DUHUN ZUCIYA
Babi Na Sha Biyu
Pharty BB
Wattpad PhartyBB.Satin Alhaji Shaheed biyu a ƙasar Austaraliya kafin ya gama yin abin da ya kaishi. Tsawon kwanakin daurewa kawai yake, a daddafe ya tsaya aka gama abin da ya kai su. Ranar da za su dawo bai jira Kabir ba ko waɗanda suka haɗa tafiya tare ba, ƙarfe shida ya samesa a airport, jirgin ƙarfe bakwai ya tashi da shi zuwa Nigeria.
Sai da ya ganshi a cikin jirgi ya ɗaga da shi kafin hankalinsa ya kwanta. Murmushi ya sake tare da hamdala lokacin da jirgi ya sanar sun kusa sauƙa. Bayan saukar jirgin ya samu driver nasa ya iso ɗaukarsa. Driver yana kallon fitowar Alhaji Shaheed da sauri ya ƙarasa ya karɓi jakan hannunsa zuwa mota. Bayan ya saka ya zagaya ya shiga yana jan motar suka bar filin jirgin.
Tafe suke ya duba agogon hannunsa, yana da sauran lokaci da zai ishesa ya je gida kafin ya fita. Bayan isar su gidan sauka kawai ya yi ta wuce, driver shi ya fito da akwatinsa zuwa falo. Ya samu Hajiya Fauzy a falon ta yi kwalliyarta tana jiransa, murmushi ya akai mata ta mayar masa da amsa tana miƙewa.
Ganin ta taso kuma za ta ɓata masa lokaci ya sa ya nufi sama yana faɗin.
"Fauzy bari na watsa ruwa."Da mugun mamaki ta bisa da kallo, mutum da koyaushe ya yi tafiya ya dawo ita yake fara son gani, ita take taimaka masa ya yi komai, idan ba ta yi ba har fushi yake.
Har ya haura da sauri ya dawo baya tunawa da akwatinsa, hakan yasa ya sauƙo, lokacin kuwa driver ya shigo da shi, karɓa ya yi kafin ya wuce. Mamaki iya mamaki Hajiya Fauzy ta shiga, tamkar wacce ta ga abin almara haka ta bisa da kallo har ya ɓacewa ganinta.
Ruwa kawai Alhaji Shaheed ya watsa ya fito, ƙananan kaya ya saka masu fitar masa da siffan yarinta, masu ƙara masa kyau da kwarjini. Mayuka masu ƙamshi ya shafa da turare kafin ya fita zuwa falo, a nan ya sake samunta zaune. Tana kallonsa ta sake miƙewa, kafin ta ce wani abu ya rigata faɗin.
"Just 5mins Fauzy, yanzu zan dawo ba zan jima ba."Yana faɗar haka ya wuce zuwa ƙofar falon. Tana kallo ya fita ya barta tsaye, ba ta san yaushe ta zube dirshan saman kujera ba. Duk rashin zama da yake yi don yanayin sana'arsa bai taɓa mata haka ba a gida, yana bata dukkan kulawa na musamman.
...
Tafe yake yana murmushi shi ɗaya a cikin motar. Duk arziƙinsa abin da bai yarda ba da shi ne yawo da driver, a faɗinsa duk inda zai je sirrinsa ne, driver na aiken gida kawai ya ɗauka don Hajiya Fauzy wani lokaci, duk da ita ma ta iya motar.
Murmushin nan bai gushe a fuskarsa ba har sai da ya gansa ƙofar gidan su Radiyya. Agogon hannunsa ya kalla ya ga ƙarfe biyu da rabi, sai ya ga ya yi saurin zuwa, addu'arsa Allah ya sa ta yi. Tsawon sati biyu ji yake ya yi kewar zoɓonta, amma ƙasan ransa na hasaso masa ba zoɓon kaɗai ba hatta ita ɗin ya yi kewar gani. Nutsuwarta da shuru shurunta yana burgesa, sam ba ta da hayaniya daga yanayinta. Gani yake sam ba za ta yarda da buƙatarsa ba, sai dai ba daga nan take ba, domin shi ma Allah ne ya ɗaura masa don ya jarabci imaninsa.
Ganin yana ɓatawa kansa lokaci akan tunanin da ya fara damunsa kwana biyu akanta ya sa ya ciro wayarsa ya ƙira lambarta....
Radiyya na tsakiyar wanki ta samu ƙiran, ɗauraye hannunta ta yi ta nufi ɗaki, a ƙofa suka yi kiciɓus da Umma ta ɗauko wayar. Karɓa ta yi ta shiga ɗakin Umma kuma ta fita.
Sai da ta nutsu ta amsa ganin mai ƙiran. Duk da yana yawan faɗo mata rai har cikin ranta ta manta da shi yau. Bayan ta amsa da sallama ya sanar mata yana ƙofar gida, babu ɓata lokaci ta ce tana fitowa. Bayan ta kashe wayar ta miƙe, hijabi babba ta saka har ƙasa ta fita. Leda babba ta ɗauka ta buɗe firigi ta zuba masa zoɓo da kunan Aya da ardeb da ta fara, a faɗinta wannan hanyar kawai za tabi ta gode masa kyautar da ya mata.
Tana gamawa ta fita zuwa ƙofar gidan, cikin motarsa na farko da ta fara ganinsa cikin gidan mai da shi ya zo. Tun da ta fito ya zuba mata idanunsa da sun yi kewar ganinta, yayin da kunnuwansa suka yi begen sauraron daddaɗan muryarta, bakinsa ya yi rashin jin garɗin zoɓonta, zuciyarsa kuwa ita kanta ta yi kewa.
Isowarta ya ankarar da shi, a hankali ya zuge gilashin motar yana ci gaba da kallonta. Kallo ɗaya Radiyya ta masa ta sunkuyr tana gaishesa da masa ya hanya.
Murmushi mai kyau ya yi tamkar tana gani ya ce.
"Allahamdulillahi. Sai kewa."
YOU ARE READING
DUHUN ZUCIYA
RomanceZuciya na duhu ta zamto kurman dutsen da ke tsakanin sahara, zafin rana na ratsa shi, turirin sahara na turara shi. Wannan shi ne kwatan-kwacin misalin da ke tsakanin wanda ya rasa kulawa da ƙauna ga makusantansa. Tsana ta ma ye wajen soyayya, has...