hadu munyi shawara akan kiyi...... hakuri......ki.....aureee....... Saleem!!! Tana kaiwa Nan tayi saurin kawar da kanta gefe don Bata San taga yadda salma zatayi.
              Girgiza kanta take cikin kidima da gigicewa tace anti zainab! Baba Bala! Yaya Ali! Kunsan abinda kuke ce min kuwa?
Duk kansu na kasa, sukace salma kiyi hakuri haka Allah ya kaddara cewa Saleem shine mijinki ba Salman ba, ki yarda cewa baka auren mijin da ba naka ba, kamar yadda baka auren matar da ba naka ba.komai na Rayuwar Dan Adam tun fil'azal Rubutacce ne a ( lauhul-mahfouz).
        Kuka sosai Salma takeyi har su zainab sukaji zukatarsu na girgiza basa son kukan Salma ko kadan.
         Ali yayi saurin rike hannunta yace Salma ki yarda da kaddara.... Mikewa tayi da karfi ta fizge hannunta sauran kadan ta Fadi cikin zafin nama tayi cikin dakinta da gudu Tana kuka 😭.
                            Abba gani!
Yawwa dauki wa'ancen invitation card din ka rabawa Abokanka su.
    Da sauri ya dago kansa tare da bude invitation card din, me zai gani? Sunansa da na wata, Salman sultan Weds Aisha Al-mustapha Wanda za'ayi kamar Haka Ranar: Asabar
Wuri kabomo, Bakori LGA katsina lokaci: 2pm, yace what 😳? No Abba no!no!!no!!! How comes ABBA, gobe kenan fa? Ni Wallahi ba wacce zan aure in ba Salma ba, Nan ya Fara surutai Sai kace wani zautacce, har Yana kuka😭 Sai kace wani karamin yaro.
Umma tace Dan Allah Salman kayi hakuri ka dauki kaddara ka yarda cewa wani baya auren matar wani, ka dauka cewa Aisha ce matarka ba Salma ba, Kuma kasan cewa komai na Rayuwar Dan Adam Rubutacce ne a (lauhul-mahfouz), itama kuka ya Soma cin karfinta, sabida a yanzu ankai wani stage din da ta Fara Jin tausayin Dan nata.
      Ali gobe ne fa daurin auran Salma inshaa Allahu.
Amin, Amma Alhaji baku tunanin wani Abu na iya faruwa ga yaran?
Yarda suke son kansu Haka,suna iya yin komai fa?
Alhaji yayi murmushi yace na yarda yaro yaro ne, Kai in Banda abinka ka taba ganin mutum yayi abinda Allah bai Yi niyya ba? A,a
To kawai mu zubawa sarautar Allah ido kawai.
Ahaka har suka Isa office din Alhaji sudais.
                 Salman ko tunda ya shiga dakinsa yake kuka, don bakin ciki Sai ya Sanya kansa cikin gwiwoyinsa kamar karamin yaro yaci gaba da kokawa kansa da kansa.
   Wayyo 🙆 Allah sarki Salma.. Tana can Tana Mana planning yadda zamuyi aure, Amma sakamakon sa shine in karya Mata zuciya in zubar da mutuncina, so da kauna a idanunta, kullum cikin hirarmu Sai tace min " karamin mutum shine Mai saka khairan da wulakanci, shiyasa ta tsane mutum Mai irin halin.
To yau gashi zan zama mayaudari agun Salma! Allah yabaki hakuri Salma wifey, ya Kuma Baki Wanda ya fini.... Ya kifa Kai Ajikin gadonsa yaci gaba da kukansa Mai sauti.
     Ihun da Salma keyi ne ya tashi hankalin Yan gidan, anti zainab tace innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, Nan take itama ta Fara kuka don gaskiya ba zata jure ba.
Su baba Bala sukace Subhanallahi zainab lafiya kuwa? Dan Allah kiyi hakuri kiyi shiru Haka Nan.
Tace ki bar ni nayi kuka ka zan samu sa'ida acikin zuciyata, gaskiya bazan iya jure zama acikin gidan nan ba, muddin Salma na cikin wannan halin.
