SHI NE MIJINA PART 7

13 1 1
                                    

"zainab! Zainab!!"
Mami ke Kira afalon sama. Ta fito daga kitchen tare da amsawa.
Mami tace wai Ina salma, ta gama shiryawa kuwa?
Zainab tace toh Bari na shiga na gani.
Mami tace toh yi maza Dan Allah.
Tana shiga taga Salma zaune agefen gado tayi nisa aduniyar tunani. Zainab ta Kira sunanta har sau uku Bata ji ba, har Sai da zainab ta Dan girgizata sannan ta dago kanta a firgice tare da ajiyar zuciya.  Tace Anti zainab da yaushe kika shigo, Dan Allah kiyi hakuri wallahi ban jiki ba!
Zainab tace dama Mami CE tace wai Baki gama shiryawa bane ke fa kawai suke jira. Zata wuce, Salma tayi saurin riko hannunta ba tare da ta juyo ba. Salma na kuka tace Dan Allah anti zainab kiyi hakuri wallahi nayi Miki Alkawarin bazan Kara yin tunani ko kuka ba. Amma Dan Allah anti zainab na tambayeki manah? Tace ina jinki.
Tace Anti zainab Ina zamuje?
Ta Kama hannayenta masu taushi tace " Salma, yayanki  Saleem  ne zai dawo daga London yau.
Salma ta bita da kallon mamaki tace na San Baki San Saleem ba, toh da ke da Saleem cousins ne.
Mahaifiyarsa kanwar Abba ne Kuma shi kadai suka Haifa, ya girma a London gun kanwar mahaifinsa, wacce take aure acan, tun Yana dan shekara shida ta tafi da shi, ke da shi baku San juna ba, Amma yayanki salihu ya Sansa sosai, domin kuwa tare sukayi wasan kasa.
  Don haka ki tashi ki gyara fuskarki kizo mu wuce,  domin yau duk dangi zasu zo tarbarsa.
  Bayan Salma ta gama shiryawa ta fito ta same kowa acikin mota, dama ita kadai ake jira Tana shiga,Direba yayi Reverse suka bar harabar gidan Sai Airport da ke birnin tarayya Abuja.
   Ahanyarsu ta zuwa Airport wayar Mami tayi Kara, Tana daukawa tace " Assalamu alaikum". Bayan ta gama wayar tayi tsaki mtswww!
Abba ya juyo ya ce lafiya ke Kuma da wa?
Ta sakeyin tsaki, sannan tace Ali Dan Allah Kai mu can Asokoro gidansu Alhaji Basheer ( Abban Saleem).
Yace to hajiya, sannan ya juya akalan motar.
Abba yace sa'adatu lafiya kikace mu tafi can?
Tace yanzu hajiya Khadija ( ummin Saleem) ta Kira ni tace wai har Saleem din ya iso, wai idan bamu tafi can airport din ba, to mu taho Nan gida, domin yanzu ma ya shigo.
Tace ai ba don mun tsaya jiran wannan Shashashar yarinyar Nan ba ai da ni ce zan Fara taran  da na, wallahi da nasan Haka wannan Yar banzar zatayi wallahi da mun wuce, cikin 6acin Rai take magana.
Abba dai shuru yayi domin ko shi abin ya 6ata Masa rai.
  Zainab da Ali Direba Sai hakuri suka basu.
Salma kuwa kuka takeyi Amma acikin zuciyarta takeyi, sabida tayi wa Anti zainab alkawarin bazata Kara yin kuka ba.
   Karfe goma daidai suka Isa
Ummi ta dubi Salma dake zaune gefen Mami ita da zainab.
Tace Salma kwana biyu kin guje mu bakya ko dan laiko mu, ko mun Miki laifi ne? Eyeh?
  Salma tayi kasa da kanta Tana wasa da zoben  hannunta.
Mami tace Taya ko Zaki ganta, Tana can tasa wa ranta damuwa, akan abinda akace har ta mutu ba zata taba samunsa ba, har Abadan kuwa!
Ummi tace ke! Salma Daman Baki bar yaron Nan bako? Wai ke wata irin yarinya ce? Nan ta shiga fada in da take shiga ba ta Nan take fita ba,Kuma Daman ita masifeffiya ce.
