KASAR WAJE. 11

1.2K 57 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd


Page.    21/22

Bayan Yusuf ya gama aikin yamma na pool sauri ya ke yau ya dawo gida yaga hayfa gashi gobe bufday d'insa na 27yrs gashi gobe hayfa zata fara aiki zaiyi kokari suyi celebrating ko yaya ne

********

Tunda ya tashi da asuba bayan yayi sallah yana tsaye kanta yana tunanin abinda zai had'a musu na karyawa kafin yasir ya iso ta fito d'aki ya juya yana kallonta

Tana sanye da doguwar rigar Sheraton dark pink ta matseta kmar da fatar jikinta aka auna d'inki tayi d'auri ta d'an bar gaban kanta gashin a kwance sosai tayi kyaw na fitina ga k'irjinta a cike dam hayfa akwai baiwar k'irji

Wani irin yawu Yusuf ya had'iye, ita yunwa ya fito da ita!

Fitowa yayi daga kantar yazo har gabanta ya d'ago fuskarta ya fara mata wani zazzafan kiss

Itama batasan ya akayi ba ta fara tayashi hannunsa ya rik'o nata ya had'a yana ci gaba da kissing d'inta na fitina kai sai gashi ya mannata da k'irjinsa sosai hannunsa na k'ugunta

sunyi nisa suka ji Yasir na k'ok'arin bud'e k'ofa da d'an sauri hayfa ta janye jikinta ya shiga d'aki
Zama tayi gefen gado ta rik'e kanta tana tanbayar kanta "mai yasa ta fara biyewa wannan talakan da ba zama tayi da shi ba"?

d'an ajiyar zuciya tayi tace in kuma bana sakar masa jiki bazan samu damar sanin kasarnan ba bare har na samu na tafi a lokacin dole ya bani takarda na nema kamal mu shirya na fara karatuna da wannan tunanin taji nutsuwa a zuciyarta tana zaune taji yasir na cewa to ka yiwa ogan café visarta ya k'are?

Yusuf yace eh kasan ana d'an d'aga k'afa wai bayan wata kafin hukuma ta shigo ciki kuma IA zan nema wani aiki gobe bayan pool wanda kaga in na had'a da café da pool da shi zan samu na ansar mata visar ko yaya ne

Yasir ya ce gaskiya tayi dace sosai da samunka a matsayin miji inama da Hamdiyya ce ta samu miji kamar ka

D'an murmushi Yusuf yayi yace meyasa kace haka?

Ita kanta hayfa ta nutsu tana saurarsu

Yasir yace ka duba yadda auren nn yazo maka babu shiri amma duk da haka baka tab'a danasanin auren ba sannan dukda nauyi da matsaloli da kake dashi kullum burinka sauke nauyin matarka da bata hakkinta kana burgeni sosai ba don nasan yadda wannan gimbiyar ya saye zuciyarka ba da na baka hamdiyya nasan ko bana raye ba zata tab'a kukan auren miji kamar ka ba!

Ajiyar zuciya hayfa tayi

Shima Yusuf ajiyar zuciya yayi yace "nagode"

Yasir yace yau wai me za muyi ya kamata muyi celebrating ko yaya ne

Yusuf yace eh ina tunani IA

Yasir yace ni zanyi komai sabida dama ban bada gudunmawar bikinku ba, wai ita madam da zata fara aiki yau ya za kuyi?.

Yusuf yace ay ita nata kamar tym d'in Gizela ne 4:pm zata fara ta tashi sai lokacin tashinmu d'aya

Yasir yace gaskiya ka fiya son yarinyarnan yanzu aikin nn da zai sosai kudin zai taimaka maka amma ka bar mata Allah yasa tana sonka kamar yadda kake sonta

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace munyi latti muje

Fita suka yi duka!

Yayinda hayfa ke zaune duk jikinta ya mutu jin hirarsu

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now