   Sukace kiyi hakuri zainab ba kuka zakiyi ba Addu'a da rokon Allah kadai Zaki Taya su Salma da shi, suna cikin Haka suka ga Salma ta fito da gudu tayi wajen gate, Mami ta biyo bayanta Tana kiranta tare da cewa Dan Allah karku barta ta fita Dan Allah ku tare min ita, itama Mami Tana magana Amma hawaye na zuba daga idonta.
Amma Ina! kafin su Ali sukai ga zuwa gun gate din har Salma tayi waje.
       
              Salman yayi shirin shi tsab! Duk da baya Jin wani karfin jiki Amma haka Nan ya shirya ya fito.
Umma ita  kadai afalo ya zo zai wuceta, tace Salman Ina zuwa da yamman Nan? Bayan Kuma baka da lafiya.
Hawaye suka ziraro daga idanun Salman sharrrrrrr... Suka zuba kamar an sunce famfo, yace cikin rishin kuka," Umma kiyi hakuri Kuma ki yafemin da abinda zan fada yanzu Dan Allah Umma kada kiyi Masa wata fassara daban, Amma yau ya zama dole nayi abinda zuciyata ke gaya min, watau yau zan kyautar da Kuma mallakawa Salma kaina adaren yau! Don bazan iya bai wa wata in ba Salma ba, Sai na dawo.
      Cikin munguwar kaduwa Umma ta tashi tare da kwala Masa Kira Amma kafin kace kwabo har ya fita da mota.
Nan ta zauna Tana kuka tare da cewa, wannan wani irin so ne yake yiwa Salma, wanda har Yana ikirarin zai mallaka Mata kansa, innalillahi wa Inna ilaihir rajiun!!!.
          Saura kiris, ya bige Salma Allah yataimaka, ita ko ajikinta don ayanzu Haka mutuwa itace kawai abinda take bukata, Bata juya ba kawai taci gaba da tafiyar ta sauri sauri gudu gudu kamar Mai yin safah da marwah.
Ita kanta Bata San Ina take jefa kafarta ba, fatanta kawai ta ganta awata duniya Amma ba wannan ba, Kuma hawaye Basu bar tsere akan kundukukinta ba Tana ta sharewa fa gyalenta.
   Da ta Kara Jin karar mota abayanta ai Sai ta Kara Artawa aguje, Shima Kuma ya Kara wutar motarshi, ya Sha gabanta har ya Dan  bigeta ta Fadi.
    Sannan ya fito, ya taimaka Mata ta tashi ya rike hannunta Gam Gam domin kiciniyar kwacewa take Tana rokonsa kada ya Mai data gida.
    Salman yace " na rantse da mahaliccina bazan Mai da ke ba, shiga mota.
     Tana Jin muryan salman dinta tayi saurin bude idanunwarta domin duk abin Nan da sukeyi idonta arufe suke.
Ta rungumeshi kukan dai bai tsaya ba Amma taji sa'ida aranta, ta shige mota suka tafi.
Lokacin gari ya Fara Dan duhu misalin karfe bakwai na yamman jumma'a kenan, Kuma daidai lokacin da sukaji sanarwa agidan rediyon Aso FM cewa Ana gayyarta yan'uwa da abokan Arziki zuwa daurin auren 'ya'yan Alhaji sultan da Alhaji Al-mustapha, watau DOCTOR SALMAN SULTAN DAURA DA MALAMA AISHA AL-MUSTAPHA BAKORI.
Wanda za'a daura acikin garin katsina A karamar hukumar Bakori.
  Sai Kuma 'ya'yan Alhaji sudais da Alhaji Basheer, watau CAPTAIN SALEEM BASHEER HOTORO DA MALAMA SALMA SUDAIS TAKAI.
Wanda za'a daura acikin garin Kano A karamar hukumar Takai Allah yabada ikon zuwa sannan Kuma Allah ya Basu zaman lafiya Allahumma Ameen.
       Sauran kadan ta tsuge da zawo bayan ta gama Jin sanarwan.
