Bismillahi Rahman Rahim.
DUHUN ZUCIYA 2021
SHAFI NA ƊAYA
Pharty BB
Wattpad PhartyBB...
'Ina ma ni ce a wannan yanayi da lokacin? Ina ma duniyata zai canza zuwa ga mafarkina? Duhun da yake kewaye ya gushe ya zamto haske. Koyaushe zan samu haske? Wa zai cire ni daga duhun da yake lulluɓe da zuciyata?
Tsawon lokaci hasken cikin rayuwata ya gushe. Ko wacce rana ina tsumayin wanda zai haskaka duniyata.'"Radiyya! Radiyya!!"
Sunan da ya shiga kunnuwanta cike da karaɗi da amo ya sa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta tsunduma kanta.
Firgigit Radiyya ta amsa tana duban wacce ta ƙirata tare da faɗin.
"Ki ka ce me?"Ba ta damu da yanayin da take ciki ba. Kullum uzurinta shi ne a gaba da rayuwar wani. Ba ta duba da rayuwar wani na kusa balle ta fahimci halin da ya ke ciki.
Mugun kallo take watsa mata, duk da ta sunkuyar kanta ƙasa balle ta hango.Kalmar da ya fara fitowa daga bakinta shi ne.
"Ubanki na ce! Kin saka mini ido kamar mayya! Cinye ni za ki yi?"
Kai Radiyya ta girgiza tana matsawa baya don kar ta taɓa lafiyar jikinta, tasan zai iya biyowa baya bayan zagi.
"Ƙarfe biyu ki tabbatar kina ƙofar makarantar su Walid, kar ki yarda ki bar mini yaro yana jira. Sannan Uncle Nasir zai dawo ƙarfe uku ki ba shi abinci, na tafi gidan sunan Farida, zan kai ƙarfe shida ko bayan magriba Uncle Nasir zai ɗauko ni."
Daga haka ba ta jira ko Radiyya ta ƙara magana ɗaya ba ta ɗauki jakarta ta fice a falon.
A sanyaye Radiyya ta miƙe ta koma ɗakinta har da saka mukulli a ƙofar, bakin katifarta a saman gado ta zauna tana zuba tagumi, a hankali wasu siraran hawaye masu zafi suka zubo mata, nata rayuwar take tunawa da babu jiƙo balle samun ƴan ci.
Gajiya ta yi da zaman ta zame ta kwanta nan ƙasa ɗakin don jiran lokaci ya yi, ta riga ta gama ayyukanta na safe da rana gaba ɗaya na gidan, babu abin da ya rage sai abubuwan da ba za a rasa ba.
Barci ya fara fisgarta ta ji bugun ƙofa tare da ƙiran sunanta a hankali kamar koyaushe, a firgice ta miƙe tana tattaro hijabinta ta miƙe tsaye cikin mugun kiɗimewa, jin muryar mai ƙiran ya haddasa mata tsoro bayan wanda kullum take ciki.Daga can waje ta ji an dakata da bugun ƙofar a hankali aka ce.
"Buɗe ƙofar Radiyya, don Allah ki buɗe mini ƙofar nan yau kaɗai."
"Bazan buɗe ba."
Ta samu kanta da faɗa cikin kukan da ya ke neman kwace mata, kafin ta ƙara sauraran maganar da zai biyo baya da gudu ta kwasa ta shiga cikin bathroom(bangida) ta kulle kanta. Tana jin ana buga ƙofar da ƙarfi wanda dai dai yake bugun da bugun zuciyarta.
Kuka ta fashe da shi tana durƙushewa nan ƙasar bangidan.'Ina zan sa ka rayuwata da wannan masifar!"
Ta furta haka cikin kuka tamkar wani take faɗawa abun da ya ke faruwa da ita a kowane rana, cikin firgici da tsoro take.
Kuka ta ci gaba da yi na tsawon lokaci har ta ji an daina bugun ƙofar, a hankali ta miƙe ta nufi wajen wanke baki, fuskarta ta wanke sannan ta fito cikin sanɗa a bangidan, numfashi ta sauƙe ganin babu kowa kuma da alama an bar ƙofar ɗakin, kasa zama ta yi saman gadon a hankali ta sulale ta zauna tana jingina jikinta jikin gadon tare da ɗaura kanta saman katifar da yake kewaye saman gadon. Idanuwanta ta lumshe wanda suka bawa siraran hawayen da ya taru damar zuba bisa kyakkyawar fuskarta. Ba ta damu ta share su ba domin a kowacce rana tana zubar da irin su babu adadi.
Rayuwarta kawai take tunawa da irin yanayin da ta tsinci kanta a matsayinta na ƴa mace mai ƙarancin shekaru. Ba ta da inuwar da za tasa kanta domin samun sauƙi daga zafin da take ji, kullum gani take tamkar rayuwarta a juye yake tafiya, ba ta da gabas balle yamma, duhu ne kewaye a zuciyarta da babu haske ko kaɗan wanda zai haskaka mata samun mafita ko hanya, ire ren tunanin da ta ke jefa kanta a ciki kullum da zaran ta samu kaɗaicewa ita ɗaya.
Alarm ɗin da ya buga ne ya sata firgita a mugun tsorace, kyawawan idanunta farare ta fara zarewa tare da jujjuya kanta tana neman inda ta ji ƙarar, can ƙarshen gado ta hango, da sauri ta miƙe ta isa gurin tana ɗauka, kashewa ta yi kafin ta duba lokaci ta ga ɗaya har ya kusa gotawa, a hanzarce ta buɗe dirowar gefen gadon ta ɗauki ƙaramar jakanta da kuɗi yake ciki ta doshi ƙofar fita, sai da ta murɗa hannun ƙofar ta tuna dalilin da ya sa ta kulle, tsoro ne ya ƙara ziyartan zuciyarta ta dakata, ga
lokaci yana tafiya, ta kusa mintuna biyar tsaye tana karanta duk addu'ar da ya zo bakinta na neman tsari da sharrin mutun da shaiɗan, wani sanyi da ƙarfin guiwa ne ya ratsata kafin ta buɗe ƙofar a hankali ta leƙa kanta cikin falon, babu kowa hakan ya sa ta fice da sauri a ɗakin ta sawa ƙofarta mukulli, tana sawa ta juya ta nufi hanyar fita a falon.
Ta isa tsakiyar falon ta ji maganar da ya kusa sa ta yin tuntuɓe tsabar tsorata.
YOU ARE READING
DUHUN ZUCIYA
RomanceZuciya na duhu ta zamto kurman dutsen da ke tsakanin sahara, zafin rana na ratsa shi, turirin sahara na turara shi. Wannan shi ne kwatan-kwacin misalin da ke tsakanin wanda ya rasa kulawa da ƙauna ga makusantansa. Tsana ta ma ye wajen soyayya, has...