BABI NA BIYAR

252 16 11
                                    

DUHUN ZUCIYA

Babi NA Biyar

Pharty BB

Wattpad PhartyBB

Ba ta taɓa tsammanin tana amfanuwa da ita ba sai yau tsawon kwanaki biyu, duk ta gaji ta yi da na sanin rashin lallashinta da ba ta yi ba ta dawo, sosai take wahala da ayyukan gida da kula da yaronta. Tun haihuwarsa ita take kula da shi, tsakanin su shayarwa. Ita ce cin sa, shan sa da komai nasa, ban da ɓangaren kula da gidan da tun da ta yi wayo ta sakamar mata ragama, hatta kula da mijinta ita ce.
Gidan a hargitse yake sosai ba za ka ce akwai mace a ciki ba, tun daga falo yake a hargitse har cikin kitchen. Kwanuka da abubuwan da ta yi amfani da shi tsawon kwanaki yana jibge babu wanki sai ƙudaje da suke bi.
Taƙaici da baƙin ciki ne turnuƙe a zuciyarsa, kallonta ya yi yadda ta yi ɗaiɗaiya a saman gadon, ta kasa ta shi ta gyara gidan, balle kanta balle maganar abinci, daren jiya ma siyowa ya yi don ƙin girkawa ta yi. Tsaki ya buga ya bar gaban madubin ya nufi ƙofa.

"Daddyn Walid!"
Ta faɗa da ƙarfi tana miƙewa ganin zai fice. Tsayawa ta yi a ƙofar a inda da ya tsaya yana binta da mugun kallo.
Kanta ta sosa tana yaƙe hakwara.
"Daddyn Walid ko za kaje gidan Umma ka taho da Radiyya. Sam gidan ya ka sa nutsuwa, dube ni dubi jikina, dalilin aikin gidan nan na kasa kimtsa kai na."

Numfashi ya sauƙe ganin ya samu damar haɗuwa da ita, damar da ya ke jira, dalili ɗaya da zai haɗa shi da ita, ya roƙeta ta dawo gidan. Kallon Mimi ya yi a karo na biyu.
"Anjima da yamma zan biya gidan."

Ƙoƙarin rumgumesa take ya ja baya, da sauri ya fice ya barta tsaye hangame da hannu.

...

Yau tun safe aikin surfe suke na hatsi, kayan azumi da maƙota suka raba kamar su hatsi, masara, shinkafa, suga, shi ne aka haɗa su ƴan matan da surfen wake da hatsi. Yara mata shida, yaran ɗakin Inna Saudatu Uku, yaran ɗakin amarya Zulaiha biyu sai Radiyya ita ɗaya. Kowanne hira suke a tsakanin su, ban da Radiyya da ta yi shuru sai aikinta take.
Sai gurin ƙarfe ɗaya suka gama, wanda za su iya wanka suka yi, wanda ba za su iya ba suka bari. Radiyya wanka ta yi ta ɗaura alwala ta ɗauki kwanon abincinta da Umma ta wuce ɗaki, kaya ta canza ta gabatar da sallah ta ci abincin ta kwanta nan saman sallayar, jin bayanta take tamkar ana sarawa tsabar gajiya, kwanciyarta ba ta jima ba barci ya ɗauketa.

Karfe huɗu Umma ta dawo daga gidan maƙota da ta shiga yin kitso, samun Radiyya ta yi rashe rashe tana barci, tayarta Umma ta yi ta fita ta ɗauro alwala ta shigo. Umma ta samu tana cin abinci, sallah ta gabatar, bayan ta idar tana zauna shuru, ɗakin ma shuru babu me yi wa wani magana.

Radiyya ce ta kawar da shurun ta dubi Umma tana faɗin.
"Umma ina son fara sana'a."

Kallonta Umma ta yi ta ɗauke kanta, duk lokacin da ta dubi fuskarta yana tuna mata da abubuwan da ya shuɗe tsawon shekaru. Kamar ba za ta ce komai ba can ta ce.
"Kin yi tunani. Sana'ar me za ki fara?"

Jin Umma ta ba ta goyon baya ya sa ta gyara zama ta ce.
"Umma ni ma ban sani ba."

Cikin gatse Umma ta ce.

"Idan za ki iya ki fara kunun Aya da zoɓo, kinga azumi za a fara kuma ana zafi."

Duk da wuya amma hakan bai hana Radiyya yin murna.

"Na gode Umma. Insha Allahu zan yi ƙoƙarin gwadawa ko shi ɗin ne."
Faɗin Radiyya, bayan Umma ta sake sun yi magana, yau rana ɗaya ta ba ta shawara a matsayinta na mahaifiyarta, lallai mahaifiya daban ce, tun zuwanta gidan rayuwarta ya fara canzawa.

DUHUN ZUCIYAWhere stories live. Discover now