Shi ko salman Allah kadai ke controlling din sitiyarin motar Amma ba shi ba, domin yadda yake sharara gudu akan titi kamar zasu tashi sama.
    Saleem Yana kwance adakinsa Yana kallon news a NTA, Yana kallon abinda ke faruwa aduniya acikin kuwa har da sanarwan daurin auren su, bai Gama tabbatarwa ba har Sai da yaga hotonsu shi da salma.
He was shock and suprise, ai bai San sanda ya dauko key din motarsa ba, don Yana son ya tabbatar da abinda ya gani shin mafarki ne ko Kuma agaske ne.
Da sauri sauri ya sauko zuwa falo Yana kwallawa Ummi kira.
     Ummi na dakinta Tana sallah Amma sabida irin Kiran da Saleem ke Mata har yasa ta manta da yin sujjada Sai dai kawai taci gaba da yin kabbara gashi ba Daman ta katse sallar.
   Tun daga bakin kofar falo yake kwala wa maigadi Kira tare da cewa baba Musa yi sauri ka bude min gate.
        Saleem na gudu akan titi zuciyarsa kamar takarda don haske, Allah Yana cika masa burirrika tun gabanin yayi furuci akansu.
Addu'a yake yi Allah yasa Salma ta karbe shi da hannu bibbiyu Kuma Amatsayin mijinta Kuma Abokin rayuwarta, Allahumma Ameen.
     Motar Saleem ta sako Kai farfajiyar gidansu salma, Sai dai me? Yana shiga cikin gidan yaji gabansa yafadi yayi saurin yin salati,  yayi sallama afalo Sai dai me? Ganin Mami yayi Tana kuka da karfinta, yayi saurin karasowa tare da fadin Subhanallahi Mami lafiya? Tace Dan Allah Saleem ka taimakeni ka dawo min da salma, tun da tafita ba'a ganta ba Dan Allah ka taimakeni please Saleem! Ai Bata Gama magana ba yayi saurin fita ya nufe gun motarsa Ali ma ya bishi, baba Bala ya bude Masa gate ya fita.
      Ummi Tana idar da sallah ko Addu'a Bata tsaya yi ba, ta fito zuwa falo, Tana fitowa idonta suka sauka akan hotunan su Saleem Wanda ake nunawa a TV, gefe daya Kuma taji kamar sheshekar kukan mutum, tayi saurin juyowa wazata gani? Neena ce ke kuka Agaban tv.
Ta karasa zuwa ga Neena ta dagata sannan suka zauna akan kujera suna facing juna, meya faru Neena? An Bata Miki Raine? Dan Allah Neena kiyi min magana manah ko zanji dadi.
     Neena ta sharce hanci da ido da tishun dake gefen tv, magana ta farko da ta furta Mata shine: Ummi Daman Yaya Saleem zaiyi aure gobe shine ban sani ba? Ko ban cancanci in sani bane, shin Ummi kin taba tunanin irin son da nake yiwa Yaya Saleem, Ummi sabida da shi na ta korar duk wani Wanda yace Yana so na! Sabida shi naki komawa gida, Amma yau an waye gari Yaya Saleem zai yi aure da wata ba Dani ba..... Sauran maganar makalewa yayi a makogaronta ta Soma kuka 😭.
        Hankalin Ummi ya tashi, kololuwar tashi kuwa, don ita gwata gwata Bata taba lura da hakan ba duk iya zamanta da Neena, shin wai yaushe ne ma aka Fara maganar auren Saleem har da ana Shirin yin aure gobe Amma Bata sani ba, Kuma ba Wanda yafada Mata acikinsu yayan nata da matarsa, Kai har ma da mijinta da Kuma Saleem din, wai da yaushe suka Fara 6oye Mata sirrika ne?.
               Abba yakira Umma awaya yace am! Saratu ki fadawa Salman cewa yayi maza ya taho katsina domin ayi daurin auren Nan da shi!
     Umma tace wani Salman din? Yace banson shashanci Salman nawa ne kika sani?
Tace to ai Salman baya Nan domin kana fita Shima ya fita, Kuma har yanzu bai dawo ba.
