BABI NA BAKWAI

219 26 9
                                    

DUHUN ZUCIYA

Babi Na Bakwai

Pharty BB
Wattpad PhartyBB

Yau Radiyya ba ta fita da wuri ba sai kusan shida saura na yammaci. Duk a firgice take sakamakon abin da ta ci karo dashi kafin fitowarta, hakan ya sa gaba ɗaya tunaninta ba ya tare da ita. Har suka isa ba ta san sun iso ba, har sai da mai adaidaitan ya sanar mata. Hankalinta gaba ɗaya ya tafi wani yanayin, har sai da ya sake maimaita maganarsa da ɗan ƙarfi kafin Radiyya ta dawo hankalinta a tsorace tana dubansa.

"Mun iso!"
Ya ƙara faɗa, hakan ya sa ta kalli wajen ta ga lallai sun iso, fita ta yi a ciki. Ganin haka mai adaidaita ya sauka ya taimaka mata ta kai wajen da take ajiyewa. Bayan ya ajiye ta biyasa kuɗinsa kafin ta nemi gurin zama. A kowanne daƙiƙa tsoro ne yake ziyartar zuciyarta yayin da fargaba yake biyo baya. Ta rasa wani irin tunani za ta yi wa wannan lamari.

"Kar fa ya zamto gaskiya."
Radiyya ta faɗa a ranta tana haɗa kai da gwuiwa, kuka take son yi ko za ta ji sauƙi daga raɗaɗin da take ji a ranta. Ta tafi duniyar tunani ba ta san Sahabi ya zo saman kanta ba har sai da ya tsugunna da ƙarfi ya ce.
"Radiyya!"

Ta tsorata sosai ta ɗago a firgice, ganin wanene ya sa ta sauƙe mugun ajiyar zuciya, sai dai hakan bai hana jikinta yin rawa ba.

"Lafiyarki ƙalau?"
Shi ne tambayar da ya mata yana bin ta da kallo. Ya hango tsantsar damuwa a fuskarta, hatta ƙwayar idanuwanta sun kasa tsayuwa waje ɗaya.

Kai ta girgiza alamar eh, sai kuma ta yi saurin gyada kai tana faɗin.
"Lafiya lau. Azumi ne."

Bai yarda ba sai dai baya son shiga hurumin da ba nasa ba, ko wuce gona da iri, hakan yasa ya miƙe, bai ce mata komai ba ya bar gurin. Har ya koma wajen aikinsa ya fara sallamar mutanen gurin sannan Radiyya ta ɗauke kanta daga gareshi. Ji ta yi tamkar ba ta kyauta ba da ta kasa sanar masa da matsalarta, sai dai can ƙasan zuciyarta ta kasa hakan don tana ganin hakan sirrinta ne.
Haka Radiyya ta yi cinikin ranar babu walwala a tare da ita, ga azumi ga tunanin da ya sa ta gaba ya haifar mata jin zazzaɓi.
Shida da mintuna talatin da ɗaya ta masa sallama ta nufi gida, tana shiga gidan ta samu kowa na aikin gabansa.  A dadafe ta watsa ruwa ta ɗauro alwala ta shiga ɗaki, kwanciya ta yi jin zazzaɓi yana neman rufeta, ta kasa fita wajen Umma su sha ruwa.
Umma ganin har an fara ƙiraye ƙirayen sallahr magriba babu Radiyya kuma babu motsinta a ɗaki ya sa ta miƙewa da sauri ta shiga ɗakin, can ta hangota kwance, da sauri ta nufi gurin tana yaye hijabin da ta rufe fuskarta da shi.

"Radiyyatu lafiyarki?"

"Umma zazzaɓi nake ji."

Tsakanin uwa da ƴa sai Allah, wani tausayin Radiyya ne ya ratsa zuciyar Umma ta tallafota ta zaunar, ba ta ce mata komai ba ta miƙe ta fita. Ɗauke da kofi cike da koko ta shigo ɗakin da kuma ruwa, gefen Radiyya ta duƙa ta ajiye sannan ta miƙe.
"Ki daure ki sha na aika miki magani."

Kai kawai Radiyya ta gyada ta ɗauki kunun ta fara sha, Umma kuma hijab ta ɗauka ta fara sallah. Rabin kofi Radiyya ta sha ta kurɓi ruwa kaɗan, ta miƙe don gabatar da sallah kenan yaron da Umma ta aika siyo maganin ya yi sallama ya shigo.

"Ga shi Umma ta aike ni magani."

"To an gode."
Radiyya ta faɗa tana karɓa ya fice, maganin ta sha ta tayar da kabbara ta hau yin sallah.
Umma tana gamawa fita ta yi ta nemowa Radiyya abinci ta dawo ɗakin, ajiye mata ta yi gefenta inda take sallah sannan ta fita a ɗakin. Bayan Radiyya ta idar ta yi addu'o'i ta shafa kafin ta gyara zama tana jawo filet ɗin gefenta, faten wake ne bai fi ci goma ba, tasan wannan shi ne rabonta da na Umma gaba ɗaya. Hawaye ta ji ya taru a idanuwanta ganin yau Umma ta damu da ita da lafiyarta, har ta iya sadaukar mata da cin ta ita ta ci duk da ta wuni da azumi, bayan hannunta ta sa ta share hawayenta da ta ji ya zubo sannan ta fara ci, kaɗan ta ci ta ragewa Umma sauran, da ta gama ta ajiye gefe gudun kar ta fitar wani ya gani ya cinye, sallar isha'i ta yi ta koma shimfiɗa ta kwanta.

DUHUN ZUCIYATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang