Mutuwar Rashidu ( baban sa'adatu) ya wujijjiga Nabila (maman sa'adatu) yanda mutum bai taba zato ba, ta daina wanka, ta daina walwala ta daina shiga mutane ta daina ci da Sha, ko ta kwana da yunwa duk daya.
Don Haka mahaifiyarta ta dukufa yin Mata addu'a sannan tasa ake yin Mata Rubutun dangana, aka Rubuce Mata AlQur'ani ta Sha. Don Haka ahankali ta Soma warwarewa ta koma harkokinta Amma ba kamar da ba.
Sa'adatu na girma hankali na Ratsata.
Ba ta da kwaramniya Sam, hatta muryarta sanyi gare ta, Amma fa wasan dandali baya wuce ta, ko ba zata shiga ba ayi gadar da ita zata zauna gefenta kunna aci bal bal,.
Sanda sa'adatu ta Isa shiga makaranta lokacin ne daya zo wa sa'adatu da Karin hankali. Ta lura mahaifiyarta Bata damu da ita ba Sai it's Kuma ta dage wajen kyautata Mata da yin Mata hidima, gyaran daki, wankin kayanta duk dai abinda ta San zai faranta ran innanta Tana yinsu.
A hankali zuciyar Inna ta Soma kaunar Yar Tata, da kanta ta dauketa ta kaita makarantar firamare, Sai dai Mai Nisa ce sosai da gidansu.
Don Haka kullum Tana hanyar zuwa makaranta, taje da kafa ta dawo da kafa ita da kawayenta su dawo.
Makarantar na karbar naira dari biyar duk bayan watanni uku daga kowanne dalibi, haka Inna ke kukkullawa ta biya,in Bata bayar ba a Koro ta, ta kwashe kwanaki agida kamin ta samu ta biya.
Kullum mahaifiyar Inna Sai tayi wa Nabila fada akan tayi wani auran Amma taki, ba don komai ba Sai don cewar ta San ba zata samu Mai halin Rashidu ba da nagartarsa.
Sannan Kuma ta roki it's da tayiwa Allah da Manzonsa ta kyaleta da auren kowani miji ba zata iya ba ta barta ta raining diyar Rashidu kadai, ta inganta rayuwarta tayi Mata aure in ta Kai munzalin. Wannan ne kadai burinta a rayuwa.
Bayan wannan Bata da wani sauran buri, Sai na gamawa da duniya lafiya da cikawa da imani
Tun daga wannan lokacin Nabila da mahaifiyarta Basu Kara yin zancen tayi aure ba. Kula da rayuwar sa'adatu ne a gabansu da tarbiyyarta. Lokacin shekarun Sa'adatu goma Sha biyu Tana firamari aji shida.
Ko lokacin da Sa'adatu ta kowa zancen tallan kindirmo Inna Bata so ba Amma da tayi Mata bayanin yanda zata dunga yi idan take makaranta sun tashi karfe biyu na rana, Sai taje tallan kindirmon, da kyar Inna ta yarda.
To kunji mafarin tallan Sa'adatu kenan.Sa'adatu ta shigo da kayan tallanta ta aje atsakar gida tayi maza tayi alwala bayan sun idar Inna tayi gyaran murya tace "sannu sa'a kinji! Allah yayi Miki albarka" sa'a tace Ameen Inna.
Inna tace Sa'adatu idan Allah yasa kin Gama makarantar Nan Sai aure Koh? Sabida Kinga ni bani da kudin da zakici gaba don Haka idan kina da Wanda kike so to kiyi Masa magana Sai ya turo magabatansa kinji Koh?
Afirgice ta juyo ga Inna.
Dariyace ta Kama Inna ganin idanun Sa'adatu sunyi mitsi mitsi. Amma Sai ta dake.
Tun daga ranan Inna Bata sake yiwa sa'adatu maganan aure ba, Amma da Tana Nan akan batunta.
