DUHUN ZUCIYA
Babi Na Goma
Pharty BB
Wattpad PhartyBB.Kamar jiya haka yau ma ta samu ƙiran Alhaji Shaheed. Da farko kamar ba za ta fita ba, sai dai rashin ɗan aike yasa dolenta ta ɗauki hijabi, tare da sa gora uku a leda masu sanyi sosai kafin ta fita. A gurin da jiya ya yi parking anan ta sameshi, kallo ɗaya ta yi wa gurin ta sunkuyar kai tana ƙarasawa. Isowarta ya sa shi buɗe gilashin motar, tun fitowarta ya zuba mata idanuwansa yana ƙare mata kallo, anan ya hango ƙarancin shekarunta. Bayan ya buɗe gilashin Radiyya ta ɗago kai ta kalli gurinsa tana gaishesa. Amsawa ya yi yana miƙa hannayensa duka biyu, ɗaya kuɗinta ɗaya kuma alamar ta miƙo masa ledar hannunta. Babu musu ta miƙa suka yi musanye.
"Sai dai babu canji, kuma akwai sauran canjin jiya."
Ta faɗa ƙasa ƙasa kanta sunkuye."Don't worry. Keep it with you."
Ya faɗa yana zuge gilashin motar tare da ƙoƙarin barin gurin. Radiyya ta ɗan fahimci abin da ya faɗa saboda tana da sanin turanci kaɗan. Tana kallo ya bar gurin kafin ita ma ta koma cikin gida a sanyaya....
Cikin satin tana samun ƴan ciniki sosai, unguwar duk an gano Radiyya mai kunun Aya da zoɓo, musamman har bukin ake take ajiyewa mutane. Kamar yau abin tamkar a mafarki aka kawowa Radiyya kuɗin kunun Aya da zoɓo da za ta yi na suna. Ba ta karɓa ba sai da ta sanar da Umma. Da ƙyar ta samu yardarta don Umma ba wannan bane a gabanta. Burinta ta koma gidan Aunti Mimi tin da sallah ya wuce, amma daga Baban har Mimi babu wanda ya ƙara tayar da maganar, kuma dole ta tayar, don haka suka yi da Radiyya azumi za ta yi kaɗai ta koma.
Radiyya bayan ta karɓa aikin da aka bata ta wuce kasuwa, tare da Amrah suka je don taimaka mata, bayan sun gama siyayyar suka dawo. Suna dawowa sun huta wajen bayan azahar ta fara nata aikin don na sunan sai gobe. Ƙarfe huɗu da mintuna ta gama don tun ɗazu ana ta shigowa tambaya.
Kamar koyaushe haka yau ma Alhaji Shaheed ya yi tattaki ya taho zuwa ga Radiyya, gaisuwar mutunci suka yi kafin ta ba shi ya amsa ya biyata. Bai jira ta ƙara faɗin komai ba kamar kullum ya ja motarsa ya bar gurin.Washegari Radiyya tun safe ta fara aikin kunun Aya da zoɓo na sunan da aka kawo mata, da taimakon Amrah take yi, Amarya Zulaiha ta hana Amrah ƙiri-ƙiri amma yarinyar ta ƙi bari. Ba su gama ba har ƙarfe biyu kafin nan, a cikin manyan kulolin da suka kawo ta zuba musu ta jera. Ƙarfe biyu da rabi suka zo suka ɗauka sai godiya suke mata, ita ma ta yi murna don sun mata sallama mai tsoka.
Gajiyar da ta yi yau ya hanata yin nata sana'ar, tun wuri masu turo a musu bukin take sanar da su yau babu sai gobe, sam ta manta da oga kwata-kwata da shi ne ruwan shansa idan ya ci abinci, wani lokaci a firiji yake sawa ya kwana da safe ya yi breakfast da shi.
Ƙarfe uku ya masa a ƙofar gidan su saboda rashin zama da bai samu ba yau, tasowarsa zai wuce gida don hutawa ya ga gwara ya tsaya ya siya kafin ya wucen. Ƙiranta ya yi a waya kamar kullum.Radiyya na kwance ta yi ɗaiɗaiya a ɗakin Umma tana huta gajiya ta samu ƙiran wayar, sam ta manta da shi, jin ƙarar wayar ya haifar mata da fargaba, babu me ƙiranta sai shi a daidai wannan lokacin. A sanyaye ta miƙe ta ɗauki wayar, shi ɗin ne kuwa. Kasa ɗauka ta yi kawai ta zurma hijab ta fita. A gurin da ya saba tsayawa ta hango sabuwar motar da ya tsaya, canjin mota na uku kenan.
Bayan tsayuwarta ya sauƙe gilashin, murya ƙasa ƙasa Radiyya ta gaishesa, bayan ya amsa ya ƙara da faɗin.
"Da alama yau kin mini rowa.""Wallahi ban samu zama ba ne, ka yi haƙuri."
Ta samu kanta da furta haka.Murmushi ya yi da shi ne karo na farko da Radiyya ta gani a fuskarsa, sai ta ga ya mata kwarjini duk girmansa, dole ta sunkuyar kanta ƙasa.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
DUHUN ZUCIYA
RomantizmZuciya na duhu ta zamto kurman dutsen da ke tsakanin sahara, zafin rana na ratsa shi, turirin sahara na turara shi. Wannan shi ne kwatan-kwacin misalin da ke tsakanin wanda ya rasa kulawa da ƙauna ga makusantansa. Tsana ta ma ye wajen soyayya, has...