KASAR WAJE. 44

969 49 2
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page. 87/88

A sokoto Abba da dagarbati gidan hakimi aka kaisu inda a kayiwa Abba tarb'a ta mutunci sosai suna fada da hakimi..

Bayan sun gama gaisawa hakimi yace y'an zaman fada su d'an bashi guri su gana da bak'on.. Bayan duk an watse garbati ma yana waje a mota hakimi da ya kasance matashi ne domin mahaifinsa ya rasu aka bashi kujerar mahaifinsa.. Cikin girmamawa ya kalli Abba yace ina k'ara muku barka da zuwa fadarmu mai albarka. Abba yace na gode ranka ya dad'e.. Hakimi yace anmin bayani cewa kunzo neman wasu y'an uwanku ne ko..? Abba yace haka ne ranka ya dad'e.. Hakimi yace to kunada sunansu ko unguwar da garin da suke nan cikin sokoto..? Abba yayi shiru kad'an kafin yace ah ah ranka shi dad'e inadai da sunayensu amma bayan haka banida wani abu da na sani.. Ajiyar zuciya hakimi yayi ya kalli Abba yace to meye tarihinsu domin tabbas anan sokoto munada y'an hijira daga chadi kamaru Niger da ma Mali.. Ajiyar zuciya Abba yayi yace wannan daga Niger suke nan Abba ya fara bawa hakimi labari har yazo k'arshe.. Ajiyar zuciya hakimin yayi yayi shiru na mintuna kafin ya kalli Abba yace gaskiya abin da d'an rud'ani sabida ba lallai ba ne nan sokoto suka tsaya mai yuwuwa sun wuce malumfashin kamar yadda suka tsara tun farko amma tunani ne mai kyaw Ku fara neman daga nan tunda nan ne tushen labarin.. Yaci gaba yanzu ku kuma masauki akwai tsofaffina abokan shawarar wannan fada kuma dad'add'un tsofaffine wasu sunkai 100yrs ma zan gana da su wata k'ila in akwai wani taimako da za suyi ko zasu iya samo mana wani haske akan al'amarin to IA zan sanar da ku.. Ajiyar zuciya Abba yayi yace nagode ranka shi dad'e saidai kamar kwana nawa za muyi nan d'in..? Hakimi yace ku bani zuwa jibi duk abinda ake ciki zan sanar da ku IA.. Abba yace godiya na ke ranka shi dad'e su kayi sallama Abba ya fito garbati ya bud'e masa mota ya tayar suka wuce masauki..

Yana aiki wayarsa ta fara ringing ya d'aga mamaki yayi ganin yasir war 12:01pm haka ko baije club ba ne za su had'u a hankali ya d'aga "ya akayi"..? Yasir ya saki dariya yace "dude yau ana anniversary na club ance tsoho da sabon ma'aikata kowa shiga free" .. Tsaki Yusuf yayi yace don wannan ne ka kirani..? Yasir yace eh mana sai kanayi kana walawa fa meye haka kai sai kace kai ake aure sam ka d'aukewa  kanka duk wata dama ta more k'uriciyarka.. Yusuf yace yanzu kai ba  kana more ta ka ba ..? Yasir yace eh kaima dole sai ka more ba wani abu zamu yi ba kawai mu shiga ne muyi kallo na bulus.. Dariya ce ta kub'ucewa Yusuf yace ay banida abin kallo na lokaci a waje bayan inada abin kallo na har abada a gida.. Dariya shima Yusuf ya saki yace gaskia ne d'an iska yanzu gori ma za kamin ko? Kai ga mai mata.. Dariya Yusuf ke yi yana ayyana yasir akwai ban dariya kamar wani comedian.. Yasir ya rage dariya yace "pls dude in ba  kazo ba shine ma zanyi sha'awar yin shirme in naga su tiffun nayi!.. Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace "is ok" zan nema excuse a masallaci in sun amince za ka jini amma in suka ce zasu yanke a kud'ina gaskiya saidai kayi hakuri"  Yasir yace blackmail ko..? Yusuf ya saki dariya yace no ka jira dai kawai ansata nan da 30mnts.. Yasir yace OK su kayi sallama.. Layin hamzad Yusuf ya jefa da ke gidansa ba nisa da masallaci sanin cewa hamzad d'in ya kan kwana karatun qur'ani.. Bugu d'aya hamzad ya ansa Yusuf ya fara gaishe shi..

Hamzad cikin d'an hanzari na fargabar ko wani ya faru a masallacin Yusuf ke kiransa a wanann lokacin.. Gyaran murya Yusuf yayi yace wani uzuri ne ya samu d'an uwana na ke neman alfarma na je na sameshi.. Ajiyar zuciya hamzad yayi yace yanzu.? Yusuf yace "eh" d'an shiru hamzad yayi ganin sam Yusuf baya wasa da aikinsa duk kuwa da cewa yana matashi kuma da mata.. Ba  komai hamzad yace amma ka jirani zan turo wani yaron gidana mai gyaran gida ya karb'a maka kaje..

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace nagode Sir..

Suka yi sallama ya kashe wayar a abinda bai fi 10mnts ba  yaron yazo Yusuf ya kama hanyar club su turai taxi kwana suke aiki koda ya iso club su yasir na ciki anata iya shege barin tiffun da Pascal.

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now