DUHUN ZUCIYA
Shafi Na Biyu
Pharty BB
Wattpad PhartyBB...
Tsoron nan da take ciki kullum shi ya ziyarci kwanyarta yayinda tashin hankali ya biyo baya, kallon su ta yi ƙoƙarin yi sai dai babu wanda hankalin sa yake gareta balle ya fahimci halin da take ciki, ita kaɗai ta damu da damuwarta da hatsarin da rayuwarta yake shirin faɗawa.
A sanyaye ta ja ƙafafunta zuwa cikin ɗakinta, ta rasa wani irin tunani za ta yi, tasan duk shirin Uncle ne da Aunti Mimi ba ta gano hakan ba, ba tasan yaushe za ta fuskanci halin da take ciki ba, ko ta samu ta sassauta mata nata matsin lambar, ta barta ta ji da ɗayan ɓangaren. Yaushe ita tana matar gidan amma sai ita za ta masa rakiya kasuwa.
'To me zan masa?'
Ta tambayi kanta tana zama bakin gado tare da rafka tagumi. Tana tsoron keɓewarsu su biyun har cikin ranta, tsoron abin da zai je ya dawo take domin tasan ita za a cuta.Kwala mata ƙiran da Aunti Mimi ta yi ya sa ta zabura ta miƙe da sauri ta fita tana amsawa. Samu ta yi ita ɗaya ce Uncle ya fita a falon.
"Ga ni Aunti."
Radiyya ta faɗa yayin da take durƙusawa ƙasa."Ki gyara saman dinning ɗin sai ki ɗaura abinci mai sauƙi don ki yi ki gama ki shirya, kar ya zo ya yi ta jiranki na sanki da sanyin jiki."
To Radiyya ta amsa da shi tana miƙewa. Tamkar yadda ta buƙata haka ta tattare gurin ta kai kitchen, sai lokacin ta yi breakfast kafin ta fara aikin. Guraren sha biyu da rabi ta gama komai tsaf ta wuce ɗakinta, wanka ta yi ta ɗaura alwala ta fito, doguwar riga ta saka da babban hijab har ƙasa, mai kawai ta shafa sai turare kaɗan marar ƙarfi ta feshe jikinta da shi, ba ta yi wani kwalliya ba bayan haka, don tsoron abin da zai faru take idan suka zamto su biyu ne. Sallah ta fara gabatarwa bayan ta idar ta fito falon, a daidai lokacin Aunti Mimi ta fito cikin shirin fita.
Kallo ɗaya ta yi wa Radiyya ta ɗauke kanta."Zan je ɗauko Walid a makaranta, idan Uncle ya zo ku tafi kawai."
Da tana da halin magana da ta yi, roko ɗaya kaɗai za ta yi gareta, su fasa fita tare ko a fasa wannan tafiyar ita da Uncle Nasir. Kai kawai Radiyya ta ɗaga tana faɗin.
"To a dawo lafiya."Ba ta gama sauraronta ba tasa kai ta fita. Kasa zaune da tsaye Radiyya ta yi ta fara zagaye falon, ƙarshe ta ɗaura hannu saman kanta ta fashe da kuka, nan ƙasan falon ta durƙushe ta ci gaba da kukanta son ranta. Hanyar da za ta kufce masa take nema domin tseratar da rayuwarta.
Ta jima haka kafin ta miƙe tsaye da sauri ta fita a falon. Ba za ta iya jira ya dawo ya sameta ita ɗaya ba.
Bakin baranda ta zauna tana zabga tagumi ta zubawa ƙofar shigowa gidan ido.
Mintuna goma da zamanta aka danna horn, da sauri Mai Gadi ya fito a ɗakinsa ya buɗe get ɗin, motar Uncle Nasir ya danno kai ciki. Da Radiyya ya fara tozali, ta cikin motar suka haɗa ido Radiyya tayi saurin sunkuyar kanta ƙasa. Ya yi mamakin ganinta a waje zaune sai kuma tunanin Mimi ta fita ya sa shi buga tsaki.
Bayan ya kashe motar ya fito ya doshi gurinta, Radiyya na ganin haka amma ta ƙi tashi ta ƙara raɓewa jikin gini. Kusa da ita ya tsaya daf yana binta da kallo kafin ya ce."Tashi mu shiga ciki."
Girgiza kai ta yi kanta a ƙasa har lokacin tana wasa da kyawawan yatsun hannunta, yayinda zuciyarta yake bugawa tamkar zai fado kirjinta.
"Nan ma ya isa."
Ta furta tana tsoron abin da zai faru.
Bai ji haushin me ta faɗa ba, ya ƙara sassauta murya."Jira na kawai za ki yi na shirya idan na ci abinci sai mu tafi, na fiki son fitar mu tare Radiyyatu."
YOU ARE READING
DUHUN ZUCIYA
RomanceZuciya na duhu ta zamto kurman dutsen da ke tsakanin sahara, zafin rana na ratsa shi, turirin sahara na turara shi. Wannan shi ne kwatan-kwacin misalin da ke tsakanin wanda ya rasa kulawa da ƙauna ga makusantansa. Tsana ta ma ye wajen soyayya, has...