BABI NA HUƊU

308 21 5
                                    

DUHUN ZUCIYA

Babi NA Huɗu

Pharty BB
Wattpad PhartyBB

Ruwan hawaye ne ya taru a idanuwan Radiyya, dama ta san da ƙyar su yarda da barinta ta zauna. Ba ta da amsar da zata ba su, tsoron sanar da gaskiya take su ƙi yarda.
Sauƙar dukan da ta ji a haɓarta ya sa ta dawowa daga duniyar da ta faɗa.

"Don ubanki ba tambayar ki ake ba! Me ya kawo ki?"
Faɗin Umma a zafafe, sanyin halin Radiyya yana ba ta haushi, sam yarinyar ba ta da zafi kamar ita ko Mimi.

Radiyya hawayen da suka zubo mata a fuska tasa hannu ta share, cikin rawar murya ta ce.
"Baba zan zauna ne anan in yi azumi."

"Ita Auntinki ta yarda ne? Ko Nasir ɗin?"
Baba Ƙarami ya sake mata wani tambayar.

Girgiza kai ta yi wani hawayen yana zuba mata, wannan lokacin ba ta share ba ta ce.
"Ni kawai na zo ne. Don Allah kar ku ce in koma, ku barni na zauna tare da ku."
Ta ƙarasa maganar cike da alamar roƙo. Idan suka ce ta koma gidan nan mai cike da duhun da ya shafi zuciyarta tabbas za ayi ɗayan biyu.

Umma da ta hasala ta nuna Radiyya da yatsa.

"To don ubanki sai kin koma yanzu ba gobe ba. Ina zan iya miki ga ni ga ke."

Fashewa da kuka Radiyya ta yi ta rarrafa wajen Baba Ƙarami.
"Don Allah Baba ka sa baki Umma ta barni na zauna anan."

"Kin san zaman gidan nan Radiyya?"
Tambayar da Kawu ya mata kenan ganin tamkar tafi son hakan. Ga inda za ta ci mai kyau, ta sha mai kyau, ta kwana a guri mai kyau, amma ta zaɓi tahowa inda ci ma yana gagaran su balle wasu abubuwan.

Umma jin abin da ya faɗa ya sa ta ƙara hasala ta kalli Baba Ƙarami ta ce.
"Ba za ta zauna ba fa Malam."

Radiyya cikin kukan da take jin zafinsa har cikin ranta ta ce.
"Umma zan riƙe kai na, idan dai don ci da sha ne. Ku bani gurin kwana kawai ya wadatar."

"Tashi ki j Radiyyae."
Faɗin Baba Ƙarami ya dubi Umma da ta haɗa rai sosai. Cikin lallami ya ce.

"Ki barta ta zauna a gurinki Zuhra tun da ta amince. Abinci ba zai gagari a bata ba idan an dafa, sauraran abubuwan kuwa ta iya wa kanta, idan kuma za ki iya mata to shikenan. Ita kuma Mimin idan ta biyo sawu sai a sanar mata, daga nan mu ji dalilin tahowarta tun da ta ƙi sanar mana."

Umma ba ta jira mai zai ƙara ba ta fice ranta ɓace. Ɗaki kai tsaye ta wuce ta samu Radiyya zaune ta buga uban tagumi. Daga alama tunanin sabuwar rayuwa da za ta fara take. Gida mai cike da mutane kala-kala, kowa rayuwarsa yake da yaransa, tsakanin su da Mai Gidan ciyarwa, shi ma sai ya nemo da ƙyar a sana'arsa na Dukanci. Shi ya sa a gidan kowa rabi shi yake rike da kansa da yaransa.

Ko kulata Umma ba tayi ba, aikin da za ta yi na wanki ta tattaro ta watsawa Radiyya a fuska. A firgice ta ankara da haka, sai lokacin ta dawo hankalinta ta fara tattare kayan tana kallon Umma da take kunce bakin ɗaurin zanin jikinta, duk ya mutu ya tsufa. Tana kallo ta ciro canji canji na kuɗi da idan aka haɗa ba zai wuce dubu ɗaya ba, ɗari biyu ta ware ciki ta mayar sauran ta kulle sannan ta kalli Radiyya da take ta kallon mahaifiyar nata.

"Ga shi ki siyo omo da sabulu na ɗari da hamsin, ki zo ki min wanki tun da Allah ya kawoki."

Babu musu Radiyya tasa hannu ta karɓi kuɗin da Umma take miƙa mata, sannan ta miƙe tsaye. Har ta kai bakin ƙofa ta tsaya, sai dai ta kasa faɗin abun da ke ranta har sai da Umma ta tambayeta.

DUHUN ZUCIYAWhere stories live. Discover now