DUHUN ZUCIYA
Babi Na Tara
Pharty BB
Wattpad PhartyBBTsawon sati ɗaya kenan Radiyya tana hutu, ba wai don ta gaji ba ne sai don ganin tamkar tsoro take ta yi ta rasa masu saya, sai dai abin mamaki tun sallah da ya wuce da sati biyu da kwana uku aka fara nema, an turo yara kusan sau biyar zuwa shida babu, hakan ya sa yau ta tashi da niyar yi.
...
Tun kwanakin sallah hidima da fama da jama'a ya hanasa zama, har yau da ana neman cinye sati biyu ya samu hutu. Tun safen bai fita ba yana kwance a gida don hutu, barci yake tun da ya yi sallar azahar. Sai misalin ƙarfe huɗu da rabi ya farka, babu kowa a ɗakin kamar yadda ya buƙata da zai shiga don kwanciya, hakan ma kuma yanzu babu wanda ya shigo. Kai tsaye banɗakin dake cikin ɗakinsa ya shiga, haɗuwa iya haɗuwa ya yi tamkar ba za a mutu ba. Ruwa ya watsa ya ɗaura alwala sannan ya fito, kayan shan iska ya saka ya tada kabbara, sallah ya gabatar lokacin ƙarfe biyar saura. Bayan ya idar ya isa gaban mirror nasa da yake cike da kayan shafe-shafe da turaruka tamkar na mace, mai ya shafa lotion mai ƙamshi kafin ya bi jikinsa da turare ya feshe kusan kala uku, tuni ɗakin ya ɗauki ƙamshi, bayan ya gama ya fito zuwa falon gidan. A hankali yake taka matakalar benen, kallo ɗaya ba za ka iya wassafa shekarunsa ba saboda jin daɗi da kuɗi da ya zauna masa.
Tana zaune ta ji alamar motsi daga sama, kallonta ta kai gurin, ganin mijinta ya sa ta miƙewa da sauri ta nufesa fuskarta ɗauke da murmushi."Ka farka? Na leƙa sau biyu ka na barci."
Kallonta ya ci gaba da yi kamar yadda yake tun sauƙowarsa, ta yi kyau cikin shigar jikinta, jin abin da ta faɗa sai lokacin ya buɗe ba ki ya ce.
"Amma Fauzy kin san na hana hakan ko?""Na sani ka yi haƙuri. Gani na yi lokacin sallah zai wuce ne."
Matar da ya ƙira da Fauzy ta faɗa a ɗan sanyaye.Bai ƙara cewa komai ba ya nufi hanyar ƙofa, ganin haka ta bi bayansa.
"Abinci fa Alhaji.""Ba zan jima ba."
Haka kawai ya faɗa mata ya fice daga falon. A sanyaye ta dawo ta zauna, tun ɗazu take jiran farkawarsa domin su ci abincin rana tare. Tana son mijinta tamkar yadda yake sonta, tana kishinsa....
Kai tsaye wajen sana'arsa da ake masa ya biya ya dudduba da bai samu ya yi ba yau, komai daidai ƙarshe ya tsaya a gidan mai nasa da Sahabi yake aiki. Burinsa da muradinsa yau yasha daddaɗan zoɓon nan, ya yi kewa kwana da kwanaki, tun bayan sallah haƙuri yake kuma rashin zama ya hanasa zuwa. Tun da ya shigo yana raba idanu ta ina zai hangota, sai dai abin mamaki iya juye juyensa bai kalli ko kulolin ba balle ita. Ba shi da niyar sauƙa amma haka dole ya buɗe motar ya fito, da Sahabi ya fara cin karo da yake jiran saukowar ogansa. Da girmawa Sahabi ya gaishesa, bayan ya amsa ya yi shuru don rasa ta ina zai fara tambayarta, amma da ya tuna Sahabi nada masaniyar ƙaunarsa ga zoɓo, musamman nata da yake aikowa ya sa ya daure ya ce.
"Sahabi ina yarinyar nan mai siyar da zoɓo?"Sahabi jin Alhaji Shaheed da kansa ya kawo maganar da yake son masa ya sa shi da sauri faɗin.
"Ai Oga ta dai na fitowa.""Saboda me? Me ya faru?"
Alhaji Shaheed ya faɗa da saurinsa.Sahabi da mamaki ya kusa kashesa, mutumin da ya ce ana gama azumi ta tattara ta bar gurin baya son ƙazanta, amma tunawa da Alhaji ya zama shaƙiƙi ga son zoɓonta ya ce.
"Oga kai fa ka ce ka bata nan da bayan azumi, shi ne ta dai na zuwa. Amma ta ce za ta yi a gida, mai so ya je can ya siya. Idan kana so in karɓo maka."
YOU ARE READING
DUHUN ZUCIYA
RomanceZuciya na duhu ta zamto kurman dutsen da ke tsakanin sahara, zafin rana na ratsa shi, turirin sahara na turara shi. Wannan shi ne kwatan-kwacin misalin da ke tsakanin wanda ya rasa kulawa da ƙauna ga makusantansa. Tsana ta ma ye wajen soyayya, has...