Ita kuwa sa'adatu tunda Inna tayi Mata maganar aure, aranta tace oh! Ni Sa'adatu Ina zan samu miji? No da ko maza bana kulawa balle koma har into saurayi.
Yau ma kamar kullum suna hanyar dawowa ita da Atika Yar ajinsu cikin nishadi suka ji magana ta bayansu duk suka matsa gefe.
Ya sauka akan kekensa Yana murmushi yace "a'a , Yan makaranta an taso ne?" Idanuwanshi akan sa'adatu, sukace "eh mun taso." Ina yini? Yace lafiya Lau, har yanzu idanunsa akan sa'adatu, am! Dan Allah zan iya sanin gidanku?
Atika tace namu ko nasu sa'a?
Yace duka. Atika tayi Masa kwatancen gidansu Dana sa'a. Yayi murmushi sannan yace toh nagode sosai Kuma inshaa Allahu Ina Nan zuwa da dare kunji?
Atika tace toh sai mun ganka.
Inna na tsakar gida, sa'adatu tayi sallama ta aje jakar makarantarta ta fada jikin innarta Tana fadin "wash! Inna na gaji sosai. Inna ta rungumeta Tana cewa, " sannu Yar gidan Inna Allah yai Miki albarka sannan Kuma ya nuna min lokacin da zakiyi aure."
Tayi dariya kawai abinta, ta gyada Kai ta Mike ta nufi can tsakar gida tayi alwala ta gabatar da sallar Azuhur. Sannan ta shiga madafi ta dauko robar abincinta a karkashin turmi.
Bayan ta kammala duk wani aikin gida Wanda takeyi ko Ina yayi tas, sannan ta Debi ruwa tayi wanka ta Sanya kayan makarantar islamiya ta yamma da take zuwa domin yau ba talla, Sai ranan kasuwa take yin talla, ta dau jakar makarantarta ta yi was Inna sallama ta tafi makaranta.
Wannan shine tsarin rayuwar sa'adatu a kullum.
Sa'adatu na cin tuwonta bayan isha'i wani yaro ya shiga yace "wai ana sallama da sa'a".
Kafin ya rufe bakinsa Inna tayi wuf tace kaje kace Masa wai Tana zuwa, Inna ta kalle sa'adatu Tana murmushi tace Kai! Allah nagode maka, tace oya! Kiyi maza kije . Sa'adatu tace aranta waye ne wanin? Kuma meyake Nima agunta? Da zancen zuci tafita tare da mamakin Wanda yazo gunta.
Yana tsaye jikin kararen da suka zagaye gidan, zai yi shekaru talatin dai dai. Yana da kyau Wanda kallo days zaka yi mishi kaga hakan, wankan tarwada , Mai tsayi da rashin kauri Yana da siririn saje agefen fuskarsa Mai laushi da sheki, da ka ganshi kaga bafilace, da Karan hancin da manya idanunsa.
Ta karasa gabanshi Tana murmushi tace au! Ashe Kai ne, Ina yini?
Yana murmushi yace lafiya Lau sa'adatu ya gida ya Kuma aiki?
Tace Alhamdulillah.
Yace to sa'adatu da farko dai sunana SUDAIS MANSUR TAKAI, haifefen cikin garin Nan ne, mahaifina shine Hakimin garin Nan, to dai kinji Dan takaitancin tarihin, tun rannan da na ganki a kasuwa naji na kamo da sanki Kuma son ma na aure, shin kin yarda da na zama abokin raguwarki?
YOU ARE READING
SHI NE MIJINA
RomanceLabari ne akan Aminan juna, Wanda Suke Rayuwa Atare, Kuma suka dau alkawarin hada ya'yansu aure, shin alkawarin zai ciki kuwa? Duk dai ku biyo ni don Jin wannan labarin Wanda soyayya da Kuma kiyayya zai kasance acikin