Haka suka hadu ita da Mami suka  sata agaba suna tayin Mata fada, har suka gaji don kansu suka yi shuru.
Salma da kuka yake son kubce Mata tayi saurin barin gunsu tayi cikin dakin Ummi, ta fada kan gado tayi rub da ciki, wannan lokacin kuka ne sosai ya kwace Mata.
   Ranan tayi kuka kamar ranta zai fita, ahaka har baccin wahala ya kwasheta.
   Zainab kuwa tun da suka Fara fadansu ta tashi ta nufi balcony tayi zamanta sabida ba zata ita ci gaba da zama ba, sabida Salma Tana Bata muguwar tausayi sosai.
  Aranta tace oh! Ni Abu, Allah na roke ka da kayi gaggawan kawa mafita ga yaran nan Kuma ka tona Asirin duk Wanda ke da hannu acikin wannan lamarin.
   Wai ace lokaci daya Aminan juna sosai kamar Alhaji sudais da Alhaji sultan sun zama Makita!.
Amma abin Nan da daurin Kai, wai ma menene silar wannan lamarin.
Ta Soma share hawayenta da gefen gyalenta. Daidai lokacin da Mami ke kwalla Mata Kira.
Karfe hudu daidai Salma ta tashi daga bacci,ta shiga toilet tayi Alwala tayi sallah
   Bayan ta idar ne Sai ta tsince kanta da son yin kwalliya.
Ta dauko handbag dinta, ta fito da kayan kwalliyarta.
Ta gama kwalliya kenan Ummi ta shigo tace Salma har kin tashi daga baccin? Tace eh ummi, Ina yini? Lafiya Lau salma.
Yawwa Salma Dan Allah ki dauki wa'ancan Bedsheets din ki Kai dakin Saleem, daki na uku shine nasa kinji Koh? Tace to Ummi .
Ta kwashe kayan kwalliyarta ta saka a handbag dinta, sannan ta nufi gun da Bedsheets din suke, Tana dagawa suka watse akasa.
Nan ta shiga gyarasu yanda zai Mata dadin dauka, Tana cikin gyarawa zobanta ya Fadi acikin bedsheets ba tare da ta lura ba.
Tayi sallama tare da turo kofar dakin
Yana zaune akan kujeran da ke cikin falon hannunsa rike da iPad dinsa Yana buga Game din Talking Tom GoldRun.
Sassanyan kamshin pure love ya tsirga har cikin kansa.
Da sauri ya dago ido ya dube ta, ya Dan Kara juyowa sosai ya kalli yarinyar don ada yayi zaton idonsa ne bai gani sosai ba, yace Dan Allah baiwar Allah daga Ina?
Tace Ummi ce tace na kawo maka bedsheets.
Yace okay Amma Dan Allah meye sunanki, Kuma waya Baki irin perfume Dina?
Murmushi tayi sannan tace Ina yini, Yaya Saleem? Lafiya Lau baiwar Allah.
Ta sakeyin murmushi,tace sunana Salma .m. Sudais TakaiKuma kanwar Yaya salihu.
Yace oh! Daman ke ce Salman da aka Haifa bayan tafiya ta London, kice min kece Yar Autar Mami da Kuma uncle Sudais.
"Wow" kin girma fa, yanzu Sai aure Koh? To Allah ya tabbatar da mafi alkhairi. Ameen
Kunya CE ta kamata, ta rufe fuskarta Ajikin bedsheets din dake hannunta sannan ta dago da kanta , Ina zan ajiye maka su.
Ta fada ba tare da ta daina murmushin da ke like atattausar fatar bakinta ba.
Yace aduk in da yayi miki, toh ki ajiye agun, kinji Koh Autarmu
Tace to, toilet yayi min, a Nan zan ajiye.
Ya tabe bakinsa tare da daga kafadunsa sama, yace okay ooo! As u wish, suka kyalkyale da dariya alokaci guda. Sannan ta bude wadrup dinsa ta ajiye aciki, tayi Masa sallama ta wuce.
Ba don yaso ba, ta wuce. Nan ya koma ya zauna a inda yake zaune da farko, yaci gaba da Game dinsa.
Haka Nan yaji Game din ya gundireshi ya rasa gane kansa, ya kasa gane meke damunsa.
