KASAR WAJE. 55

1.6K 79 24
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  109/110

Tun lokacin da tace shi saurayinta ne wani masifar tsanarta ya qara d'arsuwa a zucuyarsa tabbas zaman yaudara tayi dashi wato kawai kudi tazo nema a "Asar Waje" wani irin danasani yaji na aurenta yana kama kansa saidai ko kad'an bai bari su Sebastian sun gane halin dayake cikiba a hankali ya miqe ya musu sallama dukda Sebastian ya fahimci komai kai har sauran ma duk sun gane saidai shi bature baya shiga sabgar da bata tasa ba Yusuf yana taxi saidai hankalinsa ya gama barin jikinsa duniya ta qara masa d'aci qudirewa ma ya farayi anya bazai bar Toronto ba

Tunda suka bar studio d'in take kuka Armando na lallashi kallonsa tayi tace pls let me go inason kad'aicewa kallinta Armando yayi tazama kamar mahaukaciya yace queen bazan barki haka ba ke kad'ai is risky kizo muje na saukeki gurin Fabiola kasa yi masa musu tayi suka wuce

Kamal ya dawo gidan ya tadda batanan zama yayi dakalin qofar yana matse-matsen wayarsa da bai saka sim ba tukuna, yasir ne yake dawowa ya hangi Kamal qofar su hayfa kasa jurewa Yasir yayi domin shima sosai hankalinsa ke tashe na yadda suka rabu da Yusuf d'in shima dama gobe yake so ya d'auka hutun club yaje masallaci ya kwana gun Yusuf su shirya koda me Yusuf d'in zai masa, qarewa Kamal kallo yayi yaga wannan tabbas hausafulani ne na nageria don haka yayi masa sallama kamal ya ansa Yasir yace wa kake nema.? Kamal ya kalleshi yace yarinyar da m
Ke zaune nan, yasir ya d'anyi shiru yana nazari ko d'an uwan hayfa ne.? Ya d'ago yana kallon kamal yace ka kirata mana.! Kamal yace ai d'azu nashigo asar so ban saya sim ba tukuna, mamaki ne yakama yasir to ai itama yau ta dawo Nigeria muryar kamal ta dawo dashi tuanninsa kada ka damu kaje kawai zancigaba da jiranta a hankali yasit ya wuce cike da waswasi a zuciyarsa.

Tunda Armando ya barta gun fabiola ya qarasa gunsu raudha tana kwance kujerar falo ya qoqonsa ta miqe taje ta bud'e ganinsa qirjinta ya buga idanunta suka fito ta matsa ya shiga yana kallonta ya furta banda lokaci dayawa just kije "Fation Tv Toronto" yanzu kije ki qaryata cewa kinada ciki kuma queen matar aurece if not kin sanni fiye da kowa a kamfanin nan ya juya ya fita ya barta tsaye tana zaro idanu tabbas koda taje bazata ajiye makamanta da hayfa ba yaqi yanzu suka fara.  Sanin halin masifar da bala'en Armando da Bunill yasa ko kowa cikin palon bata yiba ta kullo gidan ta fita zuwa gidan jaridar cike da takaici da tsananin tsanar Hayfa..

Koda ta qaraso gidan Kamal na zaune yana jiranta sam wucewa tayi kamar bata ganshiba ta fara bud'e gidan zata shiga a hankali ya miqe yana kiran sunanta ta gama bud'e qofar zata shiga yana qarasowa ta juya tana kallonsa ta furta pls Kamal inason kasancewa ni kad'ai, ajiyar zuciya yayi yace pls nikuma bazan iya barinkiba a wannan yanayin shiru tayi bata kalleshi ba kafin tace nagod... Ya katseta Hayfa ban tab'a daina qaunarki ba kuma ko yanzu a shirye nake zan jiraki kiyi idda na biyoki ne domin ni kaina na d'auka tuni kuka rabu da mij... Maganarsa ce ta katse ganin Yasir ya tsaya yana kallonsu a hankali itama ta juya tana kallon Yasir d'in irin mugun kallon da yake musu cire idanunta tayi ta maida kan Kamal tace pls zan shiga ka bari zuwa gobe sai muyi magana OK yace yana juyawa ya bar gurin itama kutsa kai tayi nata parlon tana sakin kuka ta zauna kujera tana kama kanta ji take kamar ta had'iye rai ta mutu

Koda ya isa masallaci alwala yayi ya qarasa ya fara karatu Qur'ani har margrib a kayi sallah ya koma karatun sabida yadda zuciyarsa ke barazanar bugawa karatun ne kawai zai sanyaya masa zuciya

Bayan yasir ya shiga ya shirya dama ya barwa tiffun aikinsa don haka yayi shirin kwana ya nufi masallacin koda ya isa ana Ishaa yabi jam'i bayan an idar ne ya hango Yusuf can nesa yana zaune da qur'ani gefensa a hankali ya qarasa gurin shi mamaki ne ma ya isheshi rabonsa da karatun qur'ani har ya manta yazo "Asar Waje" ya shagale da neman duniya kawai Yusuf yaji tsayuwarsa kuma ya shaida anshinsa amma yaqi d'agowa saidai sosai ya samu sauqin zugin da zuciyarsa ke masa a hankali yasir ya zauna kusa da shi ya fara magana " kanata tanbayana abinda ke damuna tun ranar da matarka tayi tafiya, to abinda ka gano a yau nima shi na gano a ranar, d'an d'agowa Yusuf yayi ya kalleshi ya cire kai yasir yace bayan fitarka airport nan dai ya fayyacewa Yusuf komai wani irin qwalla ne suka taru idanun Yusuf Hayfa badata amana sam duniya da buri shine a gabanta kafad'arsa yasir ya dafa sabida ya rasa yaya ma zai lallasheshi bai tab'a ganin Yusuf haka ba rufe qur'anin Yusuf yayi ya miqe yasir ya qara dafa kafad'arsa yace pls ka yadda dani shiru yayi alamar ya sakko da yasir d'in suka nufi b'angaren d'akin Yusuf inda yasir yaga komai na Yusuf da alama ya dawo nan saidai bayason tayar masa da hankali again yace nazo tayaka aikin yau ne ajiyar zuciya Yusuf yayi baice komai ba

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now