Nan ya hauta da fada inda yake shiga ba tanan yake fita ba yace to kiyi maza ki kirashi awaya kinji Koh?
     Ranta abace don me Alhaji zai hauta da fada ko ita ta sashi yayiwa dansa abinda baya so, azuciye tace to Alhaji da hakwarana  zan Kira shi, mutunin da bashi da waya ne zan Kira.
          Yana Jin Haka ya tuna da cewa duk wayoyin Salman suna gunsa bai Kara CE Mata komai ba, ya kashe wayarsa.
   Umma ta Mike tsaye kawai tayi dakinta Rai a6ace zama tayi abakin gado tayi tagumi da hannuwa bibbiyu yanayi fuskarta kuwa ba zai karantu ba.
          Har Sha biyu na dare yayi Saleem da Ali suna kan yawon niman Salma Amma shuru kakeji sai kace malam yaci shurwa.
     Saleem yayi hagu, Ali Kuma yayi dama. Sha biyu da kwata kafin Allah yataimake su, suka same wani Mai boutique Yana Shirin rufewa kenan.
          Sukayi Masa sallama sukace Dan Allah Dan'uwa kaga Mana wata yarinya haka me Kama kaza da kaza? Ali ya nuna Masa hoton Salma awayarsa, yace tabbas na ga wannan yarinyan dazun sunzo ita da wani saurayi me kaman kaza da kaza.
Nan take Ali ya gane ko waye ne, yayi saurin nuna Masa hoton Salman da ke wayarsa yace wannan ne? Dan matashin yace kwarai kuwa shi ne!.
Sukace okay mungode sosai Allah yasaka da Alkhairi, yace Ameen sannan yayi musu sallama ya wuce abinsa.
                Saleem ya jingina da jikin mota Yana ajiyar zuciya tare da cewa Salma me nayi Miki? Meyasa Baki Sona, Baki kaunata,meyasa!!! Meyasa kika zabi bare akan Dan'uwanki na jini why Salma...
                          Ali ya juya Yana huci, cikin kakkausar murya yace Saleem kasan me kake cewa kuwa? Salman din ne bare?
To Bari kaji na fadamaka da Kai da Salman duk daya ne agunta, infact ma Salman ya fika matsayi da mahimmanci agunta, to Bari ma kaji na fadamaka Salma yanzu ma Bata son ta Kara ganinka, domin kana daya daga cikin wa'inda suka Kara Ruguza Mata farin cikinta.
Da baka fadamata abinda kace Mata shekaran jiya ba, to wallahi na tabbatar Kai ne mutum na farko da Salma zata kawo Masa matsalar ta.
Amma me? You fail her.
Na dauki Salma tamkar kanwata uwa daya uba daya, ba sabida komai ba, Sai don kawai ta kasance ba ruwanta da halaye irin na 'ya'yan  masu kudi, watau hali irin na isgilinci kokuma irin masu nunawa mu ai 'ya'yan masu kudi ne, to a'a! Wallahi Salma Bata daga cikin masu wannan halin, ta dauki kowa equally agidan Nan, Kuma ban taba Jin ta Kira sunan mutum Kai tsaye ba, har Sai tayi Masa inkiya.
Ta inda yake shiga Bata Nan yake fita ba, yau halin Aliyu Haidar din ya motsa😜.
      Shi ko Saleem tun da Ali ya Fara zazzaga Masa kwandon masifa yayi shuru baice komai ba, har Ali ya Gama fadansa, sannan suka shiga mota, suka nufi hanyar dawowa gida.
Cikin motar ma ba Wanda yayi magana wa Dan'uwansa, domin kowa da abinda ke Ransa.
Karfe daya daidai suna fall kowa da abinda ke Ransa, Mami tace to Ali, Saleem nagode kuje ku kwanta ku Dan huta.
Saleem ya Dan Susa Kai, sannan yace Mami Dan Allah zan iya kwana adakin Auta?
Sai da kalleshi da kyau, sannan tace why not! Go ahead son.
Sannan kowa ya watse ya nufi inda zai sa hakarkarinsa.


SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now