SHINE MIJINA PART 14

6 1 1
                                    

Bayan sun kallama cin abincin dare Saleem yayi dakinsa Alhaji Basheer da Ummi Suma sukayi dakinsu Sai Salma wacce ta shiga dakin Ummi tayi wanka, Tana fitowa Ummi ta Bata wani sleeping dress Mai kyan gaske tasaka har ta hau gadon Ummi zata kwanta.
    Ummi tace me nake gani Haka Salma? Ya za'a Yi ki bar mijinki shi kadai adaki ya kwana. Kar dai ki ce min har yanzu Baki bashi damar had a gado daya da ke ba🤔
     Tayi shiru Bata ce Mata komai ba.
Taci gaba, Salma kiji tsoron haduwarki da ubangijinki ki ba wa mijinki hakkinsa, yanzu dai abinda nake so da ke shine ki tashi Maza ki tafi dakin mijinki ko da ba Zaki had a gado da shi ba, amman kije dai ki kwana adakin.
  Bazata iyayi wa Ummi musu ba Sai kawai ta tafi.
       Tana shiga cikin dakin Sai ta hangoshi Yana durkushe akasa ya rike cikinsa Yana mukurkushewa alamar dai cikinsa na Masa ciwo.
      Tayi saurin karasawa gunsa Tana fadin Yaya Saleem lafia kake? Meya sameka? Duk tabi ta rude sabida ita Sam Bata son taga mutum bashi da lafia ko da kuwa makiyinta ne.
          Yace Auta cikina ne yake min ciwo sosai Dan Allah ki taimakamin please 🙏
Tace kodai na Kira maka su Ummi ne?
Ya girgiza Mata Kai, a'a
Dan Allah karki tashi wallahi naji dadin yadda Kika rikeni
Tayi saurin kallon yadda ta rikeshi Ashe rungume yake akirjinta, Aranta tace tab 😏 yaushe zan iya  ci gaba da zama da Kai ahaka, wallahi tashi zakayi malam! Ta shiga kici-kicin tureshi Amma Sai wata zuciyar tace have Salma Sai kace ke ba musulma ba don kawai yace ki taimaka Masa shine bazakiyi ba haba Salma!!!
    Tayi ajiyar zuciya tare da jawo zanin gado ta rufesu Tana ci gaba da kallon  kyakyawar fuskarsa Tana murmushi.
      Ahaka suka kwana, motsin da yayi ne ya farkar da ita
Akaro na farko kenan da tayi Masa murmushi tun aurensu tare da cewa ya jiki?
  Shima ya Mai da Mata da murmushin tare da cewa Alhamdulillah da sauki sosai Kuma nagode Allah yayi Miki Albarka! Tayi hmmm sannan tace Ameen.
              A gidansu kuwa Sam Mami taki sakarwa Salma fuska sabida akan abinda takeyi wa Saleem.
Don idan kaga Saleem yanzu Kuma ka sanshi ada, zaka ga banbanci sosai, domin yanzu duk yafita daga hayyacinsa ba kamar da ba.
          Salma da taga ba fuska awurin Mami Sai kawai ta koma gun Anti zainab suna ta hiransu
Har lokacin da Saleem ya shigo yace Mata tazo su wuce fuskarsa ta nuna Yana cin tsananin damuwa, Aranta tace wannan Kuma meyasa meshi Haka har ya fito fili oho Masa shi dai ya sani 😏.

           Aisha tace Umma Dan Allah na dan tambayeki? "Eh Aisha Ina jinki".
   Umma wacece Salma ?
Sai da gabanta yafadi, tace ke ko a Ina kikaji sunan?
     Tace wallahi kullum Sai naji Yaya Salman na mafarkinta wani lokacin kaji Yana kuka, kokuma kaji Yana dariya tare da Kiran salma, Dan Allah Umma please 🙏 idan kin santa ki fadamin ko ita din wacece agunsa.
          Hmmmm Umma tace tabbas Ni ko na San Salma domin kuwa agabana aka haifeta, Nan Umma ta Bata duk wani labarin rayuwarsu sannan tace idan kina neman wani Karin bayanin toh ki nema Zainab zakiji komai agunta.
  Tace Umma Dan Allah ko kinsan irin abubuwan da Salma take mishi idan Yana cikin bakin ciki har ta sashi Dariya.
      Umma tace gaskiya bazan iya ce Miki gashi ba, sabida bani na reneshi ba zainab itace Nanny su shi da Salma.
        Tace Umma wacece Kuma zainab?
( Idan masoyan Al-ihsan writers Basu mance ba mun bada tarihin Anti zainab da yadda akayi suka hadu da su Umma) nan Umma ta bada tarihin zainab, tun su Salma na da watannin uku aduniya renansu ya dawo hannun zainab, shiyasa tafi kowa sanin halayensu.
      Umma tayi ajiyar zuciya tare da cewa to kinji labarin zainab da Kuma su Salman.
       Aisha taji tausayinsu kwarai dagaske sannan tace  Umma nagode Allah yasaka "Ameen".
            Bayan Aisha tayi wa Umma sallama zata wuce gidanta, Amman Sai ta samu kanta da son zuwa gidan Alhaji sudais ba don komai ba Sai don son zuwa gun anti zainab domin tayi Mata wasu tambayoyi akan Salma da Salman.
        Ta ko ci sa'ar ganin anti zainab domin kuwa Tana Shirin shiga gidan su Kuma suna fitowa ita da Ali direba zasu kasuwa. Bayan sun gaisa ne Aisha tayi Mata bayani abinda ake tafe da ita.
    Anti zainab tace Allah sarki ai bakomai Nan ta Bata labarinsu da Kuma irin abubuwan da Salma takeyi wa Salman idan Yana cikin bakin ciki da damuwa, sannan Kuma ta fada Mata sirrin duk Ranar juma'a ( Friday) wacce Salman yafi tunawa da ita, domin Ranan ne Salma ke yawan so da Kuma yin abubuwa da dama wa Salman.
           Aisha tayi Mata godiya sosai sannan ta dau hanyar nassarawa cike da farin cikin cewa nesa tazo kusa🤗.
             Yau ta Kama juma'at babbar Rana, musamman ma ga Aisha wacce take ganin inshaa Allahu yau zata cika burinta.( Toooh masoyan Aisha ku fito fa ku taya fan dinku addu'a domin ganin cikar burinta ) ku ci gaba da bibiyata sannu a hankali inshaa Allahu zamu Kai ga ci.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 13, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now