KASAR WAJE. 13

1.2K 54 5
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  25/26

Tsayuwa yayi bakin k'ofar ganinta kan dadduma tana karatu da d'an k'aramin qur'ani.

Tana kaiwa a ya ganinsa ta rufe qur'anin saidai ta kasa yi masa magana tana son gaishe shi

zama yayi gefen gadon yana kallonta yace "barka da safiya"!

d'an sunkwi da kai tayi tace "kaima haka" tayi shiru..

Mik'a mata wayar yayi yace gashi na saka miki sim a ciki

d'an d'agowa tayi tana kallonsa ganin wayarsa yake ba ta...

Yace karki damu na saya wani ke kuma na baki wannan

shiru ta kasa ansa kusan 5mnts ya mik'e ya mik'ar da ita ya rik'ota zuwa jikinsa yace "muje mu karya na wuce kada nayi latti"

a dole ta biyo shi suka shiga d'an kantar tare ta d'auko bread a fridge ta shafa musu butter shi kuma ya had'a musu tea suka fito suka zauna falon suka karya

Bayan sun gama 7:23am Yusuf ya rungumeta sosai jikinsa ya mata peck tsakiyar kanta ya wuce aiki

Bayan tafiyarsa tayi gyaran gida shara mopping da wanke-wanke da wankinta duka kusan 11:9am ta gama komai ta yi wanka tazo ta d'auka wayar tana kallo IPhone5 ce ita da ko iPhone7 ta taina

fara duba wayar tayi ta shiga wpp d'in ammah ta mata voice note na yadda take missing d'inta da yara duka

Sanann ta saka number suwaiba ta gaisheta, sannan ta shiga number salma baita ganin Yusuf bai goge ba bata onlyn don haka itama ta bar mata msg ta kashe data ta kwanta domin ita dama batada Facebook accnt ba tayi shiasa ba mata shiga ba.

Armando ya kira bunil ya fad'a masa yadda suka yi da hayfa

Bunil yace gaskiya in ba zata iyaba ka nemo wata ko mu aro Raudha daga India tunda kaga dama tanata tokarmu kaga sanyi ya fara nisa a ce har yanzu bamu saki summer collection ba

Armando yace kayi hakuri mu bata lokaci yau da gobe yarinyar k'arama ce sosai bana tunanin ko 18yrs tayi dole abin ya buk'aci tayi tunani yaso zamu sa mata zafi sai ayi show nn da 10dys

Bunil yace shikenan amma gaskia daga gobe kawai...

Armando yace don't worry suka yi sallama

Tunani Armando ya fad'a Allah yasa hayfa ta amince domin bayan aikin summer ga collection d'insu na abaya na Kuwait da Dubai zai so suyi aikin da ita tunani ma yayi zai yiwa yarinyar dabara suyi contract da ita na 2yrs yadda da haka ba zata kub'uce musu ba da wannan tunanin yayi mutmushi

2:54  Yusuf yau ya gama aikinsa na yamma ya da wuri ya kira alhaji shamsu jikinsa yayi tsanani a India wani d'an alhajin ne ya ansa wayar sosai hankalin Yusuf ya tashi ya kira innarsa suka d'anyi hira tace ya gaida hayfa da haka ya dawo gida hankalinsa duk baya kwance da ciwon alhaji shamsu

Hayfa na falo da wani dogon riga mara hannu ta kama gashinta baya wani magazine take karantawa ta internet taji motsinsa

mik'ewa tayi za ta shiga d'akin saidai yanayin da ta ganshi jikinta ya d'anyi sanyi bata iya tanbayarsa ba amma ta kalleshi tace "sannu da zuwa"!

Nagode yace ya zauna ya d'an saki fuskarsa baya so ta gane komai, Ganin ma lokacin aikinta ya kusa ta shirya ta fito tace "zan wuce"!

d'an d'agowa yayi yana kallonta yace "kinci abinci"?

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now