Gaba daya ya tattaro hankalinsa da tunaninsa wuri daya. Ya zubawa tafin hannunshi ido, ahankali Kuma ya Kai shi hancinsa tare da lumshe idanuwansa, still kamshin pure love din Salma Yana Nan adakin bai gushe ba.
Duk da cewa Yana kan gabar kuruciyarsa, Kuma akan matakin da babu macen da ba zata so shi ba, ta fa ba ko wacce mace yake kallo da kima ba har ya taba yiwa kansa Sha'awar aurenta, Mata iri_iri Kam yayi mu'amala da su tun zamanin Yana karatu, don shi bai yarda Yana neman yarinya wani ma Yana nemanta ba, daga Ranar da ya gane hakan duk son da yake Mata ya barta kenan har abada.
Ya lumshe ido ahankali ya koma ya jingina da kujera, can Kuma kamar an tsugole shi ya tashi ya shiga toilet, Sai da yayi wanka ya Shirya ya fito falo ya Sami Ummi ita kadai ne afalon.
Ya rungumeta ta baya ya daura Kai bisa kafadunta yace, Ummina I'm really missing you... Tace son ya hanya?
Yace lafiya Lau Ummi, Ina mutanin gidan na ganki ke kadai.
Tayi murmushi tace kowa ya Kama gabansa, Abbanka Kuma dazun ya tafi Gombe.
  Yace Allah ya dawo da su lafiya , tace Ameen.
Yace Ummi dazun Naga Yar Autar uncle Sudais ta girma, wallahi girman 'ya mace ba wuya yanzu yanzun Nan zakiji ana batun Auranta.
   Ummi tace to Sai me in anyi, Kai dai ba kaki kayi ba, domin kana min bakin cikin ganin jikoki da tattaba kunne, yanzu fisabidillahi shekarunka nawa? Talatin da biyar fa, Amma ko maganar aure ma bakayi.
Ga salihu Nan har yayi auransa yanzuma matarsa Tana da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe.
  Haka ma mommynka na can London ke fama da Kai? Nan dai ta shiga yin Masa fada tare da nasiha.
  Bai ce komai ba har ta gaji don kanta tayi shiru.
Yace Ummi kiyi hakuri inshaa Allah kwanan Nan zan gabatar Miki da wacce zan aura.
Tace Ameen, Allah dai yasa ba zakin Baki kake min ba.
Yace no! Ummi na taba Miki wannan irin maganan ko da wasa tace a'a Amma ban sani ba ko yau ka Fara, yace never! Suka yi dariya abinsu.
  Salma na kwance agadonta cikin bargo kanta ke ciwo tare da zazzabi zazzabi sosai Amma ta Dan janye bargon ta Dan fiddo da fuskarta idanunta duk sun kankance sunyi jawur Alamun ciwon Kai Mai zafi.
Tun da suka dawo daga gidans Saleem, ta duba zobanta bata gani ba, ta wargaza kayan dakinta dukka Amma Bata gani ba, Anan take zazzabi ya rufe ta.
Domin Rashin zoben Nan daidai yake da Rashin kwanciyar hankalinta, domin shi kadai ne yake dauke Mata kewar Husby dinta .
   Yau kwananta hudu kenan Tana kwance, Sai zancen zuci take, can take tuna ko dai ta Yar da zobenta gidansu Yaya Saleem ne? Tana kaiwa Nan atunaninta, ta tashi ta fizgi gyalenta da handbag dinta tayi waje da gudu sabida sauri ma ko mota Bata tsaya dauka ba tayi tafiyarta, Sai da ta fita har can bakin titi kafin ta dauki drop din taxi ya kai ta har gidansu saleem, ta biya shi sannan ta shiga cikin gidan.
Masu aikin gidan nata gaisheta Amma Bata amsa ba ita dai burinta Tana shiga ta ga zobanta.
   Dakin Ummi ta Fara zuwa, Ummi Tana sallah Azuhur, Sai kawai ta nufi dakin Saleem, Tana shiga ta same shi Yana kwance akan kujera.
   Kamshin pure love ne yafara dakan hancinsa daga bisani Kuma yaji muryarta me Kama da anbusa sarewa tayi sallama.
Ya amsa tare da dagowa daga kwanciyar da yayi.
Tace Dan Allah Yaya Saleem baka ga wata zobe anan ba?
Yace a'a Amma Sai dai in Zaki duba cikin bedsheets din da kika ajiye!
