SHINE MIJINA PART 9

15 0 0
                                    

Acikn toilet kuwa Salma da Salman sun rasa yadda zasuyi suna cikin Haka aka turo kofar toilet din.
Mami tace Salma!!! Me nake gani Haka? Kuma me nake ji Haka? Eyeh!
Salma wacce ta gama Rudewa tace na'am Mami mekika ce?
Mami tace dan'ubanki bana hanaki kina wanka kina Waka ba?
Cikin sarkewar murya tace am sorry Mami.
Mami tayi tsaki mtswww! Allah dai ya shiryeki, sannan ta fito daga cikin toilet din tayi falo inda Abba ke kiranta.
      Zainab na ganin Mami ta fito daga toilet lafiya Lau ba tare da taji ki ta ga an fito da su Salma ba, cike da mamaki tace Aranta a'a ya'akayi ban gansu tare da Mami ba, ta kyabe Baki, ta fita da gudu daga dakin ta shige ta kofar kitchen.
Firji ta Fara budewa ta dauko Robar Ruwan Gurara biyu Mai Rangwamemen sanyi ta shanye dukka, sannan ta same nutsuwa,Ta fito tayi wajensu baba maigadi.
    Salma najin Mami ta rufe kofa, tayi saurin fita daga cikin shawa, ta dauki towel guda biyu, ta saka daya taba Salman dayan, sannan suka fito zuwa daki, da sauri tayiwa dakin key.
      Kai tsaye ta nufi wadrop ta fito da wasu Kaya na maza ta Mika Masa, tace kasan kayan Nan kuwa?
      Yace a'a, Amma naso na Dan gane shi, in fact na manta shi.
    Tayi murmushi tace ka manta kayan da ka bani, ranar da muka je park akayi ruwan sama, muka jike har muka biya ta wajan Mai wanki da Gugarku, ka karba kala biyu naka da nawa.
            Nan take ya tuna, tabbas! Ya tuna wannan Ranar Wanda Yana daya daga cikin ranakun da bazai taba mantawa dashi ba.
Ya karba ya saka Riga da wando ne, White Mai ratsin pink long sleeve.
Tace "wow" Wallahi kayi kyau sosai Husby.
Yayi murmushi yace godiya nake wifey, Nima bari Nima na dauko Miki Wanda Zaki saka.
  Wata English wear grown itama white and pink, Amma ita nata Mai hannun single ne, ya Bata ta saka, sannan ya zaunar da ita agaban dressing mirror, yayi Mata simple makeup.
Yace "wow" mashaa Allah kiyi kyau sosai wifey, ya rungumeta ya shiga kissing dinta, Sai da yayi ma ishinshi kafin ya sake ta, yace Ina iPad dinki dauko muyi pic!
Tace toh sannan ta dauko, sun dauki pics kala_kala har Sai da suka gaji dan kansu sannan suka Bari Haka Nan.
Sun Dade suna Hira har aka Kira sallar mangaruba, kafin yayi Mata sallama ba don sun so ba yabi ta kofar kitchen ya wuce, lokacin kowa na sallah, Kuma ba Wanda ya San wucewarsa.
           Bayan sallah isha'i, Saleem yayi sallama tare da shigowa dakinta, Tana zaune akan sallaya Tana addu'a, bayan ta idar, tace a'a Yaya Saleem sannu da zuwa, Kai ne da daddare Nan? Yaushe ka zo gidan bansani ba!
        Yayi murmushi yace ai tun dazun nake gidan yanzu ma naji shirun ne yayi yawa sannan ban ganki ba, shine nace bara nazo na duba ki. Tace Allah sarki yayana nagode wlh, Daman yanzu nakesan na idar da ibaduna sannan Sai na sako kasan, dama kayi zamanka wlh yayana da baka wahalar da kanka ba.
        Yayi murmushi " to ya za'ayi? Ai ko bangon duniya kike bazanyi kasa a gwiwa ba wajen zuwa ziyararta ba, domin ki bakomai idan na ganki ko naji muryarki ma ai naji dadi, don kawai na ganki ne yasa ma na dawo Nigeria". Azuci yake Fadi, bai San afili yake yi ba sabida azabar son da ke Kara Ruruwa a zuciyarsa.
   Sai tayi Dan Jim! tana nazarin kalamansa.
       Ya Ankara da katobarar da yayi, yayi saurin gyarawa da cewa nayi fushi 😠?
       Tayi murmushi tace Babban Yaya A min Afuwa nayi kuskure, kaina bisa wuya na, tare da Dan rike kunnanta.
Tayi matukar birge shi sosai, shi dai komai nata na birgeshi ji yayi kamar Kar ta daina magana, sabida zakin muryarta. 
