KASAR WAJE. 7

1.3K 69 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  13/14

Bacci ne ya d'an kwasheta duk kuwa da zafin da jikinta yayi ga rawar sanyi tana d'anyi kad'an saidai ta lullub'a da hijabinta na sallah ga safa da ta gani gefen gadon ko damuwa ba tayi ba da sanin mai shi ta saka

koda ya iso gidan magrib tayi bai ko damu da rashinta a falon ba yasan tana d'aki

shiga yayi bayi yayi alwala ya fito bayin ganin yadda take k'udundune sannan ga d'an rawar sanyi tana yi da d'an hanzari ya k'arasa gadon yana ya d'an yaye mata rufar ya tab'a wuyanta

Tana jinsa bata ko motsa ba

Sosai ya tsorata jin mugun zafin da jikinta yayi da sauri ya mik'e ya maida takalminsa ya fita zuwa pharmacy da k'afa ma ya taka babu nisa da gidansu

Bayani ya musu na yanayinta aka bashi magunguna da yadda zata sha sannan aka ce taci abu mai d'umi tukuna ta sha

Yana isowa gidan ya kunna gaz ya d'ora taliya ya mata jolof da sardin da d'an ruwa-ruwa ya juye ya had'a mata coffee ya d'auki maganin ya nufa d'akin

Ajiye plate d'in yayi a k'asa ya d'an shafa hannunta a karon farko yana kiran sunanta HAYFA ga magani ki tashi ki sha

runtse idanunta tayi sam bata jin dad'in jikinta jin magani ne a dole ta tashi domin tana so ta warke ta nema mafitar halin da ya saka su ita da y'an uwanta

d'ago tray d'in yayi ya d'ora mata kan cinyarta ya mata bayanin yadda zata sha magani ya mik'e ya bar d'akin

Bin bayansa tayi da harara tana ayyana auren nan sunansa mafarki dole ne kuma ta farka daga mafarkin

Sallah yayi a falo shima ya d'iba taliyar yaci kusan 1hr yana zaune yana tunanin inama ya bar wayarsa yana son kiran innarsa

Ganin bai ga wayar ba ya mik'e a kujerar da tunanin k'ila d'aki take ya d'auka da safe kan ya wuce aiki baya son shiga d'akin dukda yana jin son jiyarta da kansa amma dole ya hak'ura ya kwanta zuciyarsa cike da kewar y'an uwansa da mahaifiyarsa.

Sosai kamal ya haukace a gidansu ya kulle k'ofarsa yana huci dole ko waye yayi kuskuren rabashi da hayfa yayi maganinsa

Yana kwance bacci mai nauyi ya kwashe shi inda hayfa bayan ta d'anci taliyar ta shanye coffee d'in tasha magani itama jikinta yayi nauyi ta kwanta in ta farka dare sai ta maida sallah

tun 4:56am Yusuf ya tashi yayi wanka yayi alwala ganin yadda hayfa ke bacci kamar jaririya yasa hankalin Yusuf kwanciya cewa taji sauk'i ya fito d'akin

Sallah yayi ya ci bread da tea ya bar gidan!

Yana train yana tunanin yadda zasu yi rayuwar aure a haka tun ba'aje ko inaba sun fara samun Matsala da tunanin har ya iso pool.

Wajajen 6:11am ta farka da salati cikin hanzari ta mik'e ta d'auro alwala tazo ta fara sallah

Bayan ta idar ne tana kan dadduma tayi tagumi tana tunanin yadda zata b'ullowa matsalarta

Tunani tayi bai kamata ta fad'awa aunty ammah yanzu ba saidai zata k'ara tunani ta bari ayi koda wata yaso ta nema kamal su tsara yadda zata samu admission ta koma cikin university da zama kafin su fad'awa aunty ammah ta rabu da Yusuf sabida yaudararsu yayi shi ba mai kud'i ba ne

da wannan tunanin taji hankalinta ya d'an kwanta ta mik'e taje ta d'aga fillow ta d'auko wayar ta kunna ta shigar da number salma baita tayi saving kafin ta kira salman directly bata tsaya magana ba tace ki hau wpp yanzu

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now