DUHUN ZUCIYA
Babi NA Takwas
Pharty BB
Wattpad PhartyBBHar ta tsaya a ƙofar gidan ba ta ga alamun abin da ta faɗa mata ba ko kaɗan, hasalima unguwar shuru yau ko don azumi ne. Ƙoƙonto ne ya fara ziyartar zuciyarta akan ba ƙarya ta mata ba kuwa. Buɗewar ƙaramin ƙofar jikin get ɗin ne ya sa ta juyawa ta ga Mai Gadi ne.
"Mama sannu da zuwa bismillah."
Ya faɗa mata yana ba ta hanya ta shiga tana amsa masa. Kai tsaye falon gidan ta nufa, nan ma sai da ta ƙwanƙwass sannan aka buɗe. Aunti Mimi ce daga ita sai doguwar riga na barci, da alama farkawarta daga barci kenan."Umma ke ce da sassafe haka?"
Mimi ta ce cike da mamakin ganin mahaifiyarta a wannan lokaci."Zan iya shiga ko na juya?"
Ta ce tana bin ta da kallon mamaki."Shigo ciki."
Ta faɗa tana matsawa Umma ta shige cikin falon. Turus ta yi ganin falon sama da ƙasa tamkar matsugunnin taɓeɓɓiya. Juyawa ta yi ta kalli Mimi da take susan kai lokaci ɗaya hamma ya taho mata ta buɗe baki, babu shiri Umma ta kawar kanta tamkar ta yi amai. Guri ta samu ta zauna saman kujerun falon da duk sun koɗe a ƙanƙanin lokaci. Ganin haka Mimi ta zauna ita ma."Mimi me zan gani! Ƙazanta?"
Shi ne abin da Umma ta fara faɗa mata kenan. Rai Mimi ta haɗa don ta tsani faɗar Umman su, sam ba ta da daɗin sha'ani."Magana nake miki Mimi. Yanzu ba wannan ba, babu labari shuru?"
"Labarin me kuma Umma?"
Mimi ta tambayeta tamkar ba ta fahimci inda maganar ya dosa ba.Sake zama Umma ta gyara tana sassauta murya.
"Kayan arziƙi da yaron nan yake mana duk ƙarshen wata, ga kuma sallah sai gabatowa yake.""Umma kenan, ku ƙara ba shi lokaci, akwai wasu ayyuka da ya sa a gaba ne."
"Amma Mimi shi ne har yanzu shuru? Ko dai ba shi da niyar ne bana?"
Ɓata rai Mimi ta ɓata ta ce.
"Umma na sha masa maganar ya ƙi wallahi, ƙarshe da na dame sa ya ce ba zai yi komai ba, dalilin haka har bama magana."
A razane Umma ta ce.
"Kul! Hauka ki ke!! Idan ki ka ɓata masa rai ya zamto aurenki ya samu matsala ina za ki je? Kin san mu ma ƙarƙashin ku muke ci, albarkacin ki. To a hir, ki sasanta da mijinki ko hakan zai sa ya fasa niyar ƙin yi.""To Umma."
Mimi ta ce tana tuna rigimar su da Uncle Nasir.
Tun da sallah ya rage saura kwana goma sun kasa jituwa da juna. Faɗar yau daban gobe daban, ban da wanda suka gama kwanakin baya kan ƙazanta da take yi. Ba ta girki kullum sai ansha ruwa ya sayo, ba ta abincin sahur sai dai su sha shayi da biredi, gyaran gidan kuwa sai ta bushi iska.
Yau musamman ta samesa akan maganar kayan sallar iyayenta da yake siya musu kowanne sallah, da kayan abinci da yake siya kowacce ƙarshen wata. Kai tsaye buɗar bakinsa ba shi da kuɗi ya ce, da ta damesa ya ce ba zai siya ba. Hakan ya sa ta ɗauke masa wuta a gidan tun safe har dare tsammaninta idan ta yi fushi zai siya, ba ta san ta hutar da shi ba ne. Kyautatawar da yake don ya samu abin da yake muradi ne, yanzu kuma babu wa zai kyautata.
YOU ARE READING
DUHUN ZUCIYA
RomanceZuciya na duhu ta zamto kurman dutsen da ke tsakanin sahara, zafin rana na ratsa shi, turirin sahara na turara shi. Wannan shi ne kwatan-kwacin misalin da ke tsakanin wanda ya rasa kulawa da ƙauna ga makusantansa. Tsana ta ma ye wajen soyayya, has...