Murmushi yake sosai, ya kwaikwayi 'yar muryarta " ai min Afuwa nayi kuskure kaina bisa wuya na babban Yaya."
         Kunya CE 🙈, ta kamata ta rufe fuskarta da zara zaran yatsunta.
   Yace Autarmu! Yau zuwan naki ne, domin akwai abinda ke damuna acikin Rai na! Ya sauko daga akan kujera ya baje Agabanta, yace SALMA! Ina son ki da aure, Dan Allah ki taimakeni ki taimake Rayuwata ki Amince min, wallahi tun Ran da na Fara ganki naji Ina mutuwar sonki, son da ban taba yiwa wani irinsa ba, please Auta! Accepted my request!.
       Ji ta Yi kamar an dora Mata dutsen uhudu akanta, sabida nauyin da kalamansa yayi Mata, A gigice ta dago ta dubi Saleem jikinta na Bari na rudewa da gigicewa, ta shiga waiwaye waiwaye kada wai ko wani ya shigo dakin yaji abinda Yaya Saleem yace.
         Shi kuwa Saleem ko Akwalar rigarshi, bajewa ya karayi Agabanta Yana cin gaba da gaya Mata duk kalaman soyayyar dake fitowa tun daga karkashin zuciyarsa  ba daga fatar Baki ba, idanunshi alumshe, yayi kyan da Bata taba lura Ashe Yana da shi Haka ba.
         Saleem Ummi ne sak, fari Sol da shi, ga tsayi ga zati, kwayar idanunshi ba bakake bane ( brown) ce mai sheki, da ka ganshi kaga Ummi kamar tayi kaki ta tofar.
     Saleem na kirki, daga kallo na farko da kayiwa Saleem zaka gane mutum ne Mai faram-faram da haba-haba da jama'a ( sociable) Kuma yaro Mai halin manya, captain kenan sojan sama( air Marsha).
      Karkawar da jikinta keyi yakaru, don Saleem yaki yin shiru, ita Kuma gaba daya Agigice take.
Kuka ta sakar Masa Mai karfi, Arude ya dago kansa yace Auta! Meya saki kuka? Ko sabida nace zan aureki?.
        Cikin kuka tace Yaya Saleem kayi hakuri wallahi bazan iya Auranka ba, bazan iya zama da Kai ba, bazan iya maka biyayya ba, bazan iya cusawa kaina sonka da kaunarka ba! Am sorry to say! Ta hada hannayenta biyu Tana bashi hakuri.
             Ji yayi kamar an watsa Masa garwashin wuta, sabida zafin da kalamanta yayi Masa.
         Cikin sarkewar murya tare da hadiye wata zazzafar miyau yace  " okay no problems", thanks alot, yanzu akan wani can bare kike cema dan'uwanki Haka, thanks! Thanks very much! Wow what a great performance!"wow".
       Nan yaci gaba da surutansa, sannan yace okay, but I will like to said something to you dear! As far as you said so, then I would force you to marry me? But you have to choose betweens me and this! Ya Ciro zoben daga hannunsa Yana nuna Mata.
If you love the owner of this Ring, then you have to marry me and get it back, but if not then am sorry to say forget it forever!!! Now the choice is yours, yayi dariyan mugunta, sannan yayi saurin barin dakin, sabida baya son ya sake Jin wata mummunar kalma daga bakinta.
             Yana fita yayi wasu Mami sallama ya wuce gida, Abba yace Am Saleem idan kaje gida kacewa Abbanka wai Dan Allah bana son abun Nan ya wuce jibi, domin ayu komai don kowa ma ya hutu kaji Koh?
Yace okay Abba inshaa Allahu zan fada Masa, sannan ya wuce.
       Mami ta dubi maigidan nata, tace ni fa bangane muku ba fa? Acikin Yan kwanakin Nan Kai da Alhaji Basheer?
        Yayi dariya irin tasu ta manya, yace sa'adatu zakiji ne Amma ba yanzu ba, abinda kawai nake son kiyi min shine kisa Salma tayi duk wani abinda zatayi daga yau zuwa Friday. Kinji Koh?
Ta dai amsa ne kawai Amma kalamansa sunyi Mata tsaurin fahimta.
          Hmmmm! ke kenan Mami bare Kuma mu masu karatu, Amma dai muci gaba da bibiyar Abba, Saleem da Kuma Salma don Jin hukunci da zata yanke.


Ku dai  kuci gaba da sambado comment tare da voting kawai, aci gaba da gashi suya Sai ranar sallah wlh 😆😎😎

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now