KASAR WAJE. 33

1K 54 2
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 65/66

Hayfa ta kalla Surayya tace "ya shirin exam"? Surayya tayi murmushi tace lafiya aunty saidai babu sauqi ko kad'an.. Hayfa tace ay dama amma ki dage IA komai zaiyi kyaw idan kika maida hankali kina karatu sosai

Surayya tace IA.. Suka ci gaba da hirarrakinsu suna gurin Armando ya shigo duk da yaran basusanshi ba Khairat ta kwashi gudu taje jikinsa ya d'agata yayinda y'an uwanta da sauran k'annin surayya duk suka fara gaisheshi

Zama yayi itama hayfa ta gaisheshi suka d'an fara tattaunawa a kan wasu ayyukansu da kuma tafiyarsu gobe zuwa k'auyuka..

A Toronto su Yusuf ansha aiki sosai gashi anata sa ran gobe za a tashi da azumi inda suna waya da Yasir Madam hayek itama gobe take parking don haka Yusuf dama ya gama contract d'insa na ansa har ya biya kud'in 3mths sabida yanaso in ya dawo yayiwa su Qassem aike ko yaya dukda yanzu suna yawan ce masa basu cikin buqatar komai wanda shi bai yadda ba yana ganin basuson fad'a masa ne kawai..

Yasir yana gida ya ci abinci ne yanason zuwa gun Tiffun kafin lokacin club su wuce aiki sbd gobe bazaije club ba zai tsaya taya madam hayek parking sannan ya gyarawa su Yusuf yadda in suka dawo komai na tsaf zasu tare..

Bayan anyi dinner wajajen 8:30 pm a gidan Ammah kafin suwaiba ta wuce gida saidai yara su duk nan zasu kwana wai tare da hayfa wanda hakan yasa dole hayfa ta koma d'akinta na gidan tare da su duka sabida k'aton toyal bed ne a d'akin

Duk sun ma yi bacci 11:40pm ta mik'e a hankali da niyar sauka k'asa ta nema Yusuf a hankali take tafiya gudun tashin wani a gidan saidai daf d'akin Ammah taji tana waya da ya d'an d'auki hankalinta a hankali ta tsaya

Amma taci gaba Adda wlh babu wani alamar ciki tare da Hayfa tun jiya da tazo nake kula amma banga komai ba kinsan da akwai komai k'ank'antarsa zakiga ma yana sata laulayi musamman irin cikin wannan zamanin

Batasan mai aka fad'a a d'ayan b'angaren ba taji amma na cewa "eh na yiwa malam duka wannan bayanin yace zai duba kinsan yace tabbas yanzu akwai soyayya tsakaninsu ba kuma aikin da yayi bane na sanya musu yawan sha'war juna kinsan dama yace aikin da zarar tayi jini ko wani iri ne aikin zai lalace saidai aikin ya k'ara taimaka musu wajen son kusantar juna   haihuwarce ni narasa yadda zamu b'ullo Adda

Ajiyar zuciya hayfa tayi..  Ta jiyo muryar Ammah ay bama zai yuwu ba da duk wahalar da mu kasha wajen had'a auren ace na bari danginsa su rabasu idan sukaga bata haihuwa, yadda muka yi aiki ya aureta ba tare da ya shirya ma hakan ba haka yanzu komai zanyi domin shiga tsakaninta da duk wani wanda zai raba su

Mugun fad'uwa k'irjin hayfa yayi "wasu irin hawaye masu zafi suka fara sintiri a kumatunta a hankali ta juya ta koma d'aki kan kujerar d'akin ta zauna ta kama kanta tanata hawaye sosai

To a inama suka samoshi har suka masa asiri don ya aure ta..? Innalillahi take maimaitawa tabbas suna tsammanin mai kud'i ne shiasa suka aikata haka

Wani irin mugun taisayinsa da sonsa taji suna ratsa zuciya da jininta wani d'an jaririn kuka ta saki a hankali tana dana sanin duk abbubuwan da ta rik'a yi masa a farkon aurensu kuma IA da zarar ta ajiye aiki zata je ta kwance mahaifarta ta fara haihuwa kamar yadda yake so da fata baza ta k'ara bari ayi masa wani abu mai sunan asiri ba

Mik'ewa ta sake yi a hankali ta d'auki wayarta cikin sand'a ta fito har lokacin Ammah na waya don haka ta wuce ta sakko k'asa can waje ma ta fita wajen baranda ta zauna kafin ta fara nemansa

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now