KASAR WAJE. 57

1.4K 55 11
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

page. 113/114

d'an bud'e idanu hayfa tayi kamar cikin bacci ta ke kallon nurse d'in saidai ita nurse d'in batasan hayfa ta farka ba zata tsira allurar aka fara tab'a qofar cikin tsoro da fargaba ta maida allurar aljihunta hakan ne ya sanya hayfa zargin nurse d'in ta isa qofar ta bud'e wata nurse ce itama ta shigo kawowa duba hayfa da tsammanin babu kowa ciki sai tace mata tana duba hayfan ne waccan ta tafi, tayi ajiyar zuciya tana komawa inda hayfa da idanunta ke lumshe still kamar mai bacci taci gaba da kallonta a haka har ta qaraso kan hayfa tana kallon hayfa a taammaninta still hayfan bacci take yi inda tayi tunani gara ma ta sakarwa hayfa injection d'in cikin drip ta juya ta gyara drip d'in ta fitar da allurar ta fara tsirawa ciki ta gama cikin gaggawa ta juya ta kalli hayfa ta nufi fita tana fita hayfa da zuciyarta yaqi amince mata da matar ta fusge drip d'in ta fara qoqarin miqewa a hankali ta tsaya gaban drip d'in tana kallo tabbas matar wani mugun abu tasa mata a ciki to why.? A hankali taje jikin qofa ta kulle ta dawo ta zare robar drip d'in ta shiga toilet ta b'alle bakin ta tsiyayar dashi ta bar kad'an ta dawo ta maida ta rataye ta koma ta kwanta zuciyarta cike da saqe-saqe

Koda ta isa inda Kamal yake ta kalleshi tace nagama, ajiyar zuciya yayi ya mata godiya yace za suje cash ya keda shi zai bata tace OK tana juyawa sabida ita ji take yau ma tafiya za tayi Holliday zuwa Hawaii.  Da wannan tunanin ta wuce office d'insu na nurses ciki da farin cikin nasarar da ta samu..

Kamal ma cike da farin ciki ya zauna yana jiran lokaci ya d'an tafi kafin yaje ya duba hayfa ko ta farka... Yasir na son qara yiwa Yusuf magana amma ganin shima a rakub'e yake da Yusuf d'in yasa ya hakura da fatan har sai d'in ya sakko tukuna ya masa magana...

Bayan ta zare drip d'in ta koma ta kwnata bacci tunda sai gobe wai za a sallameta,..!

**********

Yau kwanan hayfa biyar da dawowa sannan sosai Yusuf ya  fita hanyarta sun d'an shirya babu laifi shi da yasir sunama ta shirye-shiryen school inda Yusuf ya koma abinsa rayuwa d'akinsa na masallaci sosai hakan yayiwa su Hamzad dad'i suka qara masa albashi na gadi dukda in ya fara school zaiyi busy, a b'angaren hayfa tausarta sosai Armando da Kamal keyi shi kamal cike da farin cikin cewa ciki ya zube don haka after gala zai fara mata maganar aurensu saidai ya lura sam kullun cikin kuka take bata tab'a wuni batayi hawaye ba inda Koda suke waya da iyayenta da su ammah bata fad'a musu komai ba saidai ta yanke hukunci idan har after gala Yusuf bai maidata ba zata koma Nigeria ta sanarwa ammah su nemi mafita ita kome zaayi masa ya dawo gareta ta amince saidai shap ta manta cewa ai in ammah tasan waye Yusuf akwai matsala saidai still tana ganin zata samu mafita inda tun bayan abinda nurse ta mata ta tsince kanta da rashin son kowa yasan cikinta na tare da ita kamar yadda ta biya Dr kamfani $100000 ya nuna a result d'inta batada ciki har lokacin da cikin zai bayyana kansa gashi yanzu saura 11dys gala aiki yayi zafi sosai take jigata saidai tanata b'oyewa kada kowa ya gane

Liliana ta kalli Raudha tace "wai ko ina kinata zuwa babu labarinsa.? Raudha tana hawaye tace eh amma ance yana cikin garin nan ni kaina ina kiransa yana shiga saidai baya d'agawa a yanzu ma yayi blocking d'in No d'ina kona kirashi baya shiga, liliana tace ga aiki ya mana yawa gobe zamu wuce Milan ya zamuyi da cikin.? Raudha tace tunda yanzu nasan shegiyarnan ce matarsa to wlh bazan fitar da cikin ba zan haifeshi ko babu komai na fita a gurinsa ni zan fara bashi baby.. Liliana ta zaro ido tace yaya za kiyi da Su bunill..? Raudha tayi tsaki tace da zarar cikin yayi 5mths zan nema Hutu ince matsala familyna ke ciki inje India in haihu in bar baby in dawo, shiru liliana tayi kafin tace kina ganin duk wannan sacrifices d'in ya cancanta.? Raudha tace eh zan mallakeshi tunda dai ya gano qaryarta sannan bazai tab'a yafe mata ba, liliana tace bt kafin mu wuce Milan kiga Dr ya baki y'en abubuwa da zasu hanaki laulayi kada asirinmu ya tonu kinma ci sa'a munyi nasara Dr kamfani ya rufa mana asiri ai da yanzu bamu zaayi wannan Gala.

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now