KASAR WAJE. 17

1.1K 51 1
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 33/34

Shiru shima yayi yana tunani tare da fatan bud'i a rayuwarsa

a hankali ya d'ago fuskarta yana kallonta yace "pls kada ki tab'a nadamar aurena IA ko bani da komai samunki a rayuwata babban arziki ne"

Hawayen dai take still inda cikin dakiya ta fad'a k'irjinsa inda shima ya k'ara rungume ta sosai

Kusan 5mnts ta d'ago daga jikinsa kanta na k'asa rik'o hannunta yayi yace "zanje aiki amma IA zan dawo da wuri na raka ki aiki"!

Ya mik'e tana zaune yanda take kanta na k'asa peck ya mata a tsakiyar kan ya fito d'akin shima bai karya ba ya wuce.

Tunda ya fita still hawaye take sosai ta fara jin tausayinsa da yadda kula da ita dukda rashin wadatarsa

Haka ta kwanta shiru tana kwance ne taji wayarta na ringing ta mik'e ta bud'e jakar ta d'auka

da sauri ta ansa ganin ammah ke Kira

Mominmu kuna lafiya? shekarn jiya muna magana wayar ta katse netwok, Ammah tayi d'an murmushi tace "yaya kuke y'an matana ya mijinki"?

Hayfa tace lafiya mominmu, ya daddy?
Ammah tace yana lafiya yana gaisheki Adda suwaiba tace shekaran jiya kin kirata ko?

Hayfa tace eh...

Ammah tace komai lafiya dai ko?

hayfa tayi ajiyar zuciya tana son fad'awa ammah maganar aikinta yadda take samun kud'i saidai sam yanzu yadda ta fara jin kusanci da Yusuf ba tason yin wani abu da zai kawo musu sab'ani cikin rayuwarsu domin ta tabbata in ammah tasan shi talaka ne dole su rabu

Ammah ce ta dawo da ita daga tunaninta "amma inaso ki k'ara kulawa kinga yadda yake mana hidima daga aurenku ko shekara ba kuyi ba ki rik'a masa biyayya komai yake so kinji?

Hayfa tace "toh"

Tace kuma komai k'ank'antar matsala in kikaga yafi k'arfinku ki fad'amin sabida na nema mafita da wuri kafin wasu su shigo ciki su ruguza muku rayuwa

Hayfa dai shiru tanata sauraro

Ammah tace "ya maganar karatu kunyi? Yaushe zaki fara?

Hayfa tayi ajiyar zuciya saidai ta kasa magana

Ammah tace shikenan kada ki takura masa ki k'yaleshi wata k'ila so yake sai kin k'ara hutawa kin saba da k'asar tukuna, ki maida hankalinki ki rik'a kula da mijinki kinga dai yadda na keyi da daddynku shi da ma baida komai amma ina bashi duk hakkokinsa na miji komai yace nayi yi nake komai yace na bari bari nake sabida Mace daga zarar tayi aure mijinta shine duniyarta da lahirarta dukkan wani iko na rayuwarta yana hannunsa koda mijin baida komai bare wanda yake maka hidima ba sassauci babu bak'in ciki, sabida kinga wani mijin bazai sauke maka hakkinka da ke kansa ba sannan kuma bazai barka ka nema ka yiwa kanka ba, ina matuk'ar farin ciki da yadda Allah ya baki wannan mijin na ki gashi da tarbiya domin baya 3dys bai kirani ko yayimin text na gaisuwa ba

Tunda ammah ta fara magana hayfa ke hawaye

Ammah taci gaba kinga yadda mukaita wahalar rayuwar aure ni da Adda mu yiwa kanmu da yaranmu amma mu ka hak'ura muna zaune domin munsan ko ta hanyar waye wata rana Allah zai canza mana rayuwa gashi yanzu Allah ya canza mana ta dalilinki, don Allah y'an matana ki rik'e mijinki kinga tun baku je ko'ina ba rayuwarmu ta fara canzawa kada ki tab'a yadda wani abu da zai kawo rabuwa tsakaninku ya gitta kinji?

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now