BABI NA SHIDA

204 24 7
                                        

DUHUN ZUCIYA

Babi NA Shida

Pharty BB
Wattpad PhartyBB.

Da gudu ya tashi daga zaunen da yake ya taho wajen Radiyya cikin murna. Ta yi farin cikin ganinsa, hakan yasa ta buɗe masa hannuwanta ya shiga ta mayar ta rufe ta rumgumesa, ta yi kewarsa sosai, shi ɗin na musamman ne a gareta, sun yi sabo sun shaƙu, tun zuwansa duniya ya buɗe ido ya ganta, ta ya zai iya kwana ya wuni bai sa ta a idanuwansa ba.

"Kin ga ni ko Umma?"
Faɗin Mimi tana kai ƙosai bakinta. Idanuwan su gaba ɗaya akan Radiyya da Walid da suke rumgume da juna cike da farin ciki.

Umma da ta miƙewa don gabatar da sallah ta ce.
"Ban san me akan yarinyar nan ba? Ba dan Baban ku da ya ce in barta zuwa nan da azumi ba ko za ta canza ra'ayi, da babu abin da zai hana na sa ta dolenta ta koma."

"Yanzu ma Umma ta yi haƙuri ta koma don Allah."
Mimi ta ce har lokacin tana kallon Radiyya da Walid.

"Ga ki ga ita."

Daga haka Umma ta wuce ɗaki ta bar Mimi zaune. Tun karfe huɗu da rabi da ta gama haɗa kayan shan ruwa ta ɗauka ta taho gida, akan idan sun sha ruwa ta roƙi Radiyya su koma tare.
Zuwanta ta samu labari ta fita talla a bakin Umma, tun da ta ji ba ta nan take roƙar Umma, ta bi hanyar da duk za ta bi Radiyya ta koma gidanta. A fili ta nuna sun yi tsantsar kewarta da rashinta, cikin zuciyarta kuma ta gaji da wahalar aikin gida da hidimar Walid, ga Uncle ya fara canza mata motsi kaɗan faɗa, sai faɗin Radiyya ta fiki ka za, ta iya abu ka za. Dole yau ta yi tattaki ta zo roƙar Radiyya su koma, ko rayuwar aurenta zai gyaru.

Radiyya da suka saki juna ita da Walid ta ja shi suka yi alwala, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe da Aunti Mimi, abin mamaki da fara'a ta amsa mata, ruwa kawai Radiyya ta sha ta shiga ɗaki don gabatar da sallah, ganin haka Aunti Mimi bin bayan su ciki.
Umma ta idar tana lazimi, Radiyya da Walid tare suka gabatar da na su, Aunti Mimi ce ƙarshe, bayan ta idar ta dubi Radiyya.

"Yanzu ke haka bai fi miki ba. Ko ba ki yi kewar yaronki ba?"

Radiyya da tasan da ita Aunti Mimi take, murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce.
"Na yi Aunti."

"Ki bi ni mu koma mu ci gaba da rayuwar mu Radiyya. Ni ban san me muka miki ba lokaci ɗaya ki ka bijire mana? Ko kin manta tun tasowarki ki ke gabana, shekarunki goma sha biyu da haihuwa ki ke gurina, tun da na yi aure. Haifarki ne kawai ban yi ba Radiyya, amma alheri na miki daidai gwargwado."

Shuru Radiyya ta yi tana sauraran maganar Aunti Mimi, gefe ɗaya kuma tana tuna irin rayuwar da ta gudanar a gidan. Tun da ta fara mallakar hankalin kanta ita ce shara, wanke wanke, lokacin da ta haihu kuwa kula da yaron su tamkar ƴar raino ta zama, hatta ga mai gidan ita take kula da cin sa da wasu abubuwa. Tun da take a rayuwa ba ta taɓa jin inda Yaya ta mayar da ƙanwarta tamkar ƴar aiki ba sai a kanta. Duk abubuwan da take yi bai tsaya nan ba, bai gode ba mata ba sai lokaci ɗaya ta fara fuskantar mummunar farmaƙi daga wajensa, a matsayinsa na mijin yayarta.
Abu mai ɗumi ta ji yana bin kumatunta tasa hannu da sauri don tabbatar da menene, ruwa ta ji, ta ciro hannunta ta duba, nan tasan da hawaye ne ya zubo daga idanunta, ba ta san lokacin taruwar su ba balle zubar su, jin zuciyarta take yana zafi, wani tsanar su na shiga kowane ƙofa na jinin jikinta. Kallon Aunti Mimi ta yi da har lokacin haƙuri take bata me cike da gorin alherin da ta yi wa rayuwarta da mahaifiyar su, hatta da Baba Ƙarami da yake riƙe da su.

DUHUN ZUCIYAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن