KASAR WAJE. 8

1.2K 58 0
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  15/16

Sosai abin ya dameshi amma a k'arshe ya share yayiwa Aliy flashing ya kunna data suyi fira ya kwanta da wuri gobe zai fara sabon aiki.

Yau Yusuf ya gama aikin café yana pool ammah ta kira ya gaisheta cikin girmamawa domin baisan komai ba akan hayfa illa ammah ce mamanta ikon Allah
Tanvayarsa tayi hayfa? Tace naji shiru tun rannan da tayimin txt na d'auka ma baku k'asar shiasa ban kira ba sai yau ganin kwanaki sun matsa

Ajiyar zuciya Yusuf yayi lallai da gaske sun d'auka shi d'an masu kud'i ne

Cikin girmamawa yace bana gida ne in na koma zamu kira IA

Ammah da ke lallab'a Yusuf kamar k'wai tace toh babu damuwa sai kun kira nagode suka yi sallama Yusuf ya fad'a tunani da mamakin al'amarin shi tunda suke chart da hayfa bai tab'a ce mata shi wani bane ko d'an wani

Hayfa yau ganin kayanta sun d'an taru tayi tagumi tana tuna Uthman mai wankinta da guga ko su pant da bra d'inta ammah ke wanke mata tas ta goge ta zuba mata a drawer ta

A dole ta mik'e ta shiga bayi ta zuba kayan a d'an k'aramin washing machine d'in ta dawo ta zauna gefen gado tana tunani tana gyaran gado ta canza bedsheets ta saka wancan a washing machine ta share d'akin tas ta d'auko d'an injin share tas tayi goge sosai tana yi tana hawaye har ta gama wardrobe ma ganin kayan Yusuf baida yawa ga sauran layi biyu na kanta space ta fitar da dogayen riguna kusan kala talatin ta jera su a gurin da hijaban sallah biyu ta gyara akwatunan ta maida su yadda Yusuf ya jera mata tun ranar da ta iso

Tana gamawa ta kwashe kayan wankinta taje ta baya inda taga Yusuf na shanya ta shanya ta dawo tayi wanka ta dafa shinkafa da stew d'in sardin da albasa kawai ta d'an ci ta koma d'aki ta zauna tayi shiru sosai take missing Aunty ammah tanata hawaye har magrib tayi sallah tana zaune kan dadduma har isha tayi ta hau gado saidai ba bacci take ba duk ta gaji jikinta ciwo yake mata ko wankinta ta manta bata kwaso ba

Bayan Yusuf ya gama da café kusan 9:34pm ya nufo gida a gajiye yana shigowa ya hango kayan hayfa a shanye sosai yayi mamaki sannan ya d'anyi murmushi yak'i kwaso mata ya shigo

Ya tsaya kitchen yaga jagwalgwalon miyarta da tayi a haka ya d'iba ya ci kafin ya shiga tana kwance ya tsaya yana kallonta ya fito da wayarsa ya jefa layin ammah yace "ke"

Ki ansa mamanki ce saura ki k'ararmin da credit dukda anan k'asar kira na da arha sosai ammah ni bamai kud'i bane taka tsantsan nake da credit d'ina sabida kullum ni kudin da nake d'an samu a lissafe suke

Tana jinsa bata motsa ba yaji ammah ta ansa tanata sallama yasa speaker bayan ya gaida ammah hayfa ta mik'e daga kwance ta fara gaisheta

Shigewarsa yayi bayi ta cire wayar daga h/free ta d'ora kunnenta

ammah tace ya gajiya?

Tace lafiya mominmu ya su muhsin da Yasmin da khairat?

Ammah tace duk lafiya sunata missing d'inki

Hayfa ta d'an share hawaye tace nima haka sosai...

Ammah tace karki damu da kin kwan biyu zaki warware bare in kin shiga dad'i mantawa ma zaki fara yi da mu gashi yanzu ma sai ni na nemo ki

da sauri hayfa tace Allah mominmu don banada waya ne..

Ammah tace bai saya miki ba?

Hayfa tace dam... Yusuf ya fito bayin ta d'ago tana kallonsa ta kasa k'arasawa

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now