BABI NA UKU

346 26 7
                                        

DUHUN ZUCIYA

Shafi Na Uku

Pharty BB
Wattpad PhartyBB

Murɗa hannun ƙofar ya yi tare da turawa lokaci guda, buɗewa ƙofar ya yi, wutar lantarkin ɗakin a kunne hakan shi ya ba shi damar hangota zaune a ƙasa ta ba ƙofar baya, kanta ta kwantar a kan gadon, duk zaton sa idonta biyu. Ƙofar ɗakin ya tura a hankali ya shiga sannan ya kulle har da sa mukulli.

'Yau ƙudiri na zai cika.'
Ya faɗa a ransa yana dumfararta cikin takun da babu sauti, har ya isa wajenta ya durƙusa saman guiwowinsa ba ta motsa ba. Leƙa fuskarta ya yi ya ga idonta rufe, anan ya ga barci take a hakan, murmushi ya yi ya miƙe tsaye, sai kuma ya duƙa ya ɗagota sama don kwantar da ita saman gado.

Wannan motsi da taɓata da aka yi shi ya farkar Radiyya daga barcin da ya kwasheta.

"Walid!"

Ta furta duk tsammaninta shi ne, sai kuma ta ji ana shirin yin sama da ita alamar ɗauka, ba ta faɗi abin da zai fito daga bakinta ba ta ji an kwantar da ita bisa gado.
'Mutum ɗaya ne zai min haka.'
Zuciyarta ya sanar mata da wannan saƙon. Take wani mugun tsoro ya ziyarci zuciyarta da ilahirin jikinta gaba ɗaya. Idanuwanta ta buɗe fes bisa fuskarshi, hasken lantarki ɗakin shi ya ba ta damar ganin shi.

Murmushi ya sakar mata, tare da ɗaura hannu ɗaya saman fuskarta ya shafa.

"Kyakkyawa."
Ya furta yana ƙoƙarin yin ƙasa da hannunsa zuwa wuyarta zai zare hijabin jikinta, kuma ya cukwuikuyeta ya hanata motsin kirki.

Fassara tashin hankali da Radiyya take ciki abu ne mai wuya a lokacin. Ji ta yi duniyarta da komai nata ya tsaya, kukan ma ta kasa sai bugun da zuciyarta yake tamkar zai faso kirjinta, magana kam yawun bakinta ya kafe balle ta samu furta wani abin.
Shurunta shi ya ba Uncle Nasir damar ci gaba da abin da yake mata, juyata ya fara son ransa har ya samu nasarar zare mata hijabi, da kallo ya bi kyakkyawar surar jikinta da shi, nan shaiɗan ya ci gaba da buga masa gangarsa.
Radiyya tana ji sannan tana gani ana neman rabata da mutuncinta da darajarta na ƴa mace, abu mafi ƙima a tare da ita, za ta rasa shi ta hanya mafi muni. Dukkan wani guntun ƙarfinta da jarumta ta tattaro ta sa hannuunta biyu ta ture sa, baya ya yi babu shiri don bai tsammaci haka ba. Ganin haka ta sake saka ƙafar damarta ta bugeshi inda ya sauka gefen cikinsa na hagu. Babu shiri Uncle Nasir ya saki ƙara tare da dafe cikin yana yin baya.
Hakan ya ba Radiyya damar miƙewa ta kwasa a guje sai bathroom,  mukulli tasa tana jingina jikin ƙofar. Zuciyarta ta dafe tana sauƙe numfashi domin wannan karon hawayen ya ƙi zuwa mata, kuka take son yi ko za ta ji sauƙin abin da take ji, tsoro da tashin hankali ya hanata tabuƙa komai, ganin abin Uncle Nasir take ya fara wuce rashin tausayi sai dai rashin tsoron Allah. Ba ta san lokacin da ta sulale ta zauna daɓas a ƙasa ba.

...

Iya wahala ya wahala don bai taɓa tsammanin haka daga gurinta ba, cikinsa riƙewa ya yi sosai sai fitar da numfashi yake yana haɗa zufa. Sai da ya samu nutsuwar hankali ya lura da Radiyya ta jima da barin gurin, tsaki ya buga ya miƙe da ƙyar yana dafe cikinsa ya fita, nan saman kujerun falon ya zube yanata juyi har barcin wahala ya kwashesa a gurin.

...

Radiyya wani abu mai suna barci ranar ba ta yi ba, yadda ta ga dare haka ta ga wayewar asuba, tana jin ƙiraye-ƙirayen sallar assalatu a hankali ta miƙe daga zaunen da take a rakuɓe. Alwala ta yi, ba ta yarda ta fito ba sai da ta leƙa ta tabbatar babu kowa ɗakin, dama tasan zuwa war haka ya fita. Cikin sauri ta fito ta nufi ƙofar ɗakin ta kulle da mukulli, sai lokacin ta ɗan ji nutsuwa ya shigeta. Hjabi ta ɗauka ta fara nafila, har aka fara sallar asuba sannan ta gabatar, ta jima tana addu'a akan Allah ya kawo mata mafita a rayuwarta sannan ta shafa.
Sai da haske ya fara haskaka ɗakin alamar rana yana fitowa kafin ta fita falon a tsorace, babu kowa ciki, hakan ya ba Radiyya damar fara gabatar da aikinta. Tana cikin haɗa breakfast Walid ya fito cikin kayan barci, kasancewar weekend ne babu makaranta kuma iyayen ba su yi ƙoƙarin sa shi makarantar islamiyya ba.

DUHUN ZUCIYAWhere stories live. Discover now