KASAR WAJE. 4

1.4K 76 2
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

Page.  7/8

Sannan amma ta bata wayarta tace ki masa flashing yanzu zai kiraki kuma ki saki jikinki kamar kun shekara tare

"Toh" kawai hayfa tace batason mijin amma jin zata k'ara kece raini da kuma burinsu da yayyunta zai cika yasa ta amince dukda gaskiya taso a ce shi ya biyota, kuma sam bata tunanin kamal duk da ya kan fad'o mata wani sa'in

Yusuf na kiching d'insa yana dafa shinkafa wayarsa ta fara ringing ko kafin ya d'auka tsinke

Da ya duba yaga Nigeria ne number da aunty ammah ta bashi ya maida kiran

Hayfa na son yin yangarta da ta saba zazzagawa maza suna binta kamar wawaye

ammah ta daka mata tsawa ta ansa wayar saidai ta kasa magana

Yusuf jin shiru yayi sallama a cikin muryarsa kamar ba namiji ba

ta ansa sallamar

Kusan suma Yusuf yayi domin muryarta kawai ya k'ara kunna masa wani gobarar Sonta

Gaisheshi tayi kawai tayi shiru su ammah na kallonta

Ayyanawa Yusuf keyi a zuciyarsa tafi surutu a chart kalla yanzu direct call tak'i magana sai yaji ta k'ara burgeshi

shiru shima ba gwanin surutu ba yace "zanci abinci yanzu mu had'u online anjuma"

"Toh tace suka yi sallma"

Su ammah suka k'ara ja mata kunne yadda zata saki jikinta dashi domin kusan mijinta ne ma shi yanzu

Ita hayfa da aunty amma ta koyar da ita jiji da kai na fitina da ko masu kud'i suka biyota haka take taka su koda zata saurari mutum amma kawai wannan ace ita zata rik'a lallab'ashi ay bazai yuwu ba gara shima ko waye ubansa yasan ita bata wasa bace

Abin mamaki wann duk yarinya mai 17yrs ke da bak'in buri da son duniya haka

Da yamma suka had'u a wpp sama-sama take bashi ansa

shi Yusuf mamaki ne ya isheshi kamar ba itace ke nace suyi ta chart ba nan ta bashi aunty ammah suka gaisa yayi mata bayanin zai turo magabatansa ta amunce

Kamar da wasa alhaji sammani yazo neman auren hayfa gun mujin ammah domin babnsu hayfa yace ya bawa mijin wuka da nama tunda su suka raine ta duk da kuwa shi ba wata tsiya yake tsinana mata ba iyakarta zaman gidan sa hasalima basu sashi cikin harkar samarin hayfa sabida shi ya dad'e yana cewa ammah ta bawa kamal hayfa ganin hidimar da yake da hayfa ba gajiyawa gashi shima iyayensa masu kud'ine sanan shima mai kud'ine gashi har gidan kansa yanada sannan ance albashisa ya kai 500k

amma ammah tace ko a mafarki hayfa tafi k'arfin auren kamar kamal, haka ya zuba musu ido!

Mijin ammah ke bata labarin yasan alhaji sammani babban attajiri ne yana harkar estate  kema bakyajin sunansa?

"Eh" tace inaji nan ta k'ara sakankancewa Yusuf d'an wani k'usan mai kud'i ne

Aka saka rana inda za 'a kai amarya gidan alhaji sammani daga can ranar da zata bar Nigeria zata wuce kano sai Toronto

Haka kuwa akayi dukda maman Yusuf na cikin rashi hidima ta musu yawa aliy ne ma ke zuwa ya bata d'an 3k ko 5k Yusuf 4mths kenan bai musu aike ba, sai k'anninsa maza bayan sun dawo boko suna zuwa dako aliy ya sama musu da ke suma sunada zuciya kamar Yusuf da haka suke taimakawa kansu suka ma daina tsammani da ga Yusuf

KASAR WAJEWhere stories live. Discover now