KASAR WAJE. 49

1.2K 56 4
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Psge. 97/98

Yace zan amince bisa sharad'in idan kika dawo zaki ajiye aikin café ki yi zamanki gida zan riqa iya qoqarina wajen biya miki dukkan buqatunki a matsayina na mijinki wanda ni Allah ya d'orawa nauyinki..

Kallonsa take sosai bata fahimta ba sosai.. Yace kin amince.? shiru tayi ta d'an sunkwi da kanta qasa yasa kyawawan hannayensa ya tallafo fuskarta yana kallonta yace.. " baby wlh sam banason yadda kike wahala a café sannan uwa-uba café kamar hotel yake kowa na shiga a riqa kallonmin ke duk inda na ke hankalina baya kwanciya da sanin wani na kallonmin sirrina mallakina kawai daurewa na ke yi sabida na san kina buqatar aikin ya d'anyi shiru yana kallonta..

Ta saki hawaye mai tsawo a ranta tana ayyana idan ya ganta a fation parade qila zuciyarsa bugawa za tayi kenan wasu hawayen suka sake biyo kuncinta yana kallonta hannunsa yasa a hankali yana share mata yace " baby ina sonki kamar yadda na ke fidda ko wani iska na numfashina" wannan yasa ina jin kishinki fiye da yadda na ke son rayuwa a wannan duniyar pls ki taimakamin ki kiyi haquri da sharad'ina ki zauna a gida na miki alkawarin zan fara dawowa gida brk daga supermarket sannan ko mun fara school da zarar ba  mu da lecture zan dawo gida gurinki zan daina barinki ke kad'ai zan saya miki katifa na saka a d'akina na masallaci muna tafiya aiki tare kina baccinki zan... Tasa d'ora bakinta kan nasa tana sakin kuka sosai...

Shiru yayi ya rungume ta tare da runtse idanunsa a yayinda tana kuka tana tunani bata tab'ajin dana sanin kasancewarta model ba kamar yau dana sani take ta maimaitawa a zuciyarta na maiyasa ta fara
.? mai yasa bata hakura da aikin café kawai ba..? Mai yasa da ta fara sonsa bata fad'awa mominsu gaskiyar waye shi ba ta kuma fad'a mata tana sonsa a haka zata zauna dashi ba wayyo ta qara sakin kuka still tana rungume jikinsa..

Sosai suka dad'e rungume kowanne da damuwarsa hakan yasa suka manta da rungumar domin ko wannensu na jin cewa yana buqatar hakan a yayinda a karon farko Yusuf ya kyale hayfa tayi kukanta mai isarta kafin ya d'agota yana kallon yadda har idanunta sun kumbura

A hankali ya zare ta daga jikinsa ya mik'e zuwa falo ya bud'e fridge ya d'auko mata fresh milk ya dawo ya zauna ya fara bata a hankali take karb'a tasha sosai kafin ya ajiye ya shafa fuskarta ya mata peck yace "baby ina zuwa" toh tace a hankali ya fito ya bar gidan 

Bayan fitarsa ta d'auki wayarta ta jefa layin Armando..

Bugu d'aya ya d'aga "queen".! Ajiyar zuciya tayi ta fara gaisheshi saidai bai idda ansawa ba ya fara tanbayarta me ke faruwa jin muryarta da ta dashe da kuka..

fashe masa da kukan ta qara yi tace "daddynmu ne ya rasu" ajiyar zuciya yayi ya fara lallashinta yana tanbayarta yaushe mai kuma ya faru da shi nan ta bashi labarin komai kafin ta fad'a masa tanason ya mata bucking na jirgin safe gobe

d'an shiru yayi domin gaskiya yanzu baya son ta motsa ko ina koda a cikin Canada bare har Nigeria jin shirunsa tace "babu fly goben ne"?

Yace No queen ay ko wane rana akwai fly na Nigeria kawai banason tafiyar ne yanzu bai kamata ba ko kinsan dukda irin shirmen da kike kwanan nan amma kin samu vote sosai a result d'in wk d'in nan kuma bama a turo da results d'in America da Italy da Paris ba jst Brazil da Colombia da Venezuela da Spain ne yake qasa inada tabbacin akwai alamar Zaki samu gala amma kinata wasa yanzu kuma tafiya why "Queen"?
Shiru tayi.. Ajiyar zuciya yayi yace zaki yafi but pls jst 4dys ki dawo in ba haka ba wlh zaki sakani rigima da Bunill haka kike so nayi ta samun problem da Bunill da su Raudha a kanki..? Ah ah tace a hankali

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now