BABI NA SHA UKU

256 26 23
                                        

DUHUN ZUCIYA

Babi NA Sha Uku

Pharty BB
Wattpad PhartyBB

Tin daga ranar Alhaji Shaheed ya fara kyautata Radiyya da iyayenta, burinsa ya samu gurbi a zuƙatan su musamman ita Radiyyar da ya lura tana ganin girmansa. Tabbas haƙarsa ta cimma ruwa, domin duk girmansa hakan bai hana Radiyya sa shi cikin ranta ba, wani matsayi ta ba shi don dalilinsa ta fara ganin haske a rayuwarta, shi ne ya yaye mata duhun da zuciyarta yake ciki, ya haskaka mata rayuwa. Idan dai yana gari to kamar faɗin Allah kullum sai ya zo, a baya idan ya zo baya jimawa amma yanzu zai tsaya su gaisa, ba zai bar gurin ba sai ya sa ta dariya.

Ƴan gidan su Radiyya tuni suka fara janta a jiki. Umma duk abin da Radiyya ta samu sai ta ƙwace. A ɓoye Radiyya ta ci gaba da yin asusunta ba da sanin Umma ba.
Baba ɓangarensa shi ma yana jin daɗin sauyi da ya fara samu dalilin Radiyya, yunwar gidansa ya fara tafiya.
Sakwannin da ake turowa Radiyya an daina sai dai a ƙirata, idan ta ɗauka ba a magana sai dai ta gaji da sallama ta kashe wayar.
...

Aunti Mimi da Uncle Nasir har ya kai ya kawo sun fi sati basa magana, kullum yana cikin faɗa da zagi. Faɗar su na ƙarshe da ya shigo ya samu inda ta ci abinci ta bari ta shiga ɗaki ta kwanta, daga nan barci ya kwasheta. A hasale ya bankaɗa ƙofar ɗakinta ya shiga, wani baƙin ciki ne ya turnuƙesa ganinta kwance tana barci.
A tsawace ya tasheta ta hanyar ƙiran sunanta.
"Maimuna! Maimuna!!"

Cikin daddaɗan barcinta ta ji ƙiran. A firgice ta miƙe zaune, murza ido ta yi ganin waye a tsaye. Cikin muryar barci ta ce.
"Lafiya?"

"Au tambayana ki ke? Wani rin ƙazanta ne wannan? Me ya sa ke ƙazama ce? Radiyya ta fiki tsafta."

Jin sunan da ya ƙira ta hargitse ta miƙe tsaye.
"Wallahi ka fara ishena da sunan yarinyar nan. Me ya sa komai sai ita?"

"Saboda..."
Sai kuma ya yi shuru ya fasa faɗar abin da zai faɗa ya nufi ƙofa. Da sauri ta tare hanyar tana masa wani kallo.
"Saboda me ya sa? Ka bani amsa."

"Ba zan bayar ba. Bani hanya na wuce."
Yana faɗin haka ya fizgeta gefe ɗaya ya yi wucewarsa. Durƙushewa Mimi ta yi jin ƙafafunta sun kasa ɗaukarta, Allah ya sa dai ba abin da take tunani ba kenan.

...

Ɓangaren Hajiya Fauziyya yanzu lamuran mijinta ya fara wuce tunaninta, duk hanyar da za ta yi bincike ta kasa. Wannan jarababben zoɓon da yake sha ya fara isharta, kullum ba ya rabuwa da shi, duk juice ɗin zamani idan ta gani za ta yi amma wani lokacin ko kallo ba ya yi.  Dalilin haka ya sa yau ta zage ta shirya masa zoɓo da kanta, ƙamshinsa da daɗinsa tasan dole ne ma yau ya yaba, kuma ya haƙura da shan wanda yake siya.
Da yamma ƙarfe huɗu bayan ya dawo daga wajen Radiyya ya shigo falon. Da ledar hannunsa ta ci karo idanuwanta suka sauka akai. Miƙewa ta yi zuwa gareshi bayan ta katse wayar da take yi. Gurinsa ta nufa tana masa sannu da zuwa. Da fara'a kamar koyaushe ya amsa, daga haka suka wuce teburin cin abinci.
A babban plate ta zuba musu ta saka musu cokali, ba ta zauna ba ta wuce ta buɗe fridge ta ciro jug ɗin da zoɓon yake ciki, ya yi sanyi sosai sai gumi yake. Komawa ta yi gurin teburin ɗauke da shi, kofi ta ɗauka da yake saman teburin a jere ta zuba ta ajiye gefen mijinta, sai lokacin ta zauna ita ma tana faɗin.
"Yau dai ni ma nayi wannan zoɓon, sai ka hakura da na kasuwa."

Murmushi ya yi yana ci gaba da cin abincinsa, kamar ba zai ce komai ba can ya dakata bayan ya haɗiye abincin bakinsa ya ce.
"Wannan daɗinsa daban ne, ba na kasuwa ba ne."

DUHUN ZUCIYAWhere stories live. Discover now