  Nan ta shiga dubawa Yana tayata, ta saukar da bedsheets din Tana dubawa daya bayan daya Shima Haka Saleem din, bedsheet na karshe ne Wanda Kuma zoben aciki yake shine Saleem ya dauko Amma bai gani ba, sabida lokacin da ya dauko bedsheet din bai lura ba, zoben ya Fadi akarkashin gadonsa, sun gama dubawa kaf! Basu gani ba.
    Hankalin Salma yakai kololuwa wurin tashi, domin Alan zoben Nan daf take da kwanciya agadon Asibiti.
  Saleem yace kiyi hakuri Autarmu, nayi Miki Alkawarin da zarar nadawo zansa ayi min kwalimar dakin Nan sabida zobenki kinji Koh!
Abinda ma bance Miki yau ba sabida Nan da awa daya da Rabi zan koma London, sabida wani Kiran gaggawa da aka min.
Duk da Haka hankalinta bai kwanta ba.
Ya kamo hannayenta ya zaunar da ita akan kujera, suna facing juna, yace kiyi hakuri.
Ta dago kanta ta dubeshi idonta cike da kwalla tace Dan Allah Yaya Saleem ka taimakeni wallahi idan na rasa wannan zoban to wallahi zan iya rasa rayuwata. Please!!
Yayi ajiyar zuciya sannan yace wacce iri ce zoben?
   Tace na gold ne Yana dauke da tambarin S$S love.
   Sai da gabansa ya Fadi menene meaning dinsa?
   Tace SALMAN and SALMA SO.
Nan ma Sai da gabansa ya sake faduwa, yace okay bakomai,
Nan tayi Masa sallama ta wuce kowa da abinda ke Ransa.
Tana fita ko takan Ummi Bata bi ba tayi wucewarta gida.
Saleem ya fito zuwa dakin Ummi yace Ummina wurinki nazo!
  Tace to Bismillah,samu wuri ka zauna Koh!
Yace Ummi Daman nazo ne, Ina son na Miki wata Yar tambaya Akan Salma.
Ta kalleshi tace me Kuma ya samu Salman?.
Yace Daman dazun ne Salma ta shigo dakina,wai Tana niman zobenta na Gold!
Tayi saurin dago kanta tace wani iri zoben Kuma ta ganshi kuwa?
Yace Ummi lafiya kuwa, Naga kamar hankalinki ya tashi daga jin na ambace sunan zobe,
Tace ni dai ka ban amsata ta gan shi?
Cike da mamaki yake kallon Umminsa, yace zoban na Gold ne me dauke da harafin S$S love
Ai Bata San lokacin da tace innalillahi wa Inna ilaihir rajiun!
Ta koma da baya turuss! Ta jingina da jikin kujera.
Tace Saleem bakayi min adalci ba da ka bar Salma ta tafi acikin wannan halin.
Da ka fadamin wallahi da ban barta ta tafi, yanzu Allah kadai yasan halin da take ciki, gashi ba'a motar gida ta zo ba,ohh! Allah na rokeka da ka kare min 'yata aduk halin da take ciki, Ameen ya Allah.
Hawayen da Saleem ya gani a idon Umminsa ne ya Kara tada Masa da hankali sosai, yace Ummi! Ni fa Kun saka ni acikin duhu fa?
   Ummi ta kalleshi tace Saleem!
Ya kalleta batare da yace komai ba.
Tace batan zoben Nan daidai yake da tarwatsa kwanciyar hankalin Salma, domin zoben Nan shine ke taimaka Mata wajen Rage Mata kewar Salman.
   Nan ta shiga fadamasa Rayuwar su Salma da salman, sannan tace lokacin da Salman yaje Egypt yasa aka Masa zoben Gold Wanda yasa aka Mai da harafin farkon sunansu.
Ranar da ya dawo yaba kowa tsarabarsa Sai ba'a ga na Salma ba, nace Masa a'a Salman Ina na Yar gidanka?
Sai kawai yayi dariya yace Ummi me kukeci ne na baka na zuba!
Mukayi dariya dukkanmu bayan anyi shiru Sai ya Ciro Yar karamar akwati daga Aljuhunsa yace kowa ya ga abinda na siyowa wifey dinna.

SHI NE MIJINAWhere